Wasiyar Aure😭❤❤
By; Naja Naira
FKD Fans Writers 《《 15 》》
Ushna nazaune tazabga tagumi hannu bibbiyu tana kallon Mama na kinkintsa kayanta cikin akwati, Takallah Fahad dake hannunta tarungumeshi tsam kozatasama 'karfin gwuiwar iya rike sautin kukan dake mata yun'kuri,
Kuka takeso tayi cincin karfinta kozata samu saukin duniyar da taimata atishawar tsaki, lalle da ace kisankai saukine ga musulmi da babu tabbaci Ushna saita margaya ko zatasama saukin 'kunar radadin da zuciyarta kemata,
Daga gefe takallah Mama ta'danyi 'ko'korin saisaita muryar tace "Mama kinata hadamin kaya kod,,,,,,,,,",
Tsit tai shiru tsoron furta abunda bakinta keshirin ambato,
Lokaci daya tatsinke da lamarin Mama, hawayen bakinciki ke ambaliya akuncinta tana kallon Mama datai banza da'ita tana aikin gabanta",Cikin 'yan mintina ta kammala, tazo tazauna gefen Ushna cikin nutsuwa da rarrashi tace "Ushna",
Cikin 'dar Ushna ta'dago kai suka hada ido tace "na'am Mama",
"Ajiye 'Dannan inason magana dake" Mama tafada cikin sanyin rai.
Ba musu Ushna takwantar dashi gefe tajuyo tana kallon Mama atsorace zuciyarta nabugu kamar zata tsaga tafito
Hannu Mama tasa tari'ko hannunta tace "Ushna ina fata zakiyi mana hisabi daidai bakin gwargwado, inaso kinsan duk 'iyaye fatansu daya, 'Yarsu tasama miji nagari, dukda nasan zakice ba'amiki adalciba, saidai inaso kisan wataran zakisan bakida masoya duk duniya kamarmu, lokacin inmuna raye toh zamuyi farinciki inkuma bamu zakisan mu masu kaunarkine, kiyi hakuri Ushna ita kaddara duk yadda tazoma bawa karba yake hannu bibbiyu yayi fatan tazame masa alkhairy,
Kuma inaso kisan yanzun dole kinatsu kisan abunda kike, duk wannan shashancin ki watsar ki rungumi 'Ya'Yanki da Mijinki amanar 'Yar'uwarki kinji",
Cikin rashin fahimta Ushna ta'dago kai tanakallan Mama, murya narawa tace "Ma Ma banga neba ko kun min Au Aurene?" Yanda take maganar atsorace yasa Mama ta ri'ko kafadarta ta rungumeta akirjita na'yan sakanni kan tace "eh za'adaura Aurenki da daddarannan amasallaci, Babanku yanzun yakirani yagayamin ana daurawa zasu biyo hanya kibi Mijinki tare da 'Ya'yanki kuwuce, yaso bayan komai yadaidaita Ushna sai'ayi taro",
Chak zuciyar Ushna ta tsaya, tanemi hawayen dake idonta tarasa, ma'koshinta yabushe ta'dago kai takallah Mama cikin dakushashshiyar murya tace "waye Mijin?"
Ita kanta Mama yanayin Ushna alokacin saida yafirgitata, murya narawa tace "Ham za ne, batun jiya Mahaifinki yasanar dakeba",
Wani irin hawaye masu ra'da'di suka tsinkema Ushna, ta rufe idonta dataji sunmata nauyi kamar andaura dutse akai, cikin kuka maisauti tace "Mama dan Allah kodai baku kuka haifainiba bakusan gayamin gaskiya, tunda nataso gidannan aka tsaneni babu maikaunata daga Aunty Rayhana sai maigadin gida, yau kuma sabida burin 'Yarku zaku aurar dani ga Ma'kiyina, sam baku damuba ko inmutu ko inyi rai ba'asona agi,,,,,,,,,,",
Muryarta tasha'ke, take tanema sautin kukanta tarasa, kuka take tuncin karfinta ba 'kara ko ita kanta bata iyajin sautin kukan,
Sai zaro harshe datake tana ma'ka'ki tana kallon Mama dake matse hawaye tana kallonta cikin tausayi."Banda Mama tasan kotai magana Alhj Shehu bazai janye ra'ayinsaba, toh tabbas datasa anjanye maganar domin yanzun kwata-kwata bata kaunar ganin 'bacin ran Ushna, barin tunda Rayhana tabar mata amanarta, sai yanzun tafara fahimtar illar kyaran 'Da, dankuwa koda baikyautawa nasiha da janhankali yake bu'kata ajanyoshi jiki ba tsangwama ba, kaicho yau gashi 'Yarta daya tilo ta kalleta tana kokwanto kan matsayinta na Uwa,
Danta ita tunjiya take ro'kon Baba yajanye maganar tunda tafahimci gaba daya basu kaunar hadin gashi babu fahimtar juna, amma saiyayi kunnan uwar shegu ya'ki, hakan yasa ta sallama tahakura",Suna cikin haka kiran wayar Alhj Shehu yashigo wayar Mama ta'dauka,
Kantace ufffan yace "Kisauko da Ushna da Yara parlour sutafi tare yanzun da Hamza"
Yakashe kiran,
Mama takallah Ushna dake hawaye tana kuka basauti ko ka'dan, tarungumo kanta kankafadarta tai shiru,
Kwarai tatausaya, zuwa lokacin tsarin da suka daukarma 'Ya'yan na hadasu da mazaje tafahimci bashida fa'ida domin tana iya jiyo bugun zuciyar Ushna dake jikinta, ta share mata hawayen dake dirara kan fuskanta tace "tashi muje Parlour Mijinki najiranki, Ushnata dan Allah karki bamu kunya, nasan ammaki badedeba kidubi girman Allah kiyi hakuri karki yarda kiwani abunda zaki zubar da kimarmu a idon duniya, kiyi hakuri",
Ta dauki Fahad ta ri'ko hannun Ushna tasauko da'ita suna tafe tana bata baki.,Suna isa Alhj Shehu yakallah Hamza yace "dare yayi, bazama zakuyiba Hamza kadaukesu kuwuce Allah maku Albarka",
Tsit Parlour yayi sai Mama datayi karfin gwuiwan gyaran murya tace "a'a Alhj daga zuwa kuma, Madina ma nadakina",
Ta sausauta murya takallah Hamza datunda yazo idonsa ke'kasa tace "Hamza ga Ushna nan kadubi girman Allah kariketa Amana, kuyi hakuri da juna tunda Allah ya kaddarceku da zama tare",
Idanunsa sunkada sunyi jajir, yayi danasanin rashin sa ba'kin Spec, dakyar ya'dago kai yace "insha Allah",
Alhj Bello yakallah Ushna yace "'Yata kiyi hakuri nasan antauyeki amma kikayi hakuri wataran sai labari, kuma duk sanda kikeda matsala kowace irice toh kizo kisameni kinji?"
Kallonsa kawai Ushna keyi babu baki,
Mama ta kada baki tace "eh dayake tana mura, bata iya magana",
Gaba daya suka dago kai suka kalleta, tarame ta lalace, daga tsaye babu rabinta dama ga siranta abunsai ya'kara hademawa da damuwa ta 'kara zama 1.
Basu tsaya 'bata lokaciba Mama tasa Garba maigadi yahada kayan Ushna data shirya mata cikin mota, suka kama hanya suka tafi Ushna na tsala ihu bamaiji, ita kanta bata iya jiyo kanta....**********
Suna isa Hamza yanufi dakinsa yabanko 'kofa,
Baidameta ba dan dama batayi tunanin zai'iya kallontaba duk rashin kunyarsa,
Hakayasa itama tashige dakinta tare da Fahad dake goye abayanta da Madina a hannu.Tana shiga tayi wanka ta hada tare da Madina tawanketa tsab,
Fahad nakwance yana harharba 'kafa tahada ruwan zafi tayima sarkin kukan daren wanka hadi da 'dan tausa, tashiryashi tsab takwantar,
Tashige toilet tadauro alwala tafito tayi sallah isha'i da batasama damar yiba akan lokaci,Kanta idar dasallah gaba daya Yaran sunyi barci hakan yasa tasama damar yinbarcin na'yan awanni, kan Karfe ukun dare Fahad yafarka yafara kwada iwuh yana neman abinci,
Cikin barci tafarka dasauri tanemi madararsa tarasa, sunbarta gidan Mama,
Tadawo tazauna tayi rarrashin duniya ya'ki hakura,
Ganin basauki tabashi ruwa mai'dumi ya'ki kar'ba,
kuka yake tuncin karfinsa har hudun dare baisaurara ba,
Tana zarya cikin daki taji 'karar bude 'kofa,
A tsorace tatsaya ta'kurama kofar ido ganin maishigowa,Hamza yashigo cikin kayan barci pyjamas ash colour, tayi 'dan ajiyar zuciya takauda kai,
'Kala baice mataba yakar'beshi yahau jijjigashi, ganin ya'ki shiru yakalleta arude yace "maike damunshi ne",
Murya narawa kamar zatai magana, maganar ta sha'ke, tarasa abunyi tana kallonsa nan tatuna wayarta dakekan gado ta dauko ta rubuta maita note "yunwa yakeji namanta da madararsa agida",
Dasauri yakaranta cikin tsawa yace "toh kuma shine bazaki gayaminba saikibar Yaro da yunwa".
Wani irin kallo taimai ta buga 'kafarta cikin zafin rai tafada gado tajanyo bargo tabarshi tsaye Fahad natsala iwuh",
Hangama baki yayi yana kallonta yana tsaye yarasa abunyi,
Ba abun yakira sunantaba tatashi taimai wulakancin dayafi karfinshi,Ganin tunani bazai fushsheshiba Fahad natsala ihu, yasa kai yafice, bai tsaya ko inaba sai dakin Uwani.
Sunanta yafara kira kan yahau kwankwasa mata 'kofa,
Cikin barci taji kukan Fahad ta tashi zumbur tabude kofar,
Hamza dake tsaye arude dasauri yadago kai yace "Uwani dan Allah maiza'abashi yunwa yakeji, Ushna kuma ta mance madararsa agida,"
Kallon hanyar kitchen Uwani tayi tana nazari tace "toh ranka yadade kozamu bashi madara, zuwa gobe saiyasha tashi dukdadai zata iya 'batamai ciki",
Zaibata amsa yaji anbuga 'kofa gwaram,
juyawan dazai yaga giftawar Ushna daga ita sai 'dan mayafi tare da makullin mota ahannunta,
Dasauri yami'kama Uwani Fahad yabita aguje,
kanya'karasa bakin 'kofa hartashiga mota tatayar,
Yayi mamakin motar datahau dan yadade yana ganinta awajan amma dayake hankalinsa baijikinsa baibi takaiba.....

YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...