WASIYAR AURE😭❤❤
By; Najaatu Shehu Naira
Wattpad; Najaatu_NairaFKD PRODUCTION FANS WRITERS. (((49)))
Atsorace takoma dabaya zata fadi, dasauri yamatsa zai riketa tace "karka sake ka ta'bani" tare da hawaye afuskanta, nandanan jikinta yahau karkarwa zuciyarta tafara 'kuna,
Saida takai jikin bango tazauna turus tana kallonshi tana kallon 'dan hannu matar,
'Kib ta rintse idonta azuciyarta tana fatan "ya Allah kasa mafarkine Ya Allah, Allah kasa wannan mafarkine ya Allah" tun tanayi azuciya harsaida yafito fili ta 'du'kun'kune jikinta tana takure yaje inda take ya dafata,
Arazane tabude ido, idonta yasauka kan kwayar idonsa tayi sauri ta goge kwallanta cikin zafin rai tace "kenan ba mafarki bane, Fid kayaudare ni, kasan baka sona maiyasa ka aureni? mainaimaka arayuwa daka rabani da farincikina Iyayena, Mijina 'Ya'ya da kowa nawa, ka'ajiyeni agidanka kana azabtar dani babu kalar ukubar da bakaiminba, mara mutunci tsinanne Allah saiya sakamin kuma wallahi,,,,,",
Saukar marin dataji kan fuskanta yasa tazaro ido tarike kuncinta tace "Fid ka'daga hannu kamareni",
Gyada kai yayi yace "eh sai inkuma kara maki, Useless mara amfani wato baki gama hankaliba kenan agaban bakuwa sai kinnuna halinki, toh bari kiji ingaya maki,
Abun dakikaimin da nadauka yanzun bazan daukaba, as you can see inacikin ahalina Mommy da Daddy suka auramin Najma har Allah yabamu rabo inkinga zaki iyazama kizauna inkinga bazaki iyaba hanya abude take, saiki shiga duniya dan ni yanxun nafi karfin inroki So wajan mace, nariga nasamu"
Gaba daya jinsa kawai take tana sharban hawaye, batare da kallon kwayar idonsaba,Akwana atashi tanaji tana gani Fidyan yamaida 'dakinta na Matarsa, tashin hankali nayau daban nagobe daban, babu wani abun dake shiga tsakaninta da Fidyan sai kyara, 'Dansu kuwa dazaran yayi kuka kusa da ita ko batasan dashi akusaba sai Fidyan yasa bulala yazaneta ko mari yana fadin bakin kishi ke damunta, ga kirsa wajan Matansa dagangan zata cika gishiri agirki tace samata akayi,
Hakanan zaman parlou agidan yagagareta,Babu abunda ke cimata tuwo akwarya irin yadda Fidyan yaki yarda yabata bayanin inda 'Ya'yanta suke, cikin zafin rai da tumin bakincikin da take kwasan jiki tafita,
Dan sarkokinta nazinari tasayar takoma sintirin kudin motar zuwa gidan Marayun dake garin, babu inda batajeba lungu-lungu sa'ko-sa'ko babu labarinsu,
Watarana tafito tana kan hanyarta ta komawa gida rana ta kwale nandanan tafara ganin juwa duniyar na juya mata batayi auneba zata tsallaka titi mota ta kwasheta, .
Gab da idonta zairufe wani guntun hawayen bakin ciki ya zararo tagefe.Bata farkaba sai washegari tana tska da raba ido dangano inda take ta tsinci wasikar Fidyan kusa da'ita tajan kune, gargadi yakemata gargadin karta jamai bala'in human right tare da saki daya,
Kuka tafara mai radadi tana danne zuciyarta dan zugin da takemata kamar zata tsege tafito,
Kuka take sosai mutane nakanta sunabata baki dukda basu santaba ko dalilin kukan,
Takardan take dada kallo tana dukan kirjinta tana fadin "haba Fidyan toh yanzun ina zani", tayi kuka ma'ishi, likitocine suka bata baki bayan kwana biyu suka sallameta,.Saida tadade tana nazarin wajen zuwa,
Duk yadda taso takauracema zuwa gidan Fidyan abun ya faskara domin harta gama tunaninta batada wajan zuwa babu wanda zata fuskanta afadin garin taji dadi,
Hawayenta kawai tashare tatsaida Taxi tanufi gidan Fidyan,.Akofar gidan tasauka tashiga ciki tinkis-tinkis ta kwankwasa kofa,
Kamar wasa saida tafi awa daya tana kwankwasa kofa rana nadukan kwanyan kanta kan Fidyan yafita yatsaya hannunsa akan kugu yace "lafiya maikika dawo yi? Bakiga sakona bane?"
Dago kai tayi ahankali takalleshi yana mata dushu-dashu dan tsananin saramata da kan keyi,
Cikin taushin murya tace "Fid dan Allah kayi hakuri yanzun inka rabu dani ina zani iyayena bazasu karbeni ba, kasab saida narabu dakowa dankai dan ina sonka dan Allah kamaidani dakina",
Tsaki yaja yana hura hanci yace "amfanin mai zakimin? Tunda na aureki gayamin kintaba bani hakkina kekenan kullun kuka akan shegun 'Ya'yanki,"
Dasauri tariko hannunsa tace "Fid zanbaka hakkinka dan Allah kayi hakuri kona koma gida zasu koreni",
Dan murmushin gefen fuska yayi ta mugunta, zaijanyota karab Najma tabude 'kofa afusace tace "ainaji komai, munafiki matar daka saki kawai dan ta amince zata baka hadinkai saika dawo da'ita, kalletafa akwanjame alalace daga gani tanada cuta shine zaka dawo da 'ita?",
Lokaci daya ya susuce yarasa tayi, yakallah kwayar idon Ushna dake zubda kwallah yace "Ushna" dasauri ta'dago kai takalleshi ganin yakira sunanta tasan ba Hope ta rushe da kuka,
Kasa magana yayi Najma tajanyoshi gefensa tace "wlh inbaka rabu da itaba saina tonama asiri wajan iyayenka kuma nima wlh nagama kishi da'ita saidai kasakeni natafi da 'Dana, akan wannan watsatsiyar yarinya,,,,,,,"
Kanta rufe baki Ushna tadauketa da mari ido jajir tace "kisan matsayinki, zanyarda dakomai amma banda zagi da wulakanci",
Cike da mamaki Najma tace "kika mareni?"
Kanta bata amsa Fidyan yace "yazaki mareta bakida hankaline?"
Fuuuuu Najma tashiga daki yabita yana kira taki kulashi,
Wardrobe dinta tanufa kai tsaye tafara watsa kayanta cikin akwatu,
Cikin tsawa yace "ke meye haka? Ina zaki?"
"Gidan iyayena zankoma" tabashi amsa,
Ajiyar numfashi yayi yace "bake zakibar gidannanba saidai in ita zata bari, kijirani",
Wuff yafada dakin Ushna tabi bayanshi ya tattaro mata duk kayanta yasa a akwatu,
Yafito fuuuu yadauki passport dinta ajakarshi zaifita yataddata a parlour tashiga,
Afusace ya funciko hannunta ya cillata waje tare da akwatun kayanta yace "kibacemin dagani, karki sake nafito naganki harabar gidannan, saki kuma nama karamaki wata akai, kije wajan masu zigaki,"
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...