ONE BLOOD

341 19 1
                                    

⚡ *ONE BLOOD* ⚡
                By
_Nu'aiymah Abdull Tafida_

_Book dedication to My Tween sis Na'imah Abdull Tafida_ 🌚

_Episode 3&4_

Misalin karfe tara da rabi na farka daga baccin safen da na koma. Toilet na fada na wanke fuskata na sauko falon kasa dan gyra bangarena, cikin kankanin lkc na gyra ko'ina yay kyal sai wani sanyayen k'amshin turare mai sanyaya zuciya da bargon jiki dake tashi da ya gauraye da sanyin AC ya bada wani kamshin na Musamman. Main parlor na karasa na fice babban kitchen din, dan daura breakfast daidai cikina kasancewar bani bace da girki Zuhrah ce dayi kuma ni tsakani ga Allah bazan iya cin abincin ta ba, shiyasa na bukaci a raba girki kowacce ta dingayi da kanta amma ya Abdull yace shi sam! Baisan zancen ba, ban kara tayar masa da maganar ba amma fa na sanar dashi wallahi ba zanci kazantar kowace gardiya ba da raina da lafiyata. Tun yana magana har ya gaji ya shafamin lafiya ganin na fishi danyan kai. kishingid'e na hangesa saman doguwar kujera ya tallafo kansa da hannayansa duka biyu ya kurawa Tv'n daketa 6a6atu idanu sai dai sam hankalinsa da tunaninsa baya wajen ya lula wata duniyar daban. Banyi mamakin ganinsa gida ba kasancewar yau Lahadi. Doya na fere na yayyanka kanana na fasa kwai biyar na jajjaga attaruhu da da tafarnuwa na juyesu cikin doyar na cakula waje daya na saka magi da kayan Kamshi. Na dora mai bayan yayi zafi na soya doyar na juye a filet mai kyau na rufe sannan na daura kunun gyada, cikin kankanin lkci komai ya zama reading, tuni kichin din ya gauraye da kamshi ga kunun gyadar ma yasha madara da kayan Kamshi na juye a jug na fice daga kichin din zuwa part dina. Yana zaune tazo ta fice ta gabansa, sanye take cikin Doguwar rigar roba-roba wacce tayi massifar dameta ta fito da kyakkyawar surar jikinta, ganin yadda take tafiya komai na jikinta na girgiza sai ya dauka da gayyah takeyi, ta6e baki yay ya dauke kai gefe. Saman dan karamin gilas table din dake tsakiyar kujerun falon na ajiye abincin na haye sama dan yin wanka. Na kwashe kusan rabin awa sannan na sakko sanye da riga da wandon jeans blue da bakar ti-chert mai photon Ledibeug, ina kokarin tufke gashin kaina da ribon din hannuna na hangosa. Cak naja na tsaya ganin kallon 6arnar da yakemin, zaune yake ya daura kafa daya kan daya ya daura filet din doyar saman cinyarsa yanaci hannunsa na hagu rike da cup d'in kunun gyadar yana sha. "Kam bala'i!." Na fada a daidai lokacin da nazo gabansa ina jifansa da harara, ganin yaki kulani yasa na daka wani wawan tsalle na zube saman tayis din ina wani uban kuka mai gauraye da ihu ina wani birgima da Fad'in wallahi sai ya biyani abincin da na kwashe tsawon lokaci wajen hadawa dan inada bukata. Kallon ta kawai yake a kaikaice bai ko motsa daga inda yake ba sannan kuma bai daina cin doyar ba yana korawa da gudun gyadar da yakejin gardi da dadi na ratsa har kwanyar kansa. Ganin yadda take birgima a tayis din wajen tamkar wata mai Aljanu sai abin ya bashi dariya amma ya dake abinsa dan kar taga damar sa, sai da yay nak sannan ya ajiye mata sauran da ya rage ya mike yabi ta gefenta ya nufi fridge din ya bude ya dakko gorar faro ya kwankwada ya dawo zai zauna. Ganin yazo zai fice ta gabana kuma yaki tankani sai wata dabara ta fadomin, banyi wata² ba na cakumo damtsen kafarsa na gantsara masa cizo iya karfina, na shiga kai masa duka ta ko'ina ina kukan ta6ara. Ganin iskancin nata bana karewa bane ya sashi daka mata tsawa, tsit ta nutsu amma still bata daina hawayen da take ba. "Tashi ki koma saman kujera ko na zubar da 'yan hanjin cikinki." Ya fada a kausashe, Ganin yadda yay maganar cikin dakamin tsawa yasa na tashi fuu zan haye sama ina sharar kwalla, yay azamar saka kafarsa na hagu ya tunkude ta kiii! Sul6in tayis din yajata zata fadi kasa, cikin zafin nama yasa hannayensa duka biyu ya tarota ta fado kirjinsa sukayi baya luu suka fadi saman doguwar kujera 3seater hakan yayi daidai da shigowar Zuhra a falon sallama dauke a fatar bakinta, 'Yar kara Nu'aiymah ta saki dalilin kujerar data daki kafadarta na dama kuma itace a kasa gabadaya ya sakar mata da yaunin jikinsa yana murmushin mugunta. Idanu na rumtse sosai ganin yadda muka samu kusanci sosai dashi numfashinmu na sauka cikin na juna, idanu ya tsura mata ganin yadda ta rumtse idanu amma hawaye na kwaranya a kyakkyawar farar fuskarta. Kasa dauke nasa idanun yay, cikin kasalar data ziyarce shi kai tsaye ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta yace. "Shiiiii!." Ya fadi Yana share mata hawaye da tafin hannunsa, wani yarr naji a sa'ilin da ya kai bakinsa daidai kunnena sai dai ko da wasa ban bude idanu ba. "Nine koh."? Naji ya fada fuskarsa daf da tawa fuskar, haka kawai na samu kaina da gyada masa kai ina turo baki, "to meyasa baki dafa abincin dani ba, rowa koh."? Ba shiri na waro idanu waje ina harararsa cike da tsiwa na bude baki zanyi magana naji ya hade bakinmu waje daya. hade jikinsu yay ya matseta sai duka take kai masa da zagi, a hankali ya dire kansa a wuyanta yana sinsinar kamshin hadadden turarenta me azabar dadi da tafiyar da zuciyar duk wani lafiyayyen namiji, dan ta hada da wani shu'umin humra wanda aka saka mata a show glass dinta shi kanshi humran na musaman ne, wani bakon yanayi ne ya shigesa bai taba jin wani feelings akan mace ba amma sanadin kamshin humran yasa shi fara kai mata wani irin sumbata wanda yake cike da tsantsar mugunta domin duk inda yasa bakinshi sai ya tsotse gurin kamar ya sami lollipop, tureshi Nu'aiymah take iya karfinta tare da kai mishi duka amma ko gezau baiyi ba, asalima sai kai hannunshi yayi cikin rigarta ta kasa ya kamo dukiyar fulaninta bai tab'a kare mata kallo ba amma yau jin Boobs dinta sun cika mishi hannu bai san lokacin da ya zaro hannunshi idanunshi a rufe, ya shiga kokuwar cire mata riga ita kuwa ihu take tana kai masa duka cikin kuka, dagowa yay da shanyayyun idanunshi ya tsurawa bakinta ido wanda suka sha pink lipstick , lumshe idanunshi ya sake yi ya kaiwa bakinta sura Ya shiga taune mata su kamar ya sami alawar tsinke, tass ya shanyesu sannan ya lallubo harshen shima ya shiga bashi horo na musanman hannunshi na cikin rigarta yana murza boobs dinta son ranshi kamar zautacce, dagowa yay ya kafa bakinsa saman nononta yana tsotsa a hankali gamida lumshe ido, daya hannun nasa kuma yana murza nipple dinta dashi. Duk wani rashin kunyarta da tsiwarta sun kasa kwatarta a hannunshi a karshe sai ta kasa kukan ma sai lumshe idanu da tayi wasu zazzafan kwalla na wasan tsere daga idanunta still bakinta na cikin na Abdull yana tsotsa, sosai ya ladabtar da'ita sai da ya gaji dan kansa sannan ya shafa mata lafiya yana murmushin nan nasa na mugunta dan shi a ganinshi yayi maganin marar kunya da tsiwa ne. Wayarsa ya dauka yaga har 13 miss calls din Zuhra, kai ya dafe cike da takaici ya gyara rigar jikinsa ya fice daga falon gabadaya yana harararta. Bayan fitarsa ta sake sakin kuka mai cin rai tace. "Allah ya isa min mugu azzalimi kawai wanda baisan annabi ya fakuba, bazan yafe taba jikina da kayi ba mugu kawai." Na fada ina mikewa zaune ina sharar kwalla cike da jin tsanarsa Hannuna akan kirjina ina laluben rigata cike da tsoron ganin yadda take kan boobs dina sukai curr da wani irin jaa na azabar da sukasha a hannun azzalumin can.

Dakina na koma na kwanta ina mai cigaba da kuka ba tare dana sake bi takan wani abinci ba duk da inajin yunwa, daga haka wani nauyayyen bacci ya kwasheni ban kuma farkawa ba sai kusan karfe uku na rana. A gaggauce na fada wanka ganin lokacin sallah ya wuceni, nayi wanka na dauro arwala na fito ina tangyad'i saboda wata fitinanniyar yunwar da nakeji dan tun jiya da rana dana tafi gida rabon da inci wani abu, doguwar rigar shan iska shara-shara na saka ban ko saka bra ba yadda kirji na ke min ciwo, na shafa mai na shinfida Darduma na tayar da sallah. Bayan na gama ina zaune inajan carbi naji kiran sallar la'asar saida nayi la'asar sannan na fice daga dakin na sauka kasa, ganin kofar falona a bude yasa gabana faduwa dan nayi tunanin azzalumin can yana nan ne, jin babu motsin kowa a falon sai na Tv yasa na karasa cikin sand'a na rufe ina sauke tagwayen ajiyar zuciya dan wallahi tsoran haduwa nake dashi da na fahimci kwata-kwata yah Abdull bashida tausayi ga kuma zagin da nayi masa dazu da safe na tabbata ya jini bai dai tankamin bane ina tsoran yazo yaymin abinda yafi na dazu da safe. Kichin na shige cikin kankanin lokaci na hada Indomie da tea na fito falo na zauna. Bayan na gama na tattare kayan na kai kichin na dawo na bude sabon shafin kallon wani serie.

Banfargaba har karfe shida tayi ban daura girkin dare ba. Tsaki naja cike da tsantsar takaici lokacin dana tuna yau bangarena Yah Abdull yake, dan dalena na kashe kayan kallon na fada kichin ina tunanin abinda zan haɗawa mai saurin sarrafawa, tsaki na kuma ja sau ba adadi na bude fridge ɗin ina karewa komai na ciki kallon tsaf. Zuciyata ce ta bani sha'awar dafa jalof ɗin Tafiya da farfesun kifi, aikuwa cikin awa daya tal! Na karasa komai na jerasu a dining bayan na tsaftace kichin ɗin. Falo na dawo nan ma na shiga gyarawa tamkar na fasa ihu dan takaici da gajiya, duk da baiyi wani datti ba kasancewar ɗazu da safe nayi shara da mopping bai hanani kara sharewa ba na feshe ko'ina da freshner masu sanyi da k'amshin dadi sannan na haye sama dan yin wanka jin an fara kiraye-kirayen sallar magarib. Wanka na shiga na dauro arwala na fito sannan na tada sallah, ban tashi daga Dardumar ba wani nauyayyen bacci ya daukeni..

Tun safe da ya baro bangaren Nu'aiymah sukayi baran-baran da Zuhrah, ta dage wai lallai yanacin amanarta ta hanyar shiga bangaren ita Nu'aiymar yana zama alhalin ba ranar girkinta bane, abinda Zuhrah batasani ba shine shiga goma Abdull zaiyi a bangaren Nu'aiymah to fah sai anyi tashin hankali da massifa a tsakaninsu, yayi kokarin fahimtar da ita amma fafur ta rufe idanu tana zaginsu shi da Nu'aiymar tana Fad'in mugayen kalamai akanta harda fadin insha Allahu sai taga bayanta. Aikuwa wata wawuyar zuciya ce ta debesa ya wanke fuskarta da lafiyayyun maruka har guda hudu ya haye upstairs abinsa ya barta tana wani irin ihu da kururuwa tamkar zautacciya. Kwanciya yay rub da ciki zuciyarsa na masa wani irin zafi da radadi, daga haka bacci ya daukesa sai misalin karfe biyu ya farka, dogon wandon jallabiya ce a cikinsa kai tsaye ya fada toilet ya dauro arwala ya fito ya zura rigar wandon ya fice daga dakin rike da key ɗin mota bayan ya kulle dakinsa ruf da mukulli gudun karma ta shigo masa daki.
Yaso lekawa part ɗin Nu'aiymah sai dai wata zuciyar ta gargadesa da fadin 'kar kaje ka kwasowa kanka wani abin takaicin da zai kara fusata ka.' da wannan tunanin yabar gidan zuciyarsa na tafarfasa. Direct Family house d'insu ya nufa ya yada zango a falon Inna, zaune ya sameta tana limke kayan wanki su Twins na tayata hira, tana ganinsa ta washe hakora tace. "A'a yau Angon nawa nake gani a gabana ko kuwa gezau ne." "Nine Inna, barka da rana ya gidan.?" Ya fada fuska ba walwala yana zama saman sofar falon "Lafiya lau! Bakada lafiya ne na ganka haka Abdullahi? Ko matan naka ne basuda lafiya."? Inna ta fada tana gyara zama sosai gamida fuskantar jikan nata. Ajiyar zuciya ya sauke yana kokarin danne fushinsa yace. "Ba komai gajiya ce kawai." Baki Inna ta tabe tace. "Shikenan ai sai kayi kuma, Allah ya huta hutadda gajiya ya rufa asiri." Ta fada tana 'yan wake-wake gamida harararsa ta gefen ido ita ala dole wai yayi mata karya. Tsam ya mike ya mike zai fice daga dakin Inna ta dakatar dashi ta hanyar faɗin. "Har zaka tafi kenan?." "Eh." Ya faɗa yana kokarin fita. "Kaga tsaya na baka sako ka kaiwa masifaffiyar yarinyar nan Dan nasan tana sonshi sosai." Daga haka ta shige Kitchen, ba jimawa ta fito rike da bakar leda a hannu ya amsa yay mata sallama, motarsa ya bude ya cilla ledar sannan ya karasa nasu part ɗin. Ummah ma yau ta fahimci yau akwai abinda yake damun ɗan nata amma koda ta tambayeshi yadda ya fadawa Inna itama haka yace da'ita, bata takurashi ba dan tasan murdadden hali irin na ɗan nata, nan dai sukaci gaba da ta6a 'yar fira irin ta uwa da ɗa kafin yay mata sallama ya shiga sashen duk Baffan nansa ya gaidasu sannan ya shiga bangarensu Nu'aiymah. Zaune ya samu Mami a falon tana yanka fruits ɗin gabanta, tana ganinsa ta faɗaɗa murmushin ta, murmushin shima yay ya karaso falon ya zauna gefen ta yana fad'in. "Mami na barka da warhaka." "Lafiya son ya aiki." Ta fada tana shafa kansa cike da kulawa take tambayarsa meke damunsa, kwanciya yay saman doguwar kujerar da Mami take zaune ya daura kansa saman cinyarta yace da'ita babu komai gajiya ce kawai, fira suka dan ta6a cikin wayo da dabara ta shiga yi masa nasiha dan ta fahimci akwai abinda ke damunsa ya dai boye mata ne kawai kuma hakan yana da nasaba da matan nasa.....✍🏻

_Follow me on Wattpad Please @Abdull Nu'aiymerh._

Wattsapp no. +227 93414725

ONE BLOODWhere stories live. Discover now