part 53-54

48 5 0
                                    

*ONE BLOOD*

#Nu'aiymah Abdull

*Shafi na 53-54*

ƙirjina ne ya shiga bugun tara-tara nai saurin ɗauke kaina gefe sanda naji shigowarsa ɗakin, ciki-ciki na amsa sallamar da yayi ina cigaba da shafa kan yarona, ƙamshin haɗaɗɗan turaransa da naji daf! dani ne ya tabbatarmin da ya iso inna nake hakan yasa na ƙara yin kicin-kicin da fuska, ganin ya zauna gefen gadon da nake kai har jikinmu na goguwa yasa na muskuta na matsa gefe ina ɗan satar kallonsa naga shima fuskarsa ba fara'a hasalima wayarsa yake operating time-time ne yake ɗagowa ya kalli yaron, na ɗan taɓe baki nima na ɗauke kaina ina ƙara tamke fuska. a ɓangaren Abdull kam yau ya tsinci kansa cikin wani irin farinciki marar iyaka, koda ya shigo ɗakin bayan an sanar masa ta farka ganin yadda tayi welcoming nasa yasa shima ɓoye fara'arsa ya ƙaraso ya zauna, ganin dai batayi azancin basa ɗansa ba yasa miƙa mata hannu alamun ta basa shi,da kallo nabi hannun nasa dashi sannan na ɗago ina kallonsa, ganin bbu alamun wasa a tattare dashi yasa na sunkuyar da kai gamida zare nonon daga bakin yaron na miƙa masa shi sannan na gyara rigata na zame na kwanta gamida juya musu baya idanu lumshe kamar mai bacci. yana karɓan yaron shima ya koma saman ɗaya gadon ya rungumesa tsam a jikinsa cikin farinciki marar iyaka, Mum Fareeda ta turo ƙofar ɗakin da sallama, ta ƙaraso ta zauna suna ƙara gaisawa da Abdull, then Leyla ta shigo riƙe da kwanto tana washe baki tayi saurin karɓar yaron itama cikin farinciki kafin ta hau masa pictures, nidai duk ina jinsu na kulle idona kamar mai bacci, Mum ce ta dubi Abdull tace "wai barin ta kai ta koma baccin bata ci komai ba to meye amfanin kiranka da nayi"? sai da ya ɗago ya saci kallon inda take sannan ya bata amsa da faɗin "tou ai nima a haka na sameta" daga haka yaci gaba da sabgogin gabansa, idanu na ɗan zaro a raina nace 'taɓ! kenan shima ya iya ƙarya'? Mum ta ƙaraso gaban gadon riƙe da kofin haɗin kakkauran tea dake ta tururi ta fara tashinta dan duk a tunaninta da gaske baccin Nu'aiyma ta koma, a hankali na juyo ina amsa kiran da take min ina yunƙurin miƙewa zaune, kofin ta miƙo min tace "maza shanye kafin kici abincin,bbu musu na karɓa na fara shaa, sai da na shanye tas! sannan na miƙa mata cup ɗin, da kanta ta taimaka min nayi wanka na canja kaya sannan muka dawo ta xubamin lafiyayyan abincin da Leilah ta kawo naci sannan na koma na kwanta a lkcn har ƙarfe biyu tayi, Mum ta dubi Abdull tace "dare yayi yakamata ku koma gida hakanan har da safe" bai mata musu ba ya miƙo mata yaron yayi mata sallama, sai da ya juyo ya kallin ɓangaren Nu'aiyma ganin har tayi bacci yasa ya fice yana murmushi Leila na bayansa. washe gari tun ƙarfe takwas ƴan uwa da abokan arziƙi suka fara tururuwa dubamu a assibiti, tuni haihuwar ta fara zagaye dangi na nesa da na kusa sai yamma liƙis aka sallame mu zuwa gida, direct part ɗin Mum aka nufa dani, har bedroom ɗinta ta saukemu, haka ƴan barka su kai ta tururuwar zuwa duba babyn. ana jibi biki Ya Abdull ya kawo akwatuna biyar cike taf da kaya kamar lefen wata amaryar, huɗu nawa ɗaya na Babyn da aka yiwa huɗuba da sunan Baffah amma za'a dinga kiransa da *PAPI*, tsadaddun atamfofi da lace da shaddodi ne na kece raini, cikin ƙaramin akwatin kuwa harda takalma da jakunkuna da turaruka masu ƙamshi irin na jarirai da kalar wanda nake using dashi ya siyo, Mum da kanta ta kai kayan wajen mai ɗinkin ta inda ta buƙaci atamfofin ayi musu ƙananan ɗinkuna, leshunan da shaddodin kuma ayi musu manyan ɗinkuna na fita unguwa,Already anyi min kayayyin fita suna. haka aka dinga tsara abubuwa da shirye-shiryen suna, washe gari ranar suna ban tashi da wata cikakkiyar lfy ba shisa ba'a wani takumin da wani canje-canjen kaya ba hasalima tunda aka shafa fatiha na koma ɗaki na kwanta sbd yanayin dana tsinci kaina, taron sunan ma ba'ayi wani tarkace an dai ci an sha haka aka tashi taron lfy. tun ranar kuma na koma part ɗin Inna da zama, kulawa kuwa bbu kalar wanda bana samu daga wajen Mum Fareeda da Inna kai harda ma Mami sai dai ita tana ɗan nuna kawaici, shi kansa Ya Abdull duk safiya kafin ya fita aiki sai ya shigo ya karɓi yaronsa yayi masa wasa sannan yake fita, baya shiga sabgata kamar yadda nima ko kallo bai isheni ba! bayan gaisuwa bbu abinda ke shiga tsakanin mu, haka rayuwa taci gaba da tafiya har mu kayi Arba'in, a ranar kuma Abdull ya koma can ƙasar da yake aiki...bayan wata huɗu sosai nayi wata fitinanniyar ƙima dani kaina idan na kalli kaina har wani burge kaina nake, hutu da jindaɗi da kwanciyar hankali ya ratsa har cikin jinin jikina dani da yarona da shima yayi ɓulɓul dashi, banida wata damuwa da ta wuce na koma makaranta amma bansan wanda zan fara tunkara da zancen ba dan nasan Baffa bazai goyi bayan hakan ba xaice sai nabi takan Abdull, Inna na fara tunkara da zancen na kuma buƙaci da ta taimaka ta sanarwa Baba Shagari inason komawa makaranta,ina da burin yin karatu mai zurfi ko dan cikar burina na son gadar mahaifiyata na zama cikakkiyar likitar mata. ko da ta sanar masa washe garin ya buƙaci ganina a falonsa, nan nabar Papi wajen Mami na fice sanye da dogon hijab har ƙasa, a hankali na tura ƙofar falon sanda na ƙaraso, sallama nai suka amsa min na ƙaraso na samu waje na zauna kai na a sunkuye na gaishe su duk suka amsa min, Baba Shagari da Baffah sai Uncle Sulaiman, then Baffah ya ɗago yayi gyaran murya ya kira sunana na amsa a ɗarare yace "naji kin turo Maama da wani zance wai a gaya mana kina son komawa karatu shine abun ya bani mamaki shisa na kiraki dan tabbatar da anya maganar nan daga bakin ki ta fito kuwa"? shiru nai cike da damuwa na sake sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna, ganin bance komai ba Baffa yace "ina sauraron ki" su dai su Baba basu ce komai ba, cikin ramar murya shima da ƙyar na haɗo kalmomin nace "e...eh inason komawa naci gaba" ƙwafa Baffa yayi yace "wllh kin bani mamaki Nu'aiymah! ni zaki mayar ƙaramin mutum? ki ƙi zaman aure sannan kice na barki ki cigaba da karatu? to ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni,cikin biyu dole ai ɗaya! ko ki haƙura ki koma gidan uban ɗanki kici gaba da karatu dan nasan bazai hanaki ba hasalima sai dai ya ƙara ƙarfafa maki guiwa,ko kuma kici gaba da zaman gida ba aure ba karatu in naga zaman ki ya isheni zan lallaɓa mai gadin nan na haɗaku aure, shashashar banza kawai tashi ki bani wuri" sosai maganganun Baffah suka soki zuciya ta, bansan sanda na fashe da kuka ba ina roƙonsa akan yayi haƙuri ya barni nayi karatuna,wata razananniyar tsawa ya daka min hakan ya sani tashi da sauri na fice ina kuka, sanda nazo fita naji Baba yana masa faɗan ai ba haka yakamata yayi ba amma bai kulasa ba yaci gaba da min faɗa, Mami na zaune a falo Mum a gefenta suna taɓa ƴar fira nazo na fice ta gabansu ina kuka,ko kallon inda suke banyi na haura sama zuwa ɗakina,wani sabon kukan takaici na saki ina bubbuga, bayan na haura sama Mum ta juyo tana kallon Mami da mamaki tace "me kuma ya same ta"? Mami ta ɗan taɓe baki tana gyara zaman agogon hannunt tace "makaranta takeson komawa, tun kwanaki ta faɗa min taga ban kula ba shine ta aiki kakar ta sanarwa ubannin nata, da safen nan suka turo Qaseem kiranta ba mamaki koro ta sukai yanzun shisa take iskancin nan" Mum ta sauke numfashi tace "amma sai nake ganin da an barta wllh tunda tana buƙatar hakan" Mami tace "ni kaina ina son taci gaba da karatunta tunda kinga tayi nisa aure ne ya daƙile mata karatun, mahaifin kuma yace muddun bazata koma gidanta ba bbu ita bbu makaranta sai dai ta zauna ba aure ba karatun" ta faɗa cike da damuwa, "danƙari!!" shine abinda Mum ta faɗa ita ma fuska cike da damuwa, then ta ɗago tace "gaskiya yakamata musan matsaya dan sam! banga amfanin zamanta a gidan nan ba ita ba mai aure ba ita ba sakakkiya kuma ba karatu ba! dole cikin biyu ayi ɗaya Maryam" Mami ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki tace "to Allah ya zaɓa mana abinda yafi Alkhairi ya kuma yi mana kyakkyawan jagora" ta amsa da "amin" sun jima suna tattaunawa dangane da matsalar daga bisani Mum Fareeda tayi mata sallama ta fice bayan ta kwantar da Papi gefen Mami, naci kuka har na gode Allah, kiran sallar asuba yasa na miƙe daga kan gadon ina layi na faɗa Bathroom na sakarwa kaina shower, sosai naji daɗin jikina, na ɗauro Arwalah na fito na zura doguwar rigar abaya baƙi da ya sha baƙaƙen stones masu kyau da ƙyalli, na taje gashin kaina bayan na busar na shafa masa mayukan gashi masu ƙamshi na ɗaure da baƙin ribon, na zura dogon hijab na tayar da sallah, na jima sosai ina roƙon ubangiji a sujjadata ta ƙarshe,cikin hawaye nake roƙon Allah yayi min zaɓi mafi Alkhairi. bayan na gama na zauna saman dardumar ina jan carbi naji an fara nocking, na miƙe na naɗe sallar na buɗo ƙofar, sabuwar maid ɗin Mami ce tsaye a ƙofa riƙe da Papi dake kuka, ta miƙo min shi bayan mun gaisa na kullo ƙofar na dawo na zauna gefen gado ina cilla Papi sama ina caɓowa, ya wangale baki yana ta min dariya har dimple ɗinsa na lotsawa, da zaran na dakatar da wasan da nake masa sai ya wage baki zai yi kuka hakan yasa ni fahimtar yunwa yake ji,na ciro abincinsa na saka masa a baki duk da nima tun abincin safe ne a cikina gashi kuma har marece tayi. A ɓangaren Salima tunda akayi sadakar bakwai ɗin Mumcy taci gaba da sabgogin gabanta hankalinta kwance,bbu ruwanta da kowa karuwanci da yawace-yawace kuwa sai abinda yacigaba,har wani sabon salo ta tsiro dashi na tara manya-manyan ƴan duniya a gidan wanda ta riga da ta mallakawa kanta dan acewarta gidan ya zama nata, har aƙabi akewa gidan da gidan ƴanci,duk wata cikkakiyar ƴar duniya da wani cikakken tantirin da kake buƙata zaka samesa a gidan kai harda ƴan daudu, a yawace-yawacenta ta haɗu da wata ƴar daɓas wadda dasu tazo ɗaya kusan duk halinsu ɗaya shisa tasu tazo ɗaya suke zuba abota fiye da tunanin mai karatu, duk sun san sirrinkan junan su har ta kai ƴar daɓas ta dawo da zama a gidan ƴanci itada saurayinta Shaho,tunda Shaho ya ƙyalla ido yaga Salima yaji ta kwanta masa,tun yana ɓoye mata har ya fito fili ya bayyana mata abinda ke ransa gameta,da farko ta ƙi amincewa sbd abotar dake tsakaninsu da ƴar daɓas bazata iya cin dunduniyarta ba,amma a ƙarshe da taga yadda Shaho ya birkice mata yasa ta yakice komai a ranta ta karɓesa hannu bibbiyu dan acewarta gidan bariki bbu wani batun yadda ko amana kowa tashi ta fishsheshi, haka Shaho da Salima suka dinga sheƙe ayarsu ba tare da sanin ƴar daɓas,har ta kaisu ga yanke hukuncin yin aure,inda Salima tace ta ɗau nauyin komai zata sayar da gidan ƴanci ta kori karuwan ciki su gudu subar unguwar suje can suyi aurensu,a take kuwa yayi na'am da batunta, a lkcn ƴar daɓas tayi tafiya gun wajen wani Alhajinta, hakan ya basu dabar aiwatar da komai cikin kwanciyar hankali,kasancewar gidan Babba ne sai yayi kuɗi sosai,koda ta karɓo kuɗin ta damƙa su a hannun Shaho dan ita kanta ta rasa dalilin da yasa komai yasata cikin rawar jiki zata aiwatar dashi, a haka suka samo iyayen ƙarya sukaje aka ɗaura musu aure suka koma can wata unguwa suka siyi wani ɗan madaidaicin gidan sukayi zaman su hankalin su a kwance. wata ɗaya tak da aurensu ta fara ganin canjin rayuwa a tattare dashi,duk da dai ta damƙa masa duk kuɗin tace ya nemi sana'a yanata raina mata hankali da faɗin zaiyi tayi haƙuri akwai abinda yake jira, sai kuma wani sabon salo da ya tsiro mata dashi na fitar dare, zaici uban kwalliya kamar bashi ba, sai ya bari tayi bacci ya silale yabar gidan, irin so da ƙaunar da take masa ne ya hanata yi masa faɗan fitar da yake,haka rayuwa tacigaba da tafiyar musu har ta kai ta kawo ko na abinci ya fara musu wuya dan kuɗaɗan da ta damƙawa Shaho duk ya ƙarar dasu, Salima bazata iya rayuwar talauci ba! hakan yasa tarihi ya fara maimaita kansa dan tuni ta koma rayuwarta ta baya kuma da auren shaho a kanta, ya zamana tun safe duk suke fita kowa zaice yayo buga-bugarsa daddare a haɗe gida, haka rayuwarsu taci gaba da tafiyar har tsawon watanni biyar, a lkcn Salima ta samu ciki wanda ta kasa gane ko na Shaho ne ko kuma na abokan tambaɗewar ta,bata wani tsaya ɓata lkc ba taje assibiti ta buƙaci a zubar mata dashi, aikuwa ta cika likitan da kuɗi ya zubar da cikin, bayan wasu ƴan kwanaki ta dawo daidai taci gaba da abunda ta saba, su Salima likkafa taci gaba dan tunda ta fahimci tara karuwai a gidanta yafi komai kawo mata kuɗi ta fara tara ƙananan karuwai harda gogaggun ma da suka jima ana damawa dasu a rayuwar bariki,sosai take samun kuɗi ba na wasa ba, hakan yasa ta sake ɗaura ɗamarar gyaran gidan nata tayi ɗakuna sama da goma, in kai mazaunin gidan ne zaka kama haya in kuma za kazo ka biya buƙatarka ka tafi ne ita zata yankar ma kuɗin da zaka biya ta kuma haɗaka da daidai kai,ita kanta ba'a barta a baya ba dan tana da nata Alhazan da suke sheƙe ayarsu, shima Shaho da ya fahimci haka ya koma ta bayan gida yana mu'amala da yaranta dan yanzu sam bata lkcn sa. A ɓangare ƴar daɓas kuwa tun sanda ta dawo daga yawon ta zubar ɗinta ta samu lbrn wai Shaho da Salima sunyi aure, sabon tashin sense kenan, dan sosai take neman su ido rufe cike da Alkwashin mummunan fansa a ranta, tayi Alƙawarin sai ta sakasu kuka da idonsu fiye da wanda ta zubar, sai ta salwantar da rayuwarsu ta baƙanta musu, taya ma za'aje saurayin da take bala'in so da ƙaunar itace cinsa ita ce shansa sannan ace rana ɗaya ƙawar da ta yarda da ita tayi nasarar ƙwace mata shi? Inaaa! wannan abun ba mai yiwa bane Tabbas! zata nuna musu sun taɓo tsuliyar dodo sannan kuma ba'a taɓa ta a kwana lfy. A ɓangaren su Zuhra ma cikin shekara ɗayan nan da ta wuce abubuwa dadama sun faru, ciki kuwa harda kammalur karatun Yayanta Jafar wanda yanzu ya zama cikakkan lauya mai zaman kansa,tuni suka tsinci kansu cikin canjin rayuwa, Jafar ya gyara musu gidan daidai gwargwadon ƙarfinsa, sunfi ƙarfin ci da sha cima ko wace haka ma sutura, har mai aiki guda biyu ya ɗauko da mai gadi, sai kuma haɗuwa Zuhra da Salim abokin Jafar wanda shima ya kasance Lauya,tun ranar da ya ƙyalla ido ya ganta ya susuce, Jafar ɗin da kansa yayi masa jagora wajen Zuhra har ta karɓi soyayyarsa, Tuntuni yaso aiko da magabatansa amma Zuhra tace ya dakata sai ta sauke Alƙur'ani dan sosai tsoran Allah ya ratsa zuciya da gangar jikinta, ta yi Alƙawarin gyara rayuwarta fiye da tunanin mai karatu shisa take ƙoƙarin ceto lahirarta, ta rasa na boko to Tabbas zata bada himma wajen samun na lahira,ita ta hana Salim turo magabatansa dan tana daf da yin Sauka a wata sabuwar makarantar da aka buɗe can cikin gari, tsakanin da Salim kam sai Ma sha Allah! dan sosai suke gudanar da wata tsaftatacciyar soyayyarsu, nutsuwar da Zuhra tayi a halinsu yanzu na mugun bawa ƴan uwanta da ita kanta Mama mamaki dan zuwa yanzu sun gama yadda haƙiƙa Zuhra ba tayi tuban muzuru ba, burin Zuhra bai wuci ta haɗu da Abdull da Nu'aiymah ba domin ta nemi yafiyarsu, tsakanin da Salima kuwa kullum tsinuwa da Allah ya isa ne, yau ma kamar safe tun safe driver ya wuce da ita Slamiyya bayan ta gama ayyukan ta. ganin dai anƙi hanani karatun ni da Leilah muka shawarci junanmu akan zamu dinga zuwa wata sabuwar Slamiyya da aka buɗe nan ƙasan layinmu, duk da dai yanzu shekaru kusan biyar da yin sauka, hadda kawai nake sai bitar sauran littafan addini, satin mu ɗaya kenan da fara zuwa kuma Alhmdllh muna jin daɗin makarantar, ƙarfe takwas muke zuwa mu tashi ƙarfe sha ɗaya, yau ma kamar kullum tafiya muke ni da Leilah muna taɓa ƴar fira, muna daf da shiga makarantar naji munyi karo da mutum,na ɗago da sauri ina kallon ko waye.

_Ngd sosai da Addu'oinku sisters, in kun karanta ku daure kuyi share da comment dan Allah musanman ƴan ONE BLOOD fans bana ganin kuna yin share ku daure kuyi share ga sauran groups please._🥰😍😘

ONE BLOODWhere stories live. Discover now