part 31-32

74 10 0
                                    

*ONE BLOOD*

_31-32_ ✍🏼

"Aunty ban fahimci zancen ki ba, kina nufin wannan shine mijin da Aunty Salima ta aura"? cike da gajiyawa matashiyar budurwar ta miƙe zaune daga kwancen da take tace "wai so nawa kikeso in maimaita maki zance? nace miki nima Ummi ta turo min photon nan tunda nima banje bikin kema haka tou meye fa'idar tsareni da tambayoyi kamar wata ƴar jarida"? Nasreen tai murmushi tace "hum bazaki gane bane shisa, wlh nasan wannan mutumin da daɗewa" wani kallon karki rainamin wayo Lubna ta watsawa ƙanwarta Nasreen kafin ta kai ga cewar komai taga ta miƙe tsaye ta buɗe wata ƙaramar sit ɗin kayayyakinta masu muhimmanci, ba jimawa sai gata ta dawo da wasu takardu da ID cart, Lubna ta karɓa ta buɗe da sauri ilai kuwa shine tsaye a cikakkan namijinsa cikin kakin sa na soja dake Massifar fito da ainahin kyawunsa da kamalarsa ga kuma sunan sa nan a rubuce, cike da damuwa Lubna tace "tou meyasa tuntuni baki mayar masa da kayansa ba, ga dai phone number ɗinsa nan da kuma adress ɗin wajen aikin su, to yanzu dai ba wannan ba ki shirya ki kaiwa ita Salimar har gida ta bashi kayansa" Nasreen ta turo baki tace "no da kaina nake son basa zan gwada kiransa ko nai masa text message" daga haka ta mayar da kayan inda ta ɗauko ta fice daga ɗakin tana saƙe-saƙe, Lubna ta bita da kallon tuhuma daga bisani kuma ta taɓe baki taci gaba da operating ɗin wayarta.

ta ƙofar baya su Aliyu suka shigo su ka yi parking a daidai part ɗinsa, Sultan ne yay azamar buɗe baya da niyar ce mata ta fito sai ya samu tana bacci, yay tsai ya ƙurawa baby face ɗinta ido har Aliyu ya iso yana tambayarsa lfy? kafin ya basa amsa yaga yadda ta barbaje tana kwasar bacci alamun allurar baccin da Dr yayi mata bai gama sakinta ba, Aliyu ya katse shirun da faɗin "tou ya za'ayi kenan? in har muka cigaba da tsaiyuwa anan wani zai iya ganinmu" Sultan ya ɗaga kafaɗa da alamun shima bai sani ba, Aliyu yaja tsaki ya buɗe murfin motar ya fara tashin ta, a hankali ta buɗe fararan idanunta a kansu, Aliyu yayi mata alamar da ta fito waje, ba musu ta fito su ka yi gaba tana binsu a baya har suka iso wani haɗaɗɗan part wanda tsaya faɗa muku kyansa da tsaruwarsa zamu ɓata lkc sosai, komai na falon golden color ne saɓanin tangamemen plasma ɗin dake manne a bangon ɗakin, Aliyu da kansa ya kaita har wani ɗaki yace ta shiga ta kwanta yana zuwa sannan ya fito falo inda yabar Sultan, sun jima suna tattaunawa sannan Sultan yay masa sallama ya fita. tana shiga ɗakin ta haye saman lallausar bet ɗin ta kwanta tayi lamo ƙwallurar kanta na juyawa, da zaran ta rumtse idanunta sai taji tamkar tana son tuno wani abu amma sai ta kasa, ganin kanta ya ɗau zafi sosai yasa ta kwanta ta rumtse idanu tana fitar da wani hucin zafi, ga kuma ciwon mara na zallar buƙatuwa dake nuƙurƙusarta.

Mami na kaiwa bakin gate ɗin gidanta ta fara horn har mai gadi ya buɗe mata ta kunno kai harabar gidan, a parking space tayi parking ta fito rataye da jakarta su Noor na biye da ita, Hadiza da wani mai bawa Flower ruwa a gidan ne suka fara shigo da kayan ciki har suka gama, gidan bashi da wani datti sosai ƙura kawai yayi, cikin ƙanƙanin lkc ta gyara ko ina yayi fess snn ta shiga kitchen tai musu girki. Mami ce zaune saman darduma tana jan carbi bayan ta gama sallar isha, gabaɗaya ta rasa kalar tunanin da zatayi, ita kaɗai tasan irin zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke mata, yarinya ta ƙaramin ciki ta ɓace ɓat kamar walƙiya kuma har yanzu bbu wani lbr? Allah shi kaɗai yasan halin da take ciki ko ta mutu ko tana da rai, tun tana kuka har ta saduda ta barwa Allah maji roƙon bawa komai, a yanzu addu'ar ta da fatan ta shine Allah ya tsare mata ita ya kuma sa ta faɗa hannu na gari, kuma ta yanke hukuncin za taje ta samu wani malami dake can ƙasan layinsu ta bashi kuɗi ayi saukan Alƙur'ani da sauran abubuwan da suka dace ayi.

a mugun fusace Acp ya watsar da takardun gabansa ya fara mgn cikin kaɗuwa mai nuna zallar ɓacin ransa "ba matar ɗan sanda ba! wlh ko matar shugaban ƙasa ce ita sai ta bani amsar tambayoyi na, shashashan banza wanda baisan me yake ba, abun duniya ya riga da ya rufe maku ido, kunyi nisa bakwa jin kira so ina son ku gane cewar ni bbu wanda ya isa ya soye ni da kuɗi! kuma ina kan aikin da ya dace da ƙasata ne wajen ƙwatarwa bayin Allah haƙƙinsu, so ka ɓacemin da gani maza sannan ita kuma ku samin ita a cell" Salima da tayi narai-narai da idanu zallar rashin gaskiya shimfiɗe a fuskarta ta fara mgn cike da magiya "yallaɓai kayi haƙuri ka fitar dani cikin wannan case ɗin wlh bansan komai ba, sati na uku da aure zaku nemi ɓatamin suna a duniya da laifin ɓatar kishiya? bansan hawa ba bansan sauka ba hasalima tunda nazo gidan ko ganinta ban taɓa yi ba, haka kawai kun ɗauko ni daga gidan aure na ba tare da sanin mijina ba, idan yazo ya samu bananan me kukeson in faɗa masa"? Acp yayi wani murmushi mai tarin ma'anoni bayan ya gama tsintar abinda yake so a kalaman Salima, da ido yaywa wasu ƴan sanda mata alama da su kamata su cillata a cell har bakinta ya mutu sannan su fito masa da ita su ɗora daga inda suka tsaya.

Misalin ƙarfe tara na dare, Aliyu ne zaune a falonsa suna video call da Amminsa da ƙanwarsa Yasmine, fira suke sosai cike da annashuwa har Mamansa take tambayarsa yaushe zai shigo ƙasar, yayi ɗan murmushi yace "kwanan nan naso muku surprise but wata ƴar matsala ce ta hanani zuwa son zaku ganni ba zato ba tsammani In shaa Allah" Ammi tayi murmushi cike da ƙaunar ɗan nata tace "tou Allah yay maka jagora a lamuranka na yau da kullum, ya sawwaƙe" ya amsa da "Ameen" cike da shagwaɓa Yasmeen tace "wlh Yah *MAN* i missed u so much dan Allah kazo kwanan nan" bai kai ga bata amsa ba mai kula da ɓangarensa tayi sallama, yayi musu sallama da uzurin yayi baƙuwa anjima zai kira, Rabi ta zauna ƙasa ta gaishesa ya amsa da ƴar fara'a, bayan few minutes Aliyu yace "dama na kira ki zan baki amanar matar abokina da ya tafi wani aiki ƙasar waje, matarsa na da ƙaramin ciki ba zata iya tafiye-tafiye ba kuma basuda wasu ƴan uwa a garin nan, shisa suka buƙaci ta zauna nan na tsawon ƴan kwanaki mijinta na hanyar dawowa, to kinga ni ba mazauni bane shisa nakeson na baki amanar ta ki kularmin da ita yadda ya kamata, zan ƙara miki Albashin ki kuma banason wani yasan zaman ta a gidan nan" ƴar dattijuwar matar tayi murmushi tace "In sha Allahu bazan baka kunya ba kuma zaka sameni mai cika Alƙawari" Aliyu yayi mata godiya sannan ya sallameta ta fice. ɗakinsa ya shiga ya fito riƙe da ledoji ya nufi ɗakinta, bakin ƙofa ya tsaya ya fara nocking, ta fito daga wanka kenan ɗaure da towel ta tsaya gaban mirror taji nocking, bbu ko hijab a jikinta ta nufi ƙofar ta buɗe, da sauri Aliyu ya kawar da kansa ya ajiye mata ledojin a ƙasa yayi tafiyarsa ba tare da yace da ita uffan ba. Nu'aiymah ta share ƙwalla ta bisa da kallo ta durƙusa ta ɗauki ledojin ta koma ta rufe ɗakin, kayan sawa ne dana shan iska dana bacci da hijabai da sauran kayayyakin amfani na mata, kayan bacci masu kauri ta saka ta haye kan gadon, ta jima tana tunani tana jin kanta cikin kewa da son tuna wani nata amma ta kasa tunawa and da zaran ta damu kanta da son tuna ita wace sai taji ƙwallurar kanta ya ɗau zafi ɗan tunanin ta ya fara rikicewa.

muskutawa Mama tayi ta dafa kafaɗar Zuhra cike da damuwa tace "yanzu bakya tunanin wannan tunanin ya haifar maki da wata matsala"? firgigit ta dawo tunaninta ta dubi Maman tata tace "nidai Mama na rasa kalar tunanin da zanyi, bansan wace irin rayuwa nake ba da kuma matsayina, mai aure ko bazawara, nidai ina ganin zanje na samu mahaifiyar Abdull ta tilasta masa ya sakeni, bazan iya zama da maci amana irinsa, sun cuceni sun zalunceni sun hanani zaman aure, wlh Mama nayi danasanin abubuwan dana aikata a baya, nasan Allah ma bazai yafemin ba har na koma ga mahalacci na, wani lkcn na kanyi baƙin cikin zuwana duniya na kanji kwata-kwata banida sa'a a duniya, na hana Nu'aiymah zaman aure da mijinta gashi ni kuma wadda ban taɓa tunanin za taci dunduniyata ta hanani zaman aure da mijina, kaico! kaico!! kaico!!! na, Allah na tuba ya Allah ka yafemin ka sauƙaƙa min lamura na dan girman zatinka da isarka ya Rabbi" ta ƙarashe maganar cikin matsanancin kuka mai tsuma zuciyar mai karatu.

Jiya nayi typing ya goge shisa kuka jini shiru. Share comments dan manzon Allah.

_Nu'aiymah Abdull_ ✍🏼

ONE BLOODWhere stories live. Discover now