*ONE BLOOD*
*_@Wattpad AbdullNu'aiymerh_*
_Episode 39-40_ ✍🏽
Sosai Salima ke cin wuya a hannun jami'an tsaron, tun tana masu taurin kai har ta fito fili ta gaya masu gaskiyar abinda ya faru, Acp bai wani tsaya ɓata lkc ba da kansa yaje har gida yay masu bayanin komai yadda Salima tai masa, a lkcn jikin Abdull yayi kyau sosai ya dawo normal kamar daa! a ranar Abdull ya zubar da hawayen baƙinciki bana wasa ba kai kace ba gawurtaccen sojan nan ba mai ji da isa da gadara, wata irin sabuwar tsanar Zuhra ce ke taso masa a ƙahon zuciyar sa, Salima kam ji yake muddun su ka yi ido huɗu da ita bbu abinda zai hanasa shaƙeta har lahira, wai shine ya auri Salima har wata mu'amala ta auratayya ta shiga tsakanin su? Salima da ta zama ta kowa ko wane kare ya tayata sai ta buɗe masa ƙafafu? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, sun cuceshi sun zalunce shi sun salwantar masa da ƴar uwarsa kuma matar sa, yanzu Allah kaɗai yasan tana da rai ko ta mutu, tana cikin mawuyacin hali ko kuma tana cikin ƙuncin rayuwa shi dai fatansa da addu'arsa shine Allah ya kare masa ita da abun dake cikinta yasa sun faɗa hannu na gari, waƴan nan abubuwan su suka tsaya masa a rai, ya kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Acp yace "to nidai yanzu na gama aiki ina ganin zan turaku kotu kawai aje a ƙarasa zancen a nan dan wannan case ɗin naku babba ne" Baffah ya girgiza kai yace "nidai a matsayina na mahaifin Nu'aiymah nake roƙon Alfarma da abar maganar zuwa kotun nan, nafison fiyayyan halitta yayi mana sakayya ga duk wanda ya zalunce mu, kuma In shaa Allahu tun a duniya mutum zai fara ganin ishara domin kuwa Allah ba azzalumin bawansa bane so dan haka ku ƙyaleta taje ita da Allah kuma mun barta da Allah yay mana sakayya daidai gwargwadon haƙƙinmu" kowa yayi na'am da zancen Baffah amma banda Abdull, da ƙyar da siɗin goshi su Baffah suka rarrashe shi ya haƙura yabar zancen, a take gaban kowa ya rubuta ma Zuhra da Salima saki uku-uku sannan yabar falon cikin tsananin fushi sosai.
bayan sati biyu da zuwansu Nu'aiymah a US sosai take samun kulawa ga ƴan gidan tun bata sakewa har ta dawo ta saki jiki dasu tamkar ƴar gidan, Ammi ta nemi shawarar Aliyu akan me zai hana su kai Nu'aiymah a boutique Slamique ɗin nan masu bada taimakon maganin karya sihiri ko wani abu makamancin haka ko Allah zaisa a dace yarinyar ta dawo hayyacinta su meƙata ga ahalinta lafiya, abu na biyu kuma cike take da kwaɗaituwar son ganin Ahalin Nu'aiymah dan tabbatar da zargin da take dan kuwa ruwa baya tsami banza, sosai shima Aliyu yayi na'am da zancen washe garin ranar yaje ya samo wani babban malamin da ya ƙware sosai a harkar ruƙiyya da kuma bada taimakon magungunan karya sihiri ya kawosa har gida, a falon baƙi aka sauke sa Ammi ta wuce ciki ba jimawa ta dawo riƙe da hannun Nu'aiymah dake sanye cikin dogon hijab har ƙasa, Ammi ta zaunar da'ita ƙasan kujerar da Malamin ke zaune a kai, kallo ɗaya yayi mata ya saki murmushin takaici ya buƙaci da a kawo masa garwashin wuta, Yasmine taje ta kawo masa sannan ya buƙaci duk su fita su basa wuri, suna fita ya buɗo wani garin magani dake ɗaure a farar leda ya zazzage cikin wutar ya kaisa daidai hancin Nu'aiymah ba tare da ta farga ba, wani mahaukacin tari Aiymah ta fara tamkar zata kifa cikin tsananin fitar hayyaci, ganin haka Malamin ya fara karanto ayoyin Alƙur'ani na karya mugayen sihiri, kusan minti biyar tana abu ɗaya da ƙƴar abun ya lafa ta zube a wurin a sume....
*WASA FARIN GIRKI*
