part 29-30

68 6 1
                                    

*ONE BLOOD*

_29-30_ ✍🏼

ƙofar ɗakin su Aliyu suka tsaya, dr da nurse suka ƙarasa ciki ya fara duba jikinta, sosai yarinyar ta bashi tausayi bayan ya gano larurar da ta shafe ta, yana mata mgn ta kasa bashi amsa sai dai ta gyaɗa masa kai ko ta girgiza masa kai alamun dai tana ji bata dai yin mgn ne, babbar damuwar ta biyu kuma itace perdre ɗin memory ɗinta da tayi wato ta manta komai da ta sani a baya, a matsayinsa na babban likita duk iya bincike-binciken da yayi ya kasa gano inda matsalar take, cike da damuwa ya juyo ya buƙaci su Aliyu da su koma offise ɗinsa za suyi mgn bayan ya umarci nurse da ta taimakawa Nu'aiymah tayi wanka tasha ko da tea ne. cike da Alhini dr ya gyara zaman sa ya fara masu bayanin duk abinda ke faruwa ya ɗora da faɗin "ni a ganina tunda abu yazo da haka me zai hana mu kai cigiyar ta a gidajen redio mu kuma sanar da hukuma asan abin yi" Aliyu ya jinjina kai cike da gamsuwa Sultan kuma ya fara girgiza kai yace "sam ban yarda da wannan shawarar, yanzu duniya ba yarda gashi kuma yarinyar nan ta manta komai, Aliyu me zai hana mu ɗauke ta harta warke sannan mu damƙata a hannun iyayenta, tashin farko naji yarinyar nan ta kwanta min arai kuma ta bani tausayi dan Allah mu taimake ta har ta warke kar ayi gaggawar sanarwa hukuma tunda bakasan dalilin fitowar ta daga inda take ba" "tou ai nima bance bata bani tausayi ba tou amma ya kakeson muyi? kaga bbu halin ka kaita gidanka kai da kake da mata tunda kasan halin shaiɗaniyar matarka, ni kuma da bani da mata ai ga matsalar Family na gashi kuma har yanzu ba'a ƙarasa ginin gidana da wlh zan kaita can na samo masu kula da ita har ta warke, Ammi na kuma bata ƙasar da inada tabbacin zasu zauna tare, tou ya zanyi kafi kowa sanin matsalata"

Sultan ya dafa kafaɗar Aliyu yace "duk abinda zai faru sai dai ya faru amma dole yarinyar nan sai ta kwana a gidan ku kafin mu samo solition, amma batun sanar da hukuma bai ma taso ba" "tou meyasa ka zaɓi wannan shawarar? in kuma matar aure ce fah ko kuma cikin shege tayo ta gudo daga gidansu?" Sultan ya watsa masa wani mugun kallo yace "kai nifa in batada aure da nafi kowa farinciki dan tashin farko yarinyar ta tafi da imani na" sai kuma ya juyo ya kalli dr dake musu dariya yace "ka taimaka ka bamu sallama muna da abin yi" ba musu dr ya rubuta musu magungunan da zasu taimaka mata sosai wajen dawo da ƙarfin jikinta, Sultan ya amsa yayi masa godiya ya fito ya samu Aliyu tsaye a ƙofar ɗakin tsaye ya harɗe hannuwansa a ƙirji yana tunani, wucesa Sultan yaso yi zai shige Room ɗin da aka kwantar da Aiymah Aliyu ya janyo hannunsa ƙii ya dawo dashi gabansa, fuska ba walwala yace "naji na amince sarkin azarɓaɓi, na yarda zan kaita gidan mu amma da sharaɗin muddun aka samu matsala wani daga cikin gidanmu ya ganta ya tambayi wacece zance dasu matar daka aura ce baka faɗawa kowa ba har kai mata koshi ka dawo da ita gidan sbd tsananin kishi irin na Fauziya matarka, kuma duk abinda zai faru ni bbu ruwana matsalar kace" ba tare da Sultan ya kawo komai a ransa ba yace "na amince" "good" faɗin Aliyu suna sakarwa juna murmushi daga haka suka kutsa kai cikin ɗakin dan ɗaukar ta su wuce dan Already doctor ya basu sallama.

Cikin kuka mai haɗe da zallar tashin hankali Mami ta riƙe kwallar rigar Baffah tana mgn "ka cuceni dr! bazan taɓa yafe maka in wani abu ya sami yarinyata, meyasa bakada tausayi? tun ina kawar da kai ina nuna maka kawaici akan yarinyata har kaje ka aikata abinda ba shi ba, badan ka koreta daga gidan nan ba da duk wannan bai faru ba, zan tattara na bar maka gidan ka da ƴaƴanka suma ka kashesu ko ka salwantar da rayuwar su kamar yadda rayuwar yayarsu ta salwanta sbd kai" ta ƙarashe maganar ta cikin kuka sosai, tayi baya-baya ta zauna saman gadon tana share zafafan ƙwallar da ta zubo mata, cike da tausayin ta Baffah ya zauna gefen ta ya kamo hannunta ya fara mata mgn cikin rarrashi da tausasa harshe "dan Allah Maryam kiyi haƙuri, kinga tun jiya ƴan sanda da gidajen redio da na jaridu suka bazama neman yarinyar nan, nasan halinki da haƙuri da tawakkali so dan Allah ki ƙara akai, ki daina ɗaga hankalinki In shaa Allah za'a ganta" cikin fushi sosai Mami ta fizge hannunta daga na Baffah tace "naji na karɓi ƙaddarar da ubangiji ya aiko min, amma inason ka sani aure na dai yazo ƙarshe dan dama igiyar aure na da kai ta daɗe tana rawa a gidan nan, to yanzu ina ganin wa'adinta ya cika ka sallameni na kama gabana dan na gaji da zama da murɗaɗɗan halin ka, haƙuri kawai nake da kai yanzu kuwa tura ta kai bango" tana gama faɗar haka tayi ficewar ta daga ɗakin gabaɗaya.

ɗakinta ta shige ta tattaro kayanta masu muhimmanci cikin babban trolly snn ta haɗa kayan Noor da Saif suma akwati biyu da sauran kayayyakin aikinta, ta fito ta miƙawa driver ya saka mata su a boot ɗin motar ta. sai da tayi wanka tayi sallah, mai aikinta Hadiza tai wa su Noor wanka ta shirya su suka fito a tare tana rataye da jakarta, zaune ta samu Baffah a falo yayi tagumi abin duniya yasha masa kai, sai da ta ƙare masa kallo da kumburarrun idanunsa tace "ina jiran takarda ta ko kuma ka samu  sammaci daga kotu" kasa ce mata komai yayi ya bita da kallo har ta kai ƙofar ɗakin yace "ina zaki kai min yarana"? cike da rainin hankali Mami tace "ohh! na manta fa, but ka nemo min yarinyata kafin na haɗasu duka na baka" daga haka ta fice daga falon, motarta ta shige suka bar gidan ba tare da ta yiwa kowa sallama ba.

ONE BLOODWhere stories live. Discover now