*ONE BLOOD*
*@Wattpad AbdullNu'aiymerh*
_Episode 43-44_✍🏽
https://www.wattpad.com/1115555552?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AbdullNuaiymerh&wp_originator=GZaTKERMmlyI7IVWlqK12p%2F9f%2B3td7jeBOARtLS0A6wfu9Q%2BgVcuyndOSEA7hlcRalXfHDawlFmKwNBBLIX%2F74hIogLjN3Dd67kjyQ%2Fu5fzqqHOQKj6x2I3CIUqTde4q
_FOLLOW ME ON WATTPAD PLEASE GUYS GA LINK NAN SAMA KU HANZARTA KAR A BARKU A BAYA MASU AMFANI DA WATTPAD_A ƙofar fita ɗakin Ammi na sami ya Aliyu a tsaye ya kasa kunne yana sauraran mu, yana ganina ya damke fuska ya juya yay kamar zai shiga ɗaƙinsa, murmushi kawai na saki ina girgiza kai na nace "dan Allah ka ban aron wayarka ina son kiran wayar Mami ne please wlh ina son jin muryarta" na ƙarasa ina langwaɓar da kai, "karki kira ta ki ɗaga mata hankali ki jira gobe da safe naje nayo mana bucking ɗin jirgin safe ki koma ciki ki sanar musu su kwana cikin shiri banaso mu ɓata lkc" yana faɗin haka ya shige ɗakinsa ya barni, jiki a sanyaye na koma ɗakin Ammi na sanar mata, da farko tace ita bbu inda zataje,da ƙƴar nima na shawo kanta ta yarda zata bimu sannan nai mata sallama na koma ɗakin Yasmine, bbu wani shirin da zanyi shisa nai wanka na kawai na haye gadon nai lamo ina tunane-tunane, bacci ne ya kasa ɗaukata har Yasmine ta shigo ɗakin tana danne-dannen wayar ta, ina jinta tana tsokanata amma na lumahe idanu kamar mai bacci da haka har bacci ya ɗaukeni bayan na tofe kaf ilahirin jikina da addu'oin tsari daga Rabbi! da asuba kiran sallar farko na farka, sai da nai wanka na ɗauro arwalah na fito na tada Yasmine sannan na tada sallah, bayan na gama azkar na zame na kwanta saman sallayar wani baccin ya sake yin awon gaba dani, ban farka ba sai ƙarfe bakwai daidai kuma bbu Yasmine a ɗakin, tsaki kawai naja na shiga bathroom nai brush na fito na ɗauko doguwar rigar atamfa ƴar ganah na kashe ɗauri, tsaye nai gaban madubi ina ƙarewa kaina kallo, na rame sosai har ƙashin wuya ya fito dama ba wani aukin ne dani ba, yanzu kuwa sai manyen idanun da hasken fatan daya rage duk nayi fayau dani, baki na yage zan fashe da kuka kenan Yasmine ta shigo tace ni kaɗai ake jira na fito kar muyi missing ɗin flight, rai na cire rigar na koma wadrop da ƙyar shima na samu wata jar rigar roba-roba na zura dogon hijab har ƙasa na fito, zazzaune duk na same su a falo ni kaɗai suke jira, fira suke sama-sama na samu wuri na zauna bayan na gaishe su sun amsa, Ammi tace "yi sauri ki tashi kisha ko tea ne kafin mu tafi zama da yunwa zai iya haifar maki da matsala" ba musu na tashi na haɗa tea a gaggauce na gama duk muka fito muka shiga mota driver yaja mu sai Airport, ƙarfe takwas daidai jirgin mu ya lula saman gajimare zuwa ƙasar mu ta haihuwa.
Mami ce kwance a gadon ɗakinta tayi shiru abin duniya ya dameta, yau ko falo ta kasa fitowa tana kwance sai juyi take, misalin ƙarfe goma na safe ring ɗin wayarta yasa ta sakkowa daga gadon, ganin wayar ta mutu yasa ta share ta shige, tana fitowa ta samu wayar tana ring kuma, ta ƙarasa ta ɗauki wayar tana kallon numbar, ganin kiran wayar Baffah ne yasa ta ɓata fuska amma ta daure ta haɗiye wani abu mai ɗaci sannan tayi picking tare da sallama, ya amsa sallamar yace "gani nazo gidan ina tare da baƙi ki fito ina son mgn dake" daga haka Baffah ya katse kiran, Mami ta sauke a jiyar zuciya mai nauyi sannan ta hau shirin ta a nutse, ko da ta gama bata fito ba sai da ta gyara ɗakinta tsaf sannan ta nufi ƙasa, a hankali take takowa daga steps tana sanye cikin wani tsadaddan farin less irin na manyan matan nan ƴan ajin tubarkallah😆ko maƙiyin ta ya kalleta sai ya ƙara balle masoyi irin su Baffah (lol), tana ganin waƴan da Baffah yazo dasu ta ɓata rai dan tasan meke tafe da su, Baba shagari da uncle Sulaiman, Uncle Malik sai Baba Manir sai wani Malam Imam da sauran matan matan su, bbu yaro ko ɗaya sai Abdull da Qaseem dake zauna kusan iyayen su, danne abinda ke ƙoƙarin taso mata tayi ta ƙaraso falon ta zauna gefen Mum Fareedah ta gaisa dasu a mutunce, Abdull da Qaseem ma suka gaisheta ta amsa musu ba yabo ba fallasa, kitchen ta koma tasan mai aiki ta kawo musu ruwa da lemo sannan ta dawo, Then Mlm Imam ya buɗe taro da addu'a kenan wayar Mami dake gefen ta ya fara ring hakan ne ya dakatar dashi, Mami ta ɗauki wayar da niyar ɗorawa mode flight kenan taga baƙuwar number, haka kawai ta tsinci kanta ta ɗaga wayar da sallama. ƙarfe goma daidai jirgin mu ya sauka a Airport, nan Abdull ya buƙaci da in basa no ɗin Mami ya kirata, duk yadda naso ya bani wayar ni nai mata mgn amma yaƙi yarda acewar shi zan ɗaga mata hankali ne kawai gwara ta ganni ido da ido zaifi, haka dai na haƙura na ƙyalesa har yayi dialing numbar ta ya kara a kunne duk mukayi tsuru-tsuru muna jiran muji me zai ce "wa'alaiki Salam dan Allah ina mgn da Dr Maryam ne"? kai tsaye Mami ta amsa da "eh ita ce" Aliyu yace "ya gida ya aiki"? tace "Alhmdllh mun gode Allah" yace "Ma Sha Allah! dama wata ƙanwata ce take buƙatar adress ɗin gidan ki tana son zaku tattauna wata muhimmiyar magana ne" Mami tace "Okay! zan tura maka a text message amma gaskiya yanzu banida lkc sai dai ta jira har wani lkcn tukun" "ba damuwa Ngd sosai" tace "ba komai daga haka su kai sallama ya katse kiran, mintuna biyar kacal! sai gashi ta turo masa adress ɗin, murmushi nai nace "to wai an gaya maka bansan gidan bane da zaka wani kiranta ka gaya mata"? yace "yo wa ya sani abu a duhu" murmushi na kuma yi nace "haka ma zaka ce ko? to inga wayar" ya miƙo min na karɓa ina kallon adress ɗin da Mami ta aiko masa, cike da mamaki nace "tou kenan Mami ta koma gidan ta ne bansani ba"? sanin banida mai bani amsa yasa nai shiru muka shige motocin muka bar harabar Airport ɗin, da kaina nai ta masa kwatance har muka iso ƙofar gidan, duk muka firfito cikin motar muka ƙarasa bakin gate mai gadi ya buɗe mana muka shige gidan, motoci ne birjik kusan su shida fake a harabar gidan, gabana ne yayi wata irin bugawa ganin har da motar dodon nawa, dakewa nai cike da son cire duk wani fargaba a raina dan nima lkc yayi da zan ƙwatarwa kaina ƴanci, a hankali naji wasu zafafan hawayen tsanarsa sun silalomin ta cikin kwarmin idanu na, Ammi ce ta fara danna bell duk muna tsaye bayanta, Mami ta ƙwalawa Hadiza mai aiki kira tazo ta buɗe, ganin baƙi ne yasa Hadiza ta koma ciki tace da Mami tayi baƙi, Mami tace "Ohk ki barsu su shigo sai ki wuce dasu falon baƙi har mu gama" ta amsa da "to" ta koma dan yi musu iso, da sallama Ammi ta shigo falon duk suka juyo suna son ganin mamallakiyar muryar dan cikin su ƙalilan ne basu gane muryar ba! cikin tsananin tashin hankali ta firgici wanda ba'a saka masa rana Baba Shagari ya miƙe tsaye yana nuna ta da yatsa, da ƙyar da siɗin goshi ya samu ya ambato sunan ta "Asma'u! ke ce!! da gaske nake gani gabana kuwa"? Ammi tayi wani murmushi tana girgiza kai tace "ƙwarai kuwa Malam Shagari! ai kasan ranar bikin farar kura balbela ba sai an gayyace ta ba!" ta ƙarasa faɗa tana watsa masa wani kallo, duk su ka yi ƙuru-ƙuru suna kallon Ikon Allah dan kaf ɗin su ƙalilan ne basu santa ba, ganin feeling ɗin da suke ciki Ammi ta dawo da dubanta ga Shagari tace "ɗan da ka nemi kashewa shekarun da suka gabata na kawo yaga mahaifinsa amma fa badan mugun halinka ba, nayi haka ne dan sauke nauyin dake kaina" tana gama faɗin haka ta juyo tace "ku shigo mana" Aliyu ne gaba sai Yasmine sannan ni a bayan su, tsaya faɗa muku irin tashin hankalin da suka shiga lkcn da su ka yi tozali da fuskojin Nu'aiymah da Aliyu wlh ɓata lkc ne amma na baiwa kowacce dama ta ƙiyasta. "Nu'aiymah!" cewar Baffah kenan da Abdull kenan, sauran mutanen falon kuma hankalinsu ya karkata ga kallon Aliyu dake tsaye fuska ba yabo ba fallasa, Mami kam kowa ya kasa fahimtar ainahin yanayin da take ciki, da gudu Aiymah ta ƙarasa ta rungume Mami tana wani irin kuka mai ɗaga hankalin mai sauraro,cire duk wata kunya Mami tayi ta rungume ƴarta tsam a jikinta suna kukan tare aikuwa kallo ya dawo kansu, kallon su Kawai ake cike da tausayawa Baffah ya share hawaye ya koma ya zauna inda ya tashi, Qaseem da Aliyu aka tsaya ana kallon-kallon haka ma kowa na falon suka dawo da kallonsu ga Aliyu, wanda suka san sa tun yana yaro sun ganesa wanda ma basu sanahi ba zuciyarsu ta raya masu cewar duk inda ya fito daga tsatson Shagari yake saboda tsananin kamar su tamkar an tsaga kara, Ummah kam ƙiris kawai ya rage ta saki fitsari a zani (ni kuwa nace "ƙarshen Alewa ƙasa"). a hankali Baba Shagari ya tako inda Aliyu yake ya kamo hannunsa yana ƙara kallonsa, Aliyu ya ɗauke kai Shagari ya fashe da wani matsanancin kukan nadama ya rungume Aliyu tsam a jikinsa yana kukan, kasa haƙura yayi dan shima zuciyarsa tayi rauni, jin kuka mahaifin nasa yake har a ƙasan ransa da ƙyar aka ɓamɓare su aka zaunar, kowa ya samu wuri ya zauna banda Abdull,sai bin Aliyu da Nu'aiymah da kallo kowa yake tamkar sun sami Tv, ga dai tambayoyi birjik a ransu amma bbu damar yi, Mlm Imam yace "Alhamdulillah ala kulli halin, godiya ya kamata ku yiwa ubangijin talikai da bayyanar ƴaƴanku guda biyu" duk suka jinjina kai cike da farinciki masu baƙinciki kuma ƙiris ya rage zuciyoyinsu su fashe, Nidai tun zuwan mu nake maƙale da Mami tamkar wata mage, ƙin ɗagowa nai na kalli kowa sai ɓoye fuskata nake a jikin Mami tamkar wacce batada gaskiya. "dan girman Allah da manzon sa ki yafe ni Asma'u, ki gafarce ni wlh sharrin shaiɗan ne" Ammi tayi saurin ɗaga masa hannu tace "baka min komai ba Shagari! kanka kaiwa kuma na daɗe da yafe maka tuntuni ya rage tsakanin ku da ɗanka, Allah shi yafe mana baki ɗaya" kowa ya amsa da Ameen, daga nan ta basu lbrn haɗuwar Aliyu da Nu'aiymah, har zuwan su US bata ɓoye musu komai ba, nan ma tuni masu raunin zuciya suka fara hawaye, Shagari kam yasha kuka har ya gode Allah! sai Yamma liƙis Ammi tai haramar gidan barin gidan, duk yadda Mami tayi ƙoƙarin shawo kanta dan ta zauna nan amma taƙiya but tace zata dawo ta kawo ma Mami ziyara ta musanman da haka ta samu Mami ta barta ta tafi ɗin amma ta hana Yasmine da Aliyu tafiya, har mota duk suka rakota suna ƙara mata godiya, tana tafiya su Baffah suka bar gidan aka Abdull zaune a wajen ko niyyar tashi bashida, mota ɗaya Aliyu da mahaifinsa suka shiga da Qaseem, sauran ma suka shige motocinsu suka bar haramar gidan Mami, ina ganin Mami taje rakasu na ɗago ina kallon falon, bbu kowa sai ni hijab ɗin jikina na cire na shige kitchen tea nasa Hadiza ta haɗamin na zauna nan kitchen nasha na fito, sai yanzu naji ƙamshin turaran sa ya daki hancina, juyowar da zanyi mu ka yi ido huɗu dashi, cikin faɗuwar gaba na ratsa ta gefensa zan wuce naji ya kira sunana, gudu-gudu sauri-sauri na fara tsallake uptairs da bibbiyu, da ido Abdull yabi da dashi ganin bbu Alamun kowa a falon yasa yabi bayanta da sauri, tana daf da shiga ɗakinta na daa! ya damƙo hannunta ya mannata ga bangon ɗakin, rumtsa idanu nai hawaye suka fara zubomin, shirun shima yayi amma kana iya jiyo sautin bugun zuciyar sa, ganin yadda numfashin mu ke sauka cikin na juna yasa na fara turesa amma ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba! cikin rawar murya nace "please ka sakeni kar Mami ta shigo ta same mu a haka" "fushi kike dani ko"? na jiyo muryarsa a dodon kunne na, sai a sannan na ɗago ina dubansa mukayi ido huɗu tashi, mun kwashi kusan minti uku a haka nice ma nai yunƙurin janye nawa idanun dan bazan iya jurar kallon ƙwayar idonsa ba, Then Abdull ya buɗe lumsassun idanunsa masu firgitata ya ware su akanta yace "kinyi shiru Please Sweet cucumber kice wani abu mana" ya faɗi yana ƙoƙarin kissing ɗin wuyanta hannunsa na saman ɗan matashin cikinta yana shafawa da yanzu watan sa huɗu kenan kuma ya ɗan fito, saurin ɓoye fuskata nai a ƙirjinsa ina share ƙwallah ganin yana ƙoƙarin sumbatar wuyana dan ko da wasa bana ƙaunar wani abu makamancin hakan ya shiga tsakanin mu dashi saboda har yanzu ina jin zafin abinda yayi min a baya, hannunsa ya kai a bayana yana shafawa nai saurin turesa na tsugunna a wajen na fashe da kuka, motsi naji a bayan mu hakan yasa na miƙe tsaye na raɓa ta gefensa na shige na kulle ɗakin na haye saman bet ina sauke ajiyar zuciya tamkar wacce tayi gudun tsere, Abdull ya jima tsaye a ƙofar ɗakin yana kallo bayan Nu'aiymah ta shige, ji yake tamkar ya ɓalla ƙofar ya shiga ya gaya mata gaskiya ko zata rage haushinsa da take. ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ya fara a hankali yana kiran sunan, wani mugun tsaki naja na sake gyara kwanciyata na juyawa ƙofar baya, Abdull ya kwashe kusan 15 minutes yana abu ɗaya, ganin bbu sarki sai Allah yasa ya baro ƙofar ɗakin ya sauko ƙasa zuciyar sa ba ɗaɗi, Mami kawai ya samu da mai aikinta a falon tana buɗe kayan miyar da Hadiza ta siyo, sai da ya sosa ƙeya sannan yace "ni zan wuce Mami" Mami tace "Awn baka tafi ba kenan" yace "eh yanzu zan tafi" Mami tayi murmushi tace "to tsaya a zuba maka abinci mana" "no a ƙoshe nake sai da safe" "Allah ya kaimu" ta faɗi tana miƙewa tsaye, direct ɗakin Nu'aiymah ta wuce ta fara nocking, jin taƙi buɗe ɗakin Mami tace "ki taso ki buɗe nice"