part 33-34

180 9 2
                                    

*ONE BLOOD*

_33-34_ ✍🏼

Mami na Falo taji dannawar bell, da ido ta yiwa Hadiza alama da taje ta buɗe tacigaba da aikinta, bayan kamar minti uku Hadiza ta dawo tace "yace ace Acp ne" Mami tayi tsai tana tunani can kuma tace "ce masa ya shigo sannan ki kawo masa abin sha ina zuwa" daga haka ta miƙe ta tattare kayanta ta wuce ɗakinta, ba jimawa ta dawo sanye da dogon hijab har ƙasa, zaune ta samesa yana danna waya ga drinks nan da Hadiza ta kawo masa bai taɓa ko ɗaya ba. a mutunce suka gaisa da Mami bayan ya mata jaje ya ɗora da faɗin "docter nazo muyi wata ƴar mgn ce da ke! Allah yasa zaki bamu haɗin kai" Mami tayi ɗan murmushin da yafi kuka ciwo tace "ina jinka" Acp ya gyara zamansa sosai yace "a binciken da muka fara jiya zuwa yau mun gano cewa ke kika kai Larai mai aiki gidan yarinyar ki da ta ɓata, gashi kuma yarinyar ta gudu kuma na tabbata bazaki rasa sanin inda ta fito ko kuma wani nata ba, muna buƙatar yarinyar cikin gaggawa" Mami tace "nayi tunanin yarinyar ta gudo ne sbd al'amarin nan da ya faru ne, eh nasan yarinyar dan nima yayarta take min aiki, in zaka jira ma zan tura driver yaje ya ɗauko ta yanzu" "a'a yanzu ina kan hanya but wajen ƙarfe biyar na yamma haka zaki iya tura min ita a can station" Mami tace "to shikenan! mun gode sosai" daga haka yayi mata sallama ya tafi. tun kafin yamma tayi Mami ta tura driver da Hadiza suka ce ɗauko ta, Mami da kanta ta kaita bayan tayi mata dogon gargaɗi akan ta faɗi duk abinda ta sani tsakanin ta da Allah banda ɓoye-ɓoye kar kuma ta damu kanta da barazanar Zuhra dan burga ce kawai bbu abinda ta isa ta mata, da haka Larai ta saki jiki sosai ta faɗa ma acp duk abinda taga da kuma abinda taji harda barazanar da Zuhra ta mata da irin korar karen da ta mata, kuka sosai Mami tayi acp kamal ya fara bata haƙuri, a haka Baffah da Baba shagari sai uncle Malik da Mum Farida sai Umma da Inna suka shigo offise ɗin, bayan gaisuwa da akayi bbu wanda yace da Mami uffan akan abinda ta aikata dan basa cikin nutsuwar da zasuyi wannan maganar sai bayan komai ya lafa tukun, zamansu da minti goma sai ga wasu ƴan sanda mata biyu nan sun fito da Zuhra da tayi wujiga-wujiga duk tayi laushi tamkar ba ita ba, yasa aka zaunar da ita ɗan nesa dasu sannan ya nuna Larai yace mata "kinsan wannan"? ta ɗago ta kalleta ta girgiza kai alamun bata santa ba, Acp Kamal ya dubi Larai yace "ke kin santa"? tace "eh ni tsohuwar mai aikin kishiyar ta ce" yace "ok bamu lbrn abinda ya faru tsakanin ku" ta ƙara maimaita abinda ta faɗa ɗazu gaban su Baffah kuma gaban inda kanta, ta wani sunkuyar da kai kowa na ɗakin ya fara binta da kallon mamaki, ƙaramar yarinya irin haka ta iya aikata wannan ɗanyan aiki? Qaseem dake tsaye ƙofar offise ɗin ya faki idon mutanen ɗakin, tsalle ɗaya yayi ya cakumo wuyanta ya damƙata ga bangon ɗakin yana wani irin huci, idanunta sunyi wata irin kakkafewa ta azaba ta fara kakarin amai amma yaƙi sakinta sai ƙoƙorin aikata lahira yake, Mami ce ta farga da aika-aikar da yake shirin yi ta saki salati hakan ya ankarar dasu suma, Uncle Malik yayi saurin kamo sa ta baya, ya fara fixge-fixge da faɗin "ku sakeni sai na kashe ta, sai na tura ta inda ta tura Nu'aiymah" da ƙyar ya zaunar dashi ya fara masa mgn cikin kwantar da hankali da tausasa harshe "haba kai kuwa Qaseem ba girman ka bane ka tsaya dukan mace sai kace ba namiji ba? ka ƙƴaleta kowa yayi na gari ai dan kansa" da haka ya lallaɓasa har ya haƙura ya dawo wajen zaman sa ya zauna, bayan hayaniyar ta ɗan tsakaita Acp ya kalli Zuhra da ta durƙushe a wajen tana kuka, tsawa ya daka mata sannan yace "da zaki taimaki kanki da kin faɗi gaskiya mun sake ki, but tunda kika nuna taurin kai zan nuna maki na fiki dan yanzu kotu zan turaku amma sai kinyi laushi tukun" cikin ƙaraji Zuhra tace "nace maka bansan komai ba sharri sukai min amma kaƙi yarda tou ya kakeson nayi so kake na karɓi laifin da ba nawa ba"? ya saki murmushin mugunta ya umarci matan da su mayar da ita a cell tunda taurin kai ya hanata faɗan gaskiya, ya kalli su Baffah yace "inason mubi komai a sannnu, ina mai tabbatar muku da cewar zamu cigaba da azabtar da ita yadda ya kamata har sai ta faɗi gaskiya da kanta sannan mu turaku kotu dan ƙwatar haƙƙin wanda aka zalunta da ma ku kanku ahalinta" su Baffah su kai masa godiya suka fito cike da ƙwarin guiwa kowa ya shiga motarsa ya kama gabansa, Mum Farida ta shiga motar Mami tace suje can gidan nata akwai maganar da zasuyi, murmushi kawai Mami tai ta tada motar suka bar station ɗin.

ONE BLOODWhere stories live. Discover now