*ONE BLOOD*
*SHAFI NA 49-50*
girgiza kai Mami tayi ta koma ciki cikin tsantsar mamakin Nu'aiymah da Abdull ganin suna neman maidata ƙaramar yarinya, but bbu komai zata bisu a yadda sukeso taga iya gudun ruwansu. ina zaune a falon bayan na gama sallar isha har Mami ta sakko ta sameni riƙe da laptop da takardu a hannunta, kasa ɗagowa nai na kalleta sbd wata massifaffiyar kunyarta da ta dabaibayeni, Mami na lura da ita amma ta ɗauke kai tacigaba da operating ɗin Laptop ɗinta, na gaisheta ta amsa min a taƙaice ba tare data kalleni ba, sun ɗau tsawon lkc a haka kafin Aliyu yayi sallama ya shigo, ya gaishe da Mami ta amsa cike da fara'a ya ƙaraso ya zauna nima na gaisheshi, a haka muka fara ƴar fira sama-sama Mami na tambayarsa ya aiki, tun bai ƙaraso cikin falon ƙamshin turarensa ya daki hancina, gabana yayi wata irin faɗuwa sa'ilin da naji ya turo ƙofar falon sallama ɗauke a fatar bakinsa, wata dakakkiyar shadda ruwan zuma ce a jikinsa data sha ɗinkin surfani wacce tayi bala'in yi masa ƙyau ta fito da tsantsar kyawunsa da cikar haibarsa, gaishe su yayi duk suka amsa ya samu wuri ya zauna yace "Mami Baba ne yace inzo ki dubani" ya ƙarashe maganar yana murmushi, "bangane in dubaka ba"? tayi tambayar tana binsa da kallon mamaki, ya shafa kansa yana murmushi yace "banjin daɗin jikina ne" Mami tace "dole kayi rashin lafiya ai" ta ƙarasa faɗa tana murtuke fuska, duk muka ɗago muka dubeta, nidai na tashi nabar falon gabaɗaya sbd wata massifaffiyar kunyar data ƙara rufeni, Mami tabi bayan Aiymah da kallo taja tsaki nan ma kallonta Aliyu da Abdull su ka yi, Abdull ya sosa ƙeya yayi mata sallama ya fita dan zuwa yanzu ya fahimci Mami ta gano su. cikin ɗaga murya Salima tace "a'a Mumcy ki daina bani haƙuri wlh sai na wulaƙanta kaff dangin nasa na ɗau fansa, zaman gidan Abdull ai yanzu na soma ki rabu dani tunda bakya kishina bakya ƙaunata taya ma zakice min in haƙura da Abdull"? rai a ɓace Mumcy tace "ni kike gayawa haka Salamatu? kin manta ni mahaifiyarki ce da zaki gaya min mgn haka bbu tausa harshe"? a fusace Salima tace "tou ya kikeson ince dake ba ke kika janyo komai ba? ina amfanin uwar da bata tausayin ƴarta? nace ki ƙƴaleni ki rabu dani dama ai ba sona kike ƙwaɗayin abun hannuna kike yanzu da kikaga na daina fita neman na kaina dole ki ce min haka" "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" shine abinda Mumcy ta faɗa hawaye share a fuskarta tana jin wani jiri na neman ɗibarta, tayi baya-baya tana hawaye hannunta na dama dafe da saitin zuciyarta dake wani irin bugawa sannan ta soma mgn cikin kuka sosai "yanzu Salamatu ni kike gayawa irin wannan maganar sai kace bani na haifeki ba? anya zakiga daidai a rayuwar ki kuw? karki manta ni na ɗauki cikinki wata tara naci kashin ki naci fitsarinki yanzu dan ɗibar Albarka ki tsaya a gabana kina min rashin kunya"? Salima ta ɗauke kai tana taɓe baki tace "kar Allah yasa inga daidan Mtss" cikin wani firgitaccen kuka Mumcy tace "Salima nasan kece ajalina! baƙincikin ki shine zai kashe ni, kasheni zakiyi ki huta Innalillahi wa'inna ilai..." bata ƙarasa faɗa ba ta tari yaci ƙarfinta ta zube a wurin tana wani irin tari mai ban tsoro jini na fita ta hanci da bakinta. hankali tashe tayi ɗaki da gudu ta ɗauko waya ta fara kiran Abbansu, tayi masa mss calls kusan goma amma bbu answer, tasan yanzu yana can gun amaryarsa bashida lkcn su, ta wurgar da wayar tayi hanyar waje da gudu tana kiran driver, da taimakon driver suka sanya Mumcy a mota suka nufi assibiti da ita still jini bai daina fita ta hanci da bakinta ba!. ina fita falon na ƙarasa kusa da wasu Furanni nayi zamana ina tunanin abin duniya, minti biyar da zamana naga ya fito, na ɗauke kai nai tamkar ban gansa ba, Abdull ya ƙaraso wajen da take ya tsugunna a gabanta ya kamo hannun tana shirin fizgewa ya riƙe gam, kallona yake ido cikin ido nai saurin ɗauke kaina dan kallon tsakiyar idonsa na sakani cikin wani yanayi, hakanan kuma da zarar jikina da nasa sun haɗu sai na kasa taɓuka komai ko inason masa rashin kunya sai naji na kasa sai in baya kusana kamar wani mai siddabaru, sunana da ya kira ne ya dawo dani hayyacina, Abdull ya miƙe daga tsugunnan da yake ya zauna gefenta har suna gugar juna still hannayensu sarƙe cikin na juna, Slowly yake murza tafin hannunta cikin nashi, ta lumshe ido hawaye na rigen-rigen zubo mata tace "ka sakarmin hannu dan Allah" ya girgiza kai rai a ɓace yace "meyasa kikeson wahalar da zuciyar ki da tawa? Look at me Nu'aiymah ki daina wani ɓoye-ɓoye nasan kina sona kamar yadda nima sonki da ƙaunarki yayi min mugun kamu tun bakida wayo kuma tun bakisan kanki ba, dashi na rayu bansan muhimmancinki sai da kikayi nesa dani na gano cewa bazan iya rayuwa in bbu ke, ina massifar so da ƙaunarki Aiymah dan girman Allah kiyi haƙuri ki manta duk abinda ya faru a baya ki dawo mu rayu tare karki bari Babyn mu yayi kuka maraici dan Allah" kuka sosai yaga ta fashe dashi ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana cigaba da rera kuka, few minutes yaga ta sake ɗagowa tana share hawaye ta miƙe tsaye tana girgiza masa kai "Allah ma muna masa laifi yana yafe mana balle mu bayinsa, na yafe maka ya Abdull Allah shi yafe mana baki ɗaya but inason ka cire batun zan koma gidanka a ranka dan abu ne da bazai taɓa yiwa ba!" with shock ya miƙe tsaye yana binta da kallon mamaki, then ya haɗiye abu mai ɗaci yace "zan iya sanin dalili"? ta ɗaga kafaɗa itama tace "sbd baka sona kuma baka tausayina, kai azzalumi ne Abdull baka yadda da ƙaddara ka riƙeni da amana ba, koba so ai akwai zumuncin iyayenmu bai kamata ka wulaƙantani a gaban matanka ba, kullum cikin cin zalina kake karka manta har akuya ka kirani dashi, tunkiya, jaka babu wanda baka kirani dasu, taya kake tunanin zan manta waƴan nan abubuwan?? nima fa inada zuciya a ƙirjina, so na haɗaka da Allah ka fita a rayuwata ko zan samu salama ko nima zanyi farincikin dana rasa a baya a rayuwata, da zaran na haihu zan damƙa maka ɗanka ni kuma ka damƙamin takardata Allah ya haɗa kowa da rabonsa, and pls and pls inason ni da kai muyi respecting ɗin juna karkasa sauran mutuncinka da ya rage a idota ya ƙara zubewa..." tana kaiwa nan ta juya tacigaba da tafiya, wani irin zafi ƙirjinsa ya farayi masa tuni ya fara ganin dishi-dishi, wani ƙatoton abu da ya turniƙe masa maƙogoro da ƙƴar, yasan ta fisa gaskiya sai yanzu tarin danasani da nadama marar amfani ta rufesa, da ƙƴar ya iya buɗa baki yace "naji na amince kuma In shaa Allah! ni Abdull Malik Yusif Shagari zan fita a harkar ki, zanyi nesa da duniyarki, Allah ya haɗa kowa da rabonsa" yana kaiwa nan ya juya yabar wurin cikin wani irin yanayi wanda ni Nu'aiymah bansan yadda Alƙalamina zai rubuta muku shi, Nu'aiymah tabi bayan gawurtaccen mijin nata wanda takun tafiyarsa ma abun kallo ne ta fashe da kuka tace "kayi haƙuri ya Abdull bazan iya komawa gareka dan bbu burbuɗin sona a zuciyarka, bani kakeso jiki na kakeso sha'awata kawai kake, ni na yarda da zanen ƙaddarata kuma zan karɓeta a duk yadda tazo min, kayi haƙuri abar maganar banason zumuncin mu ya lalace Allah ya haɗa kowa da rabonsa" ina kaiwa nan na shige part ɗin Inna da gudu ina wani irin kuka mai ɗaga hankali, tunda ta fara mgn shi bai jiyo ba kuma ya kasa cigaba da tafiya, ya tsaya kamar wani gunki yana sauraron lafazin ta yana ƙoƙarin yin fashin baƙi a kansu. a gaggauce likitocin suka karɓi Mumcy urgence, Salima da ƙanwarta suka rungume junansu suna kuka, Doctors ɗin nata basu haƙuri, da ƙƴar suka shawo kan matsalar su ka yi mata allurar bacci bayan an gama saka mata drip, special room suka kaita dan ta huta aka umarci su Salima su fito ɗakin dan batason hayaniya, a haka Dad da Amaryarsa Jamila sukazo asibitin suka samesu, cike da tausayinsu Haj Jamila take tambayarsu jikin mahaifiyarsu, Humaira ce kaɗai ta amsa da kulawa Salima kam sai ma wani matsiyacin kallo da ta watsa mata tana jan tsaki, bbu wanda ya tanka mata dan basuda wani sukuni a yanxu, da ƙyar Dad ya shawo kan Doctor ya barsu su shiga suga suga Mumcy amma da sharaɗin kar suyi surutu, gabaɗayansu suka shigo kowannensu ya samu wuri ya zauna, Dad ya ƙarasa gaban gadon yana kallon matar tasa cike da tausayi, ya jima yana guje mata irin wannan ranar da Salima zata sakata kuka, ta ɗauki son duniya ta ɗora mata da zaran yayi mgn ta hayayyaƙo masa a ƙarshe dai tazo ta zama sangartacciya tafi ƙarfinsu gwara ma shi yana cin ubanta, gabaɗaya bata ganinsu da gashin ido yanzu gashi nan tun ba'aje ko'ina ba ta fara sakata kuka, Humaira ce kaɗai batayo halin uwar tasu da yayarta shisa yake bala'in ƙaunar yarinyar, cike da takaici ya samu wuri ya zauna shima. mintuna goma da zaman Dad Mumcy ta farka tana ihu da shure-shure, gabaɗaya suka yo kanta cikin tsananin tashin hankali, Salima ce ta fita da gudu dan kirayo Dr, tana fita Mumcy ta riƙo hannun Dad hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, da ƙƴar ta fizgo maganganun a bakinta tana jan lumfashi "ka gafarceni Alhj! ni tawa ta ƙare don Allah Alhji ka taimaka ka yafe min duk abinda nai maka, nasan ni mai laifi ce kuma ba lallai ka yafemin ba dan ban cancanci hakan daga gareka, dan Allah ka yafe min mutuwa zanyi tawa tazo ƙarshe, sai yanzu na fara kirban abinda kake gaya min akan Salima, kayi haƙuri ka yafe...." Dad yayi saurin tarin numfashinta yace "na yafe miki, Allah shi yafe mana baki ɗaya kuma In shaa Allahu baza ki mutu ba Allah ya tashi kafaɗun ki" Mumcy tayi wani murmushi mai ƙayatarwa tace "a'a ni tawa tazo ƙarshe, ga mutuwata nan a gabana ina gani, nidai addu'arku kawai nake buƙata" kuka sosai Humaira da Haj Jamila suke, Mumcy tace "Humaira kizo ga hannuna mu gana, Jamila kema ki gafarceni, ga kuma Humaira na bar miki amana karki bari rayuwata ta lalace banason su taru su zama ɗaya da Salima, ki riƙemin ita amana don Allah" Humaira ta rungume Mumcy tana wani firgitaccen kuka tana faɗin bazata mutu ba, Dad ya kawar da kansa yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa cike da tausayin Humaira, tari ne yaci ƙarfin Mumcy ta farayi ba ƙaƙƙautawa daga bisani tayi baya ta kwantar da kanta saman pillow, jin jikinta ya saki Humaira ta saki wata razananniyar ƙara ta zube a wurin sumammiya, hakan yayi daidai da shigowar Dr da Salima Dad kuma na ƙoƙarin fita daga ɗakin yana share ƙwallah, tun a lkcn Dr ya fahimci abinda ya faru hakama Salima, tayi zaman ƴan bori a wajen ta kasa taɓuka komai tana zare idanu, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kulli nafsin za'ikatul! mauti, mutuwa mai yankan ƙauna, Allah yayiwa Mumcy cikawa😭ya Allah mu da muka rage Allah kai mana kyakkyawan ƙarshe kasa muyi mutuwar shahada, jama'a mutuwa mai yankan ƙauna, Mutuwa! mai raba ƴa da uwa ya raba uba da ɗa ya da ƙanwa, Mutuwa rigar kowa ko wane bawa sai ya ɗanɗana zafin mutuwa da raɗaɗinsa😭👌🏼Manzon Allah s.a.w ma ya mutu yabar gidan duniya bare mu, ya Allah ka cire mana son duniya da ƙƴaleƙƴalen cikinta, ka ɗoramu akan tafarkin dai-dai ka zama gatanmu ya Rabb! kacigaba da tunasar damu da kwanciyar kabari, ya ubangijin talikai kar daɗin duniya yasa mu manta da lahirarmu da kuma kwanciyar kabarin dake jiranmu, jama'a akwai fa babban aiki a gabanmu, idan na tuna kwanciyar kabari da azabar kabari da kuma makomarmu sai inji hankalina ya tashi, ya rabbi ka hanamu aikata saɓa maka ka yafe mana kurakuran mu kasa mu gama da duniyar nan lafiya ka jiƙan iyayenmu da kakanin, mala'ikunka na rahama ya rahamce su in tamu tazo Rabb! kasa muyi mutuwar shahada, a rayuwa anya akwai mutuwar da tafi zafi irin ta uwa? sannan ta uba ga ta miji nidai a tawa ƴar fahimtar😥to ya take ga wanda uwarsa ta mutu tana fushi dashi? Yah Subhanallah! Allah ka rabamu da iyayenmu lfy ka bamu ikon faranta musu duniya da lahira😭wannan page ɗin ni kaina ina typing ina share hawaye da tissue, ina bala'in son uwata fiye da tawa rayuwar, Allah ka bamu ikon farantawa iyayenmu duniya da lahira, Zanyi farinciki sosai idan kikai comment ki nunamin yadda kika kasance a wannan shafin ta hakan ne zan fahimci darasin da kuka ɗauka a shafin nan.
22793414725 wattsap no