*ONE BLOOD*
*59-60*
#The End
"Mami dan Allah kiyi hƙr wllh ban taɓa tunanin zanyi abinda zai ɓata miki rai, wllh tllh na amince zanyi duk yadda kike so kuma zan basa haƙuri amma kafin nan dan Allah ki daina wannan fushin da kike dani please" "naji tashi kije" yadda tayi mgnr ne yasa jikina yin sanyi, na miƙe tsaye ina jan ƙafafu na bar ɗakin jiki bbu ƙwari. A hankali nake sakkowa daga stairs zuwa sitting room ɗinmu, hijab ne har ƙasa a jikina na ƙaraso cikin falon da ya cika da sanyi Ac. ƙamshin turaren da ya gauraye kowane angle ɗin falon yasa ya ɗago muka haɗa ido nai saurin sunkuyar da kai na zauna saman kujera, cikin sanyi murya nace "good evening" ya ɗan kalleni sannan ya ɗauke kai yanawa Papi wasa dake ta dariya tun ɗazu shi kuma ya biye masa suna wasan, then harna fidda rai da samun amsa naji yace "Evening Haw Are U"? "Alhmdllh" na faɗa ina wasa da yatsun hannuna, na miƙe zan shiga kitchen ya dakatar dani da faɗin "no don't bring Anything I'm Okay! sit dawn" ba musu na dawo na zauna saman kujerar dake facing nasa, a fakaice yake kallonta daga sama har ƙasa, banda glowing ɗin ƙamshi bbu abinda take amma ta rame sosai ba kamar kwanaki da tayi ƙiba, gyara zamansa yayi suna fuskantar juna yace "kince za mu yi mgn oya ina sauraren ki" da ƙyar na tattaro sauran ƴar nutsuwa da jarumtar da ta rage min nace "bbu batun wani ɓoye-ɓoye na kiraka ne daman akan matsalarmu wacce har take ƙoƙarin shafar zumincin iyayan mu, amma akwai sharaɗi" tsaya rubuta muku irin tsananin farincikin da ya riski kanshi a time ɗin zamu ɓata lkc sosai, sai dai sam bai nuna hakan a fuskarshi, ƙayataccen murmushi kawai ya sakar mata yace "Okay! tel me Now you list Them abinda kikeso da wanda bakya so gudun shiga haƙƙin juna" na gyara zama sosai cike da ƙoƙarin yakice duk wata fargaba a raina. "da farko dai na riga na rantse da cewar wllh wllh na gama rayuwar ƙasƙanci da rashin kulawa da rashin girmama juna a gidanka tamkar irin wacce mu ka yi a baya, aure ya wuce gaban wasa da zamu tsaya muna wasa dashi kamar wasu shashashu ko ƙananan yaran da basu san me suke ba! inason ka rubuta ka ajiye a wannan karon zanyi zaman aure ne irin wacce ko wace mace takeyi a gidan mijinta duk da dai bawai ina sonka bane aa auren biyayya zanyi da kuma Albarkacin ɗanmu dake mugun bani tausayi dan bazanso ya tashi a ukubar kishiyar uwa, ni kaina da nake uwarsa nasha azaba a hannun kishiya nasan illar dake tattare da kishiya kaima shaida ne, banason harka ta rashin kamun kai ko rashin girmama juna dani da kai inason kowanne yasan matsayin ɗan uwansa sannan muyi respecting ɗin juna, abu na gaba kuma dole ka barni naci gaba da karatuna sbd tun farkon aurenmu munyi wannan yarjejeniyar da kai, shikenan kawai saura naka sharaɗin" kalmar 'duk da dai bana sonka zanyi biyayya ne kawai' ta mugun masa zafi kuma ta dakesa kuma yayi Alƙawarin sai tayi dana sanin furta ta da tayi, da yake namijin duniya ne shi ko a fuska mai nuna mata ba, hasalima wasa yakewa ɗansa har ta kai ƙarshen aya a zancenta ya ɗago yace "ni banida wasu sharaɗai, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya kau da sharri" daga haka yayi gum da bakinsa ya ciro wayarsa ya fara yima Papi pictures yana murmushi, nidai ina zaune a falon amma tamkar bananan sai jefi-jefi nake satar kallonsu, bayan wani ɗan lkc falon yayi tsit hatta hayaniyar Papi ba aji alamun yayi bacci, Abdull ya ɗago yana kallonta ganin ta ƙurawa lallausan carpet ɗin ido alamun tayi nisa a tunani, gyaran murya yayi yace "taso ki karɓesa kije ki kwantar yayi bacci, sannan ki sameni a mota ki karɓi kayan wasan da na siya masa ki dawo ni zan wuce" a hankali take taka lallausan carpet ɗin tamkar wata marar laka har ta ƙarasa gabansa ta sunkuya zata karɓesa, fuskokinsu suka haɗe dana juna yayi saurin miƙa mata shi yana ɗan basarwa, yayi mata sallama bayan yace ta fito ta karɓi kayan da ya siyawa Papi. bayan kwana biyu da faruwar haka muna zaune a ɗakin Mami ina linke kayan wankin ta, tana aiki a laptop mu biyu ne kawai a ɗakin, ta juyo gareni tace "anjima kije Baffan ki na son mgn dake" "to" na bata amsa naci gaba da abinda nake, bayan Isha naje kiran Baffah, zaune na samesa shi kaɗai na gaishesa bayan ya amsa gaisuwata yayi gyaran murya yace "Abdull ya sameni da zancen kin amince zaki koma gidanki, Allah yayi maki Albarka ya faranta maki yadda kika faranta mana,kiran da nasa Maminki tayi min kenan tashi kije sannan ki kasance cikin shiri In sha Allah son zaki koma duk dai bai faɗi rana ba" jiki a sanyaye nai masa sallama na koma part ɗinmu, sai da na sanar da Mami yadda mu ka yi da Baffah sannan na koma ɗakina dan yin wanka. a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah yau sati ɗaya kenan amma har yanzu bbu wanda ya faɗa mata takamaiman ranar tariya ba, Mum Farida dai ta duƙufa wajen gyara ƴarta da ingantattun magunguna masu kyau da na sha, mai gyaran jiki ta ɗakko wacce take mata tsumi da gyaran jiki kai kace sabuwar amarya, gabaɗaya ta canja tayi wani irin fresh sai wani sheƙi da glowing ɗin ƙamshi take kamar wata amarya, amma ta rame sosai fiye da kwanaki sbd tunanin da ya addabeta na sabon rayuwar da zata fuskanta duk da dai ba baƙonta bane amma gabaɗaya idan ta tuna irin zaman da tayi a gidansa a baya sai taji ta sare gabanta ya dinga faɗuwa kenan, yau ma kamar kullum ina zaune a ɗaki fitowata kenan daga wanka Towel ne kawai ɗaure a jikina, nayi nisa sosai cikin tunani abun duniya ya isheni, Mum Farida ta shigo ɗakin da sallama, firgigit na amsa mata da ƴar yaƙe a fuskata,ta ƙaraso ta zauna riƙe da cup a hannunta,dafa ni tayi tace "kin gama ashe kika ƙi fitowa mai ƙunshi tana can ɓangarena tana ta jiranki kin zauna anan kina shiririta" ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi nace "sorry Anty I'm coming Now In sha Allah" ta ƙara dafa cike da kwantar min da hankali "keep praying daugther! nima zan tayaki In sha Allahu lfy lau zaku zauna, ki karɓa ki shanye ki bani kofin sannan ki tabbatar kinci abinda na bada a kawo maki ɗazu kafin ki fito" kai kawai na gyaɗa mata ta karɓa na shanye tass na bata kofin, tana fita na tayar da sallar Azhar, na jima zaune kan sallayar ina addu'oi sannan na miƙe na linke hijabin na zauna ƙasan carpet na jayo plate ɗin naman Mum ta aiko Hadiza da shi, cinya ɗaya na iya ci da ƙyar shima sai kakarin amai nake ganin haka na tsiyayo fresh milk a cup nasha hakan ne ya hana aman tahowa, na rufe naman zan tura ƙarƙashin gado kenan Mami ta turo ƙofar ganin naƙi fitowa har yanzu, kallo ɗaya tayi min ta juya ta bar ɗakin ba tare da tace min ƙala ba, hijab na saka cike da kunyar ganin taga abinda nake ƙoƙarin aikatawa, har part ɗin Mum naje na samu mai lalle na zauna ta fara tsantsara min jan lallai wadda ta fito raɗau a farar fata ta, sai daf da magriba muka gama, bayan na wanke sai ya ƙara wani mugun kyau da sheƙi a saman farar fatata, can ɓangaran Mum nayi sallar Isha muka ci abinci da Leila dake ta tsokanata, sanda na fito zan koma ɓangaren Mami Mum Fareeda ta kirani zuwa ɗakinta. press ɗin kayanta ta buɗe ta jayo wata ƙatuwar Troley ta ƙarasa bakin gado ta buɗe, ɗinkuna atamfofi da lace da shaddodi sunfi kala talatin duk an ɗinka su, ni dai kallonta kawai take har ta gama jera su tsaf tace "gasu nan jiya tela ya kawo su anjima zan tura Qaseem ya kai can ɓangaren Mamin ki da sauran kayan ki" na amsa da tou sannan nai mata sai da safe na wuce. misalin ƙarfe tara nayi shirin kwanciya bacci amma baccin yaƙi ɗaukata, nayi zurfi sosai cikin tunani naji ƙarar wayata, jiki a mace na janyo wayar ina kallon baƙuwar numbar dake yawo kan sreen ɗin wayar, na jima ina kallon numbar da ƙyar nayi picking ina yin sallama,sautin murmushinsa kaɗai na jiyo na gane ko waye, na gyara zamana a daidai sanda yake amsa sallamata tare da faɗin "sorry na tashe ki kina bacci" sai da na lumshe idanu na buɗe sannan nace "Aa ban kwanta ba tukkun" "me kike har yanzu" "karatu" na basa amsa a taƙaice, "Owk Allah yayi kyakkyawan jagoranci ko nazo na tayaki ne"? Ajiyar zuciya na ƙara saukewa nace "ai na gama yanzu zan kwanta dare yayi" yace "Okay! tou sai da safe ki shafamin kan Baby na" na ɗan taɓe baki nace "In sha Allah! uhm dan Allah ina son maka wata tambaya" ya gyara kwanciyarsa yana sakin wani ƙasaitaccen murmushi yace "ina jinki" shiru nai na lumshe idanu gabana na faɗuwa dan bansan yadda zan masa tambayar ba, then dai na cire tsoro nace "wai da gaske aure za ka yi"? dariya ta bashi sosai amma ya gumtse ta yace mata "uhm ya akayi ko kina da matsala da hakan ne"? na rumtse idanu zuciyata na min zafi nace "Aa ko ɗaya daga tambaya"? yace "sai amsa" nai shiru na kasa motsi tamkar wacce aka dasa then nai ƙarfin halin faɗin "amma ba a gida ɗaya zamu zauna kou"? yace "Eh ke zaki zauna a sabon gidana ita kuma zata zauna acan tsohon gidana da nake kan gyaransa" cikin rawar murya nace "Ok Allah ya taimaka, ni zan kwanta sai da safe" ƙitt na kashe wayar na zame na kwanta na rufe kaina da duvet ina danne kukan dake ƙoƙarin taho min, murmushi yayi yana shafa kansa ɓangare ɗaya na zuciyarsa na tausayinta dan ya fahimci Nu'aiyma irin matan nan ne da sam basa iya ɓoye kishin su, zuwa ynzu tsaf ya fahimci ta fara sonsa ƙarfin hali irin nata ne kawai, shi kuwa me zai kaisa ga ƙara aure muddun ta karɓesa hannu biyu tana basa kulawar da ta dace, a daren ranar shima da ƙyar bacci ya ɗaukesa. washe gari misalin ƙarfe tara na gama shiri na ina jiran shigowar Leila, ina sanye cikin riga da zani na atamfa nayi ɗaura ɗankwali daidai misali ina zaune ina shayar da Papi ta shigo tana ƙwalamin ƙira tana faɗin "dan Allah kiyi sauri ko nai tafiya ta" ko kallon inda take banyi ba har ta gaji da tsaiwa ta ƙaraso ɗakin tana karkaɗa key ɗin hannunta tana wani ɓata rai, ni dai ban kulata ba balle muyi abinda muka saba, sai da na tabbatar yarona yayi bacci na kwantar dashi muka yiwa Mami sallama muka fito, a compound muka haɗu ya fito shirinsa na fita Offise yana ƙoƙarin ɗaura agogon hannunsa, cike da rawar kai Leyla ta ƙarasa wajensa tana washe haƙora, ni dai na fizgi key ɗin hannunta na ƙarasa na buɗe motar na shiga na rufe ƙofar, kusan 15 minutes suna tsaye sai murmushi suke ni dai na taɓe baki gamida ɗauke kaina, then naga ya nufi motarsa ya buɗe ya shiga sai gashi itama ta nufo motar mu tana murmushi, tana shiga ta kwashe da dariya tace "shashasha maimakon ki tsaya ku gaisa ki tatsi abinda kika tatsa kinsan ynzu da zaki koma gidansa a yadda naga yana rawar kan nan ko Hjy kika ce ya baki zai baki amma kin tsaya kina shashanci ni dai na samu rabona wllh dubu hamsin ya bani yace inyi na credit" cike da rainin hankali nace "Awn Allah ya saka da Alkhairi ai zai ishe mu dukkan mu gashi kuma ina da kuɗi a jakata" a kaikaice ta kalleni tace "eh mana da yake sallamammiya ce ni" mu ka kwashe da dariya sannan ta yiwa motar key muka baro harabar gidan, wani saloon dake nan kusa damu muka je, mun ɗan tarar da layi shisa muka jira har layi yazo kanmu, gyaran gashi aka mana, Leyla ta nace akan dan Allah na bari ayi min kitso nace bana so, ganin yadda muke ta gardama kamar ƙananun yara matar da dubeni tace "wllh da gaskiyar ta, 2days bakiyi kitso ba da zaki amince wannan karon ayi miki kawai ko dan gudun lalacewar wannan dogon gashin naki, kinga mun kawo wasu styles masu kyau muje ciki in nuna maki ki zaɓi kalar wanda kike so yau da kaina zan maki" na ɗan sosa kai ina ɓata rai nace "ni fa kitson ne bana so amma muje kawai" nan ta shigar damu wani ɗaki Leila ta zaɓi kalar style ɗin da za'a min muka fara kitson muna ƴar taɓa fira, har wasu mata biyu da suma kitson suka zo yi suka shigo suka same mu, a kallo ɗaya zaka musu ka fahimci cikakkun ƴan duniya ne wanda suka jima ana damawa dasu a harkar bariki, da yake customs ɗin Mdm Rebecca ne sai ta tsaya suna gaisawa dasu cikin kulawa harda tambayarsu ina ƙawarsu ta kwana biyu bata zo wankin kai ba, a fusace ɗayar da tunda suka shigo take ta faman girgiza ƙafa ta dakatar da ita da faɗin "dan Allah ki daina kawo mana zancen Salima muddun ba so kike mu ɓata dake ba, ni karan kaina neman ta nake ruwa a jallo dan nayi Alwashin ɗaukar fansa a kanta, bata gama sanin halina bane shisa taci amana, wllh tllh ni ƴar daɓas duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, bazan taɓa ragama Salima ba muddun muka haɗu, daman can bariki ce ta haɗamu ba dangin iya bare da baba, yanzu kuwa ta ɓata rawarta da zallanta dan ina nan ina bibiyar rayuwarta har sai burina ya cika a kanta." Mdm Rebecca tace "ikon Allah ƴar daɓas ke kuwa meya haɗaki da ƴar ƙawarki ne har haka"? tayi tambayar cikin gurɓatacciyar hausarta, mu dai mun zama ƴan kallo sai kallon ikon Allah muke dan ni tsoro ma suka bani, ɗayar da batayi mgn tun shigowar ba ne tayi shewa tana faɗin "bariki alalan gero in baka iya wataran ta kwaɓe ma" ta faɗa suna tafawa da ƴar daɓas dake ta ɓaɓɓaka dariya tace "nan da kike ganina wllh duk iskancina ina tsoron ɓata ran iyayena, iyayena basu taɓa ɗaga baki sun jefeni da kalmar alkaba'i kullum fatan shiriya suke min, ita kuwa Salima na farko bakin iyaye na ɗawainiya da ita, sam bata san darajar iyayenta ba, ke in taƙaice miki zance ita ce ta kashe uwar da siyar da gidan ubanta ta gudu yawan bariki, kuma tun farkon haɗuwarmu na samu wani lbr wai mijin da ta aura kwanaki ashe amanar babbar ƙawata Zuhra taci tayi luf-luf ta aure mata miji bayan ta fitar da ita Zuhran daga gidan shi Abdoul ɗin" gabana ne yayi wata irin razananniyar faɗuwa daga ni har Leila dan duk mun fahimci da wa suke, duk yadda na kai ga ɓoye tashin hankali abun ya gagara shisa nai saurin ɓoye fuskata cikin guiwata ina share zufar dake keto min, ƴar daɓas taci gaba da faɗin "bayan ta hana uwar gidan zama ta haukatar da ƙaramar itama ta gudu tabar gidan da ƙaramin ciki, rana ɗaya Allah ya tona mana asiri ya sakota tazo gida ta kashe uwar ta faɗa rayuwar bariki, da yake daman can tana ɗan taɓawa har tazo ta zama gogaggiyar karuwa ta buɗe gidan karuwai tou nan muka haɗu muke ƙawance ta ƙwace min saurayin da nake mugun so fiye da rayuwata ashe jira kawai suke nai tafiya zuwa wajen wani Alhaji na su ka siyar da gidan ƴanci suka gudu su ka yi aurensu, lbr kawai ya riskeni bbu irin neman da ban masu ba a garin nan amma ko mai kama dasu ban gani ba kuma ina kan neman nasu dan har yanzu ina kan bakana." Mdm Rebecca ta girgiza kai cike da Alhini tace "tou Allah ya kyauta ya shirye ku gabaɗaya ya kawo maku mazajen aure na gari" suka amsa da "Ameen" suna cigaba da ɓaɓɓaka dariya tamkar wasu taɓaɓɓu, Allah-Allah kawai nake mu baro saloon ɗin sbd a lkcn zuciyata tayi rauni,cikin ikon Allah aka gama min da wuri muka sallame ta muka fito, tunda muka shigo motar da fashe da wani matsanancin kuka harda shashsheƙa, ganin abun bana ƙarewa bane Leila tayi parking gefen titi tace "kin dage sai sharɓar kuka kike kin hanani nutsuwa yanzu tsakanin ki da Allah meye abun kuka a lbrn da mahaukatan nan suke faɗa? ni sam ban ɗaukesu masu cikakkun hankali ba wllh,kuma a wannan zamanin ko me akace mutum zai aikata meye abun mamaki ai zamanin ne yazo da haka sam bbu tsoron Allah a zuƙatan wasu mutanen so dan Allah ki daina kukan ya isa haka" ta faɗa tana yago tissue ta miƙo min, ba musu na karɓa ina goge hawaye, sai da ta tabbatar na daina kukan ta tayar da motar muka soma tafiya, then na ɗago ina kallonta nace "kinsan me yasa ni kuka"? ta girgiza kai tace "Aa" ta faɗi hankalin ta na kan tuƙin da take, murmushin takaici nai nace "Aunty Zuhra ce tayi mugun bani tausayi Sbd kema kinsan a daa! ba haka halinta yake ba, ta'ammali da mugayen ƙawayen banza shine yayi silar jefa rayuwarta cikin halaka har matsalar tazo ta shafe mu, anan kam tana buƙatar ayi mata uzuri duk da tana da nata laifin amma Salima ita ce silar komai sbd ita ta ɗora Aunty Zuhra kan turbar da ba daidai ba ita kuma sbd toshewar basira da ƙarancin ilimin addini ta hau kai ta zauna, sai ynzu nake danasanin ƙin kulata da nai kwanaki a makaranta, kuma wllh na yafe mata sbd itama ta cutu, ƙawar ta ƙwace mijin a ƙarshe mijin ya sake ta kinga nasan itama tayi danasanin ganin da nai mata ranar ya tabbatar min da lallai ta nutsu" Leila ta jinjina kai tace "aikam dai lkcn auren su da Ya Abdull ba haka take ba, ita dai ki barta da ƙazanta kawai amma gaskiya bata irin waƴan nan abubuwa Salima ce dai tayi nasarar gurɓata mata tunani a ƙarshe ta cuceta, Allah dai ya kyauta ai kowa yayi na gari dan kansa, Allah ya haɗamu da ƙawayen ƙwarai dan somtimes wllh iyaye suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen ɗora ƴaƴansu akan tarbiyyar da ta dace, amma lkc ɗaya idan yarinya ta haɗu da ƙawayen banza musanman idan tana da raunin imani zakiga ƙawayen sun juyar mata da tunani, Allah dai ya rufa Asiri" na amsa mata da "Ameen" har muka ƙaraso gida muna taɓa ƴar hira dangane da matsalolin mu na yau da kullum. tun sanda muka dawo nake bacci sai yamma liƙis na farka da wata irin kasala, na yunƙura zan tashi kenan Mum ta shigo ɗakin da sallama, na amsa mata ina murmushi tace "ana ta haramar sallah ke sai yanzu kika tashi daga bacci"? na ɗan shagwaɓe fuska nace "wllh bacci ne ɗaukeni sosai amma ai na tashi ynzun" girgiza kai kawai tayi tana murmushi ta wuceni zuwa Bathroom ba jimawa ta fito ta dubeni tace "tou maza ki shiga wanka ki fito kiyi haramar sallah zanje in taho da mai kwalliya" na ɗan ɓata rai nace "Mum da kanki zaki haɗamin ruwan wankan kuma? and wace mai kwalliya"? "ke bana son shashanci halan Mamin ki bata gaya maki yau zaku koma gidan ku"? a tsorace na gwalalo manya idanu na waje nace "yau kuma?" sai kuma na girgiza kai hawaye na taruwa a idona nace "ni wllh bbu wanda ya gaya min dan Allah kuyi haƙuri ko zuwa gobe ne wllh banyi shirin komai ba" Mum tayi ficewarta ba tare da ta kalli ko inda nake ba, na share hawaye na miƙe na shiga Bathroom,shi kansa ruwan wankan da ta haɗa min na musanman ne dan wani fitinannan ƙamshi ruwan suke, tsaki naja can ƙasan zuciyata nace "iska yana wahalar da mai kayan kara" haka na gama wankan na fito, na zauna gaban mirror ina shafa Lotion Leila ta shigo riƙe da leda ta ajiye saman gado tace "in kin gama ki saka kayan nan ki fito ana jiranki Mlm, kina wani ɓata rai sai kace bakyason zuwa karr nake ganinki Hjy, ni dai ina neman Alfarma yau ki taimaka ki barmin Papi bayan kwana biyu zan kai muku shi dan nasan yau dai ba dama dan duk wayon yarinya sai ansha romonta" ta ƙarasa cike da shaƙiyanci, ban ɗago na kalleta bama balle na bata amsa har ta ƙaraci iskancinta ta fice, shafa Lotion ɗin nake tamkar ina tausayin fatar jikina, haka na gama shafa man shima da ƙyar na zura doguwar rigar jallabiya da hijab na tada sallah, bayan na gama na cire hijabin na ƙarasa gaban gadon na buɗe ledar da Leila ta shigo dashi, wani tsadadden Lace Purple ne mai manyan stone masu shegen kyau da sheƙi suma purple ne, kai da ka gansa kansa an zuba dukiya wajen siyansa, tsaye nai gaban madubi bayan na sakasu, riga da sket ne ɗinkin zamani, sket ɗin irin dogon nan ne mai tsaka daga baya mai fito da shape ɗin mutum rigar ma sama a tsuke ƙasan rigar ya ɗan buɗe sai ɗinkin ya zauna ɗas a jikina sai dai gabaɗaya ya gama fito da Albarkatun jikina, sai mita nake ni kaɗai aka turo ƙofar ɗakin da sallama, Wata mata ce ta shigo riƙe da ƙatuwar jaka Leila dake bayanta ta nuna mata ni sannan ta fita, ɗan murmushin yaƙe nai na jayo kujera na bata ta zauna ina gaisheta dan matar ta girmeni sosai, ƙatuwar jakarta ta buɗe ta fara fito da kayanta na mak-eup hakan yasa nima na janyo kujerar mirror na zauna, cikin ƴan mintuna ƙalilan ta gama tsara min simple Mak-eup wanda yayi daidai da fuskata bbu wani takarce, tayi min ɗaurin ɗankwali shima mai kyau, ni kaina sanda na kalli kaina cikin mudubi nasan nayi kyau ba sai wani ya faɗa ba, muna gama kwalliyar tayi min sallama, ta fita kenan Leila ta shigo riƙe da wani leda again, ajiye ledar tayi tana "wow!! Ma sha Allah Mrs Abdull kin ganki kuwa anya kin taɓa irin wannan kyan"? hararar ta nayi ina ɗauke kaina ita kuma ta hau yi min pictures tana tsokana, ledar da ta shigo dashi ta buɗe ta warware wani purple mayafi da takalma simple suma kalar kayan ta miƙo min tace "kiyi sauri ana jiranki" nace "Ok dan Allah kawo min Papi sannan" tace "tou ai tun ɗazu na shiryasa yana can wajen babansa kuma kinga ni ba shiga part ɗin su nake ba sbd bama shiri da Umma" "tou yayi Allah ya shiryeki" na faɗa ina yafe gyalen na saka takalman na ɗauki wayata sai kuma na kasa fita dan wllh kunya nake ji, sai kawai naja kujera nai zamana har Mum tazo ta sameni a ɗakin ta rufeni da faɗa akan tun ɗazu Ya Abdull yana can part ɗin Baffah yana jira zamu wuce, ita ta saka ni a gaba har part ɗin Baffan mu, da sallama muka shigo falon dake cike taff da duk mutanen Family house ɗinmu babba da yaro duk Uncle's ɗinmu da matansu da yaran harda Hjy Inna, ni dai kaina a ƙasa a kunyace na zauna ƙasan ƙafafun Mami, Baba ya buɗe taro da addua ya fara mana nasiha mai ratsa jiki irin ta nagartattun iyaye,haka kowa yayi mana tasa nasihar tare da addu'ar zaman lfy aka watse, Mum ta ƙara kaini wajen Mami itama tayi min nata nasihar sannan ta kama hannuna ta kaini har mota inda yake jiran Fitowata. tunda na gaishesa ya amsa min na kwantar da kaina jikin kujerar, shiru mu ka yi tamkar kurame har muka iso makeken harabar gidan, Papi dake kan cinyarsa ma yayi bacci, yana yin parking ya fito saƙale da Papi a kafaɗarsa ya zagayo ya buɗe min na fito ina ƙarewa harabar gidan kallo, boot ya buɗe ya umarci mai gadi ya shigo da kayan ciki, yayi gaba ina biye dashi, tafiya sosai mu ka yi sannan muka ƙaraso makeken falon wanda ya yayi kyau harya gaji da haɗuwa, gabaɗaya tsarin gidan ya gama tafiya dani,komai na gidan sabo ne hatta fournitures ɗin gidan su kansu abin kallo ne, komai na falon golden ne, na kasa bin bayansa na tsaya a falon ina ƙara kallon ko ina harya fara hawa uptairs ya juyo yana kallo ganin na tsaya yace "halan nan zaki kwanta naga kin tsaya"? na girgiza kai nabi bayansa har zuwa saman, ya subhanallah sai da muka hau sama na raina kaina sbd ƙayatuwar saman, nan ma babban falon ne shima adonsa da komai nasa daban yake dana ƙasa, shi na saman komai da komai purple ne babban Tv plasma ɗin ne kawai black, a nan saman ma sai anyi ƴar tafiya sannan zaka kai ga ɗakunan bacci, tun shigowar mu na fahimci an zuba ma'aikata masu kula da ko wane ɓangare a gidan, sbd tunda muka shigo ma'aikata mata ke ta shawagi a wajen sai zubewa suke suna gaishe mu har muka iso saman, shi saman bbu kowa alamun ma'akata basa shigowa wajen ma kwata-kwata, ɗakin dake tsakiya ya sanya key ya buɗe muka shiga, wani daddaɗen ƙamshi mai gauraye da sanyin Ac ne yake welcoming ɗin mu, babu wani takarce a bedroom ɗin gado da manya kujeru uku ne irin wanda ake sakawa a ɗakunan bacci sai wadrop da tv sai lafiyayyar Carpet pink dake shimfiɗe, komai na cikinsa Pink ne hatta kujeru da gadon da komai, a hankali ya ƙarasa gaban makeken gadon ya kwantar da Papi, ya juyo yana kallona yace "wai meye haka ne Nu'aiyma kin tsaya kina abu kamar ba gidan ki ba? ko dai har ynzu baki yadda da yayanki bane? tou ki sauya masa kayan jikinsa wannan sunyi nauyi kema kiyi wanka ki kwanta ina zuwa" kai kawai na gyaɗa masa na buɗe press ɗin ɗakin na ciro kayan bacci na sakama yarona bayan na gyara masa kwanciya na masa addu'a nima na shiga wankan, ina tsaka da wankan na ji motsin shigowa ɗakin, na ƙarasa wankan na fito ɗaure da Towel iya cinya, zaune yake cikin jallabiya ruwan milk har yayi wanka ya canja, waya yake dannawa nan na kalli gabansa naga Plate ɗin gasassun kaji ne da lemon kwali mai sanyi a gabansa, ƙarar rufewar Toilet ɗin yasa ya ɗago da sauri ganin bbu kaya a jikinta Towel ɗin ma ɗan gudu ne dan iyakarsa tudun mazaunanta yayi saurin ɗauke kai, gyaran murya nayi cike da kunya nace "uhm ina aka kai min kayana"? "duba a wadrop zaki samu ynzu dare yayi ni bbu inda zan fita kuma" ganin yadda ta ɗan turo baki yasa shi saurin ɗauke kai yana murmushi, sai da ta juya yabi bayanta da kallo, ɓata rai nayi sanda na gama duba kayan gabaɗaya bbu kayan arziƙi a ciki, na juyo ina langwaɓar da kai nace "Eyyah! tou ai bbu kayan arziƙi a nan dan Allah ka taimaka ka kawo min rigar da zanyi sallah please" "Okay! ɗan jirani" ba jimawa sai gashi ya dawo ɗakin riƙe da rigarsa jallabiya, idanu na ɗan zaro nace "wannan rigarka ce" "eh wllh sai kin saka yi sauri kizo muci abincin ni bacci nakeji" na maƙe kafaɗa nace "Aa gaskiya ni bazan saka rigar maza ba" yayi tsai yana tunani then ya ɗago yace "Okay ki saka kiyi sallah muci abincin in mun gama sai kizo muje ɗakina kayan ki suna can kinga sai zaɓi wanda kikeso" nace "tou" na karɓi rigar na saka, dariya ya fara min ganin yadda rigar tayi min yawa yana faɗin nayi kyau cikin rigar maza, shi yaja mu sallah raka'a biyu yayi mana addu'oi, plate ɗin naman ya jayo ya ajiye gabana na girgiza kai nace na ƙoshi, wani kallo yayi min yace "kici nace" nace "kai fa"? yace "na ƙoshi" nace "tou ai nima na ƙoshi" yayi murmushi ya saka hannu ya faraci ganin haka na ɗauki cinya ɗaya shima da ƙyar na cinye na wanko hannuna nayi brush na dawo na kwanta kan gado, ya jima zaune yana Operating ɗin wayarsa har bacci ya fara ɗaukana ya miƙe ya fita da kayan ba jimawa ya dawo yace "Tasbahii Alaa Khaaiir in kina buƙatar kayan sai ki biyo ni ki karɓa" "eh inaso dan Allah ka kawo min anan bazan iya fita nabar Papi ba" kallon da yayi min ne yasa na miƙe nabi bayansa dan harga Allah ina buƙatar kayana, yana gaba ina biye a bayansa ina ɗan harararsa a fakaice har muka iso ɗakin. sai da ya bari na ƙarasa can tsakiyar falon yasa key jikin ƙofar yana faɗin "wa na kama"?
Yau naso kawo ƙarshen lbrn amma ayyuka sun hanani saƙat!.
Share Fisabilillah