*ONE BLOOD*
_Episode 37-38_✍🏼
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSel_o3rogkHJZAAAmRHh2J_kZZOyZvH6cWZ40nJ2u3iYtvaXw/viewform
_DAN GIRMAN ALLAH MASOYAN ONE BLOOD DA KUMA MASOYANA NA HAƘIƘA KU DAURE KU SHIGA LINK ƊIN NAN NA SAMA DA KUKE GANI KUJE KU YIWA SISINA HASSANA ƊAN LARABAWA VOTING A CIKIN LITTAFIN TA MAI TAKEN *BA ZATO!!* KAR KU MANTA ITA CE *B* PLEASE INA NEMAN WANNAN ALFARMAR A GAREKU NASAN BAZA KU BANI KUNYA BA_ 🤲🏽
Mumy ta ƙara matsar ƙwallah tace "kayi shiru ina mgn?" Abbie yace "to ya kikeso in ce?? ni na haifi Aliyu nasan halinsa da ɗabi'un sa tun yana ɗan ƙanƙanin sa, nasan abinda zai iya aikatawa kuma nasan wanda bazai aikata ba, nasan Aliyu ba manemin mata bane so dan Allah ki rabu dani kina neman saka min ciwon kai" Abbie ya faɗa yana kwantar da kansa jikin sofa, Mumy ta sake fashewa da wani mahaukacin kuka wiwi kai kace ƴar yarinya ta fara maganganu marar sa kan gado "shikenan Alhaji kaima ka amince da maganganun jama'ar gari na cewar banason Aliyu dan yana ɗan kishiyata, duniya zata faramin kallon muguwa ace na baiwa yarana tarbiya amma ɗan kishiya ta ya gagare ni basusan cewa kwata-kwata Aliyu baya jin magana ta ya raina ni kai a taƙaice ma bayason ganina gidan nan gani yake nice silar raba ku mahaifiyar sa" haka Mumy tayi ta surutai marar kan gado tana ƙara jaddada masa lallai sunga mace mai ciki a part ɗin Aliyu har Abbie ya fara kwaɗaituwa da son sanin ainahin abinda ke faruwa a gidan nasa dan shi ba mazauni bane matafiyin ƙasashan waje ne sbd harhar busness ɗinsa, amma baice da Mumy komai ba ya miƙe tsam yayi hanyar ɗakin sa ta bisa da harara tana murmushin mugunta. bayan sallar isha a hanyar su ta dawowa gida Abbie yace Aliyu ya samesa a falon sa zasuyi mgn, cike da mamakin kiran nasa Aliyu yace "to" sannan ya koma ciki dan hankalin sa gabaɗaya ya karkata gun duba lafiyar Aiymah dan tun jiya rabon sa da ita gashi kuma jibi zai bar ƙasar zuwa US wajen su Ammi, kai tsaye ɗakin sa ya wuce yayi wanka ya canja kaya ya dawo falo yaci abinci sannan ya nufi ƙofar ɗakin ta ya fara ƙwanƙwasawa a hankali, tana kwance saman gado sai murƙususu take hannunta dafe da mararta, hawayen tsantsar azaba da raɗaɗi ne kebin kuncinta sai juyi take, a hankali ta fara jin ana bubbuga ƙofar ɗakin amma ta kasa ko ɗago kai balle ta iya tashi, tun yana buga ƙofar a hankali har ya fara bugawa da ƙarfi amma shiru kake ji, hakan ne ya tabbatar masa da bbu lafiya ya tura ƙofar ya zura kai ciki, halin da ya tsinkaye ta ciki yasa ya ƙarasa gunta da sauri ba tare da ya kawo komai a ransa ba, lumfashin ta ne ke fita da sauri-sauri ga kuma idanunta da suka sauya kala zuwa jaa kamar garwashin wuta, idanu ya ɗan zaro cike da tsoro ya juya da niyar fita ɗaukar wayarsa yaji caraf ta kamo hannun sa, ya juyo yana kallon yadda ta damƙe hannun sa gam! tana matsar ƙwallar azaba hannunta dafe da mararta, yayi saurin kawar da kai yana tsarkake sunayen Allah a zuciyar sa, ya ƙwace hannun sa daga nata cike da tausayin baiwar Allah, juyowar da zaiyi da niyyar fita daga ɗakin sukayi ido huɗu da Abbie dake tsaye a ƙofar ɗakin hannayensa sarƙe a ƙirjinsa, lbrn zuciya a tambayi fuska, to iya fuskar Abbie kaɗai ta isa ta nuna maka tsantsar ɓacin ransa, cikin i ina yace "batada lafiya ne Abbie" Abbie ya tsurawa kyakkyawar matashiyar yarinyar dake kwance kan gado sai murƙususu take yana nazarin halin da take ciki can yace "ka kira Dr ya duba ta" baiko tsaya jin ƙarshen zancen Abbie ba ya wuce da hanzari, then bayan 10 minutes ya dawo ya samu Abbie tsaye a inda ya barsa, mintuna ashirin kacal Dr ya iso ya fara bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah abun ya lafa, ya buƙaci a kawo mata tea mai zafi ta shaa, bayan tasha yayi mata allurar bacci bayan ya bata magani tasha ta kwanta sannan ya rubuta ma Aliyu magungunan da za'a siyo mata bayan ya musu bayanin komai. then bayan tafiyar Dr Abbie ya tsare Aliyu da tambayoyi, ganin yadda ran mahaifinsa ya ɓaci ya gaya masa gaskiya bai ɓoye masa komai ba ya ɗora da faɗin "Sultan da Dr sune shaida ta" Abbie ya jinjina kai cike da gamsuwa then yace "kun kai cigiyar ta gidajen redio da police station"? ya sunkuyar da kai yace "a'a" "zan iya sanin dalili"?? Aliyu ya sosa ƙeya yace "Sultan ne ya hana" Abbie yace "gobe zan bar ƙasar amma ina dawowa zan kirasa naji dalilinsa nacewar kar akai cigiyarta kuka san irin damuwar da ahalinta suke ciki amma sbd rashin hankali kuzo ku girke ɗiyar mutane a gida ba cigiya ba komai" haka Abbie yay ta faɗa ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba a ƙarshe ya sallame sa, a washe garin ranar Abbie yabar ƙasar ba tare da ya baiwa Mumy tarin tambayoyin da take masa. tunda Aliyu ya raka Abbie Airport bai dawo gida ba direct offise ya wuce, a ranar sosai ayyuka suka masa yawa shisa bai samu dawowa gidan ba sai ƙarfe goma na dare, bai wani tsaya ɓata lkc ba ya hau shirya kayansa na tafiya, bayan ya kammala ya samu nutsuwa ya kira Rabi a falo ya ƙara damƙa mata amanar Nu'aiymah "bazan daɗe ba sati biyu kawai zanyi dan Allah ki kula da ita ki dafa mata duk abinda takeso zan baki kuɗi ki ajiye gunki ko da kunyi buƙatar wani abun duk da akwai komai, sannan karki bari ta fita ko nan zuwa ƙofa ne saboda kinsan halin matar gidan da yaran, wlh in wani samu yarinyar nan ke na sani karki bari ta fita kar kuma ki bari kowa ya shigomin falo" gaban Rabi na faɗuwa ta amsa da "In shaa Allah" wani ɓangare na zuciyar ta nason faɗa masa abinda ya faru shekaranjiya amma da zaran ta tuna warning ɗin da Mumy tayi mata sai ta haƙura, ɗakin Aiymah Aliyu ya ƙarasa dan yi mata sallama, ƙofar a buɗe tana zaune saman sallaya carbi a hannun ta, karon farko yaga ta sakar masa murmushi har dimple ɗinta suka lotsa, ya mayar mata da martani ya zauna saman kujera har ta shafa addu'a ta kuma ɗagowa ta dubesa, then Aliyu yace "dama nazo miki bankwana ne gobe da safe zan bar ƙasar zanje wajen Ammi na amma bazan daɗe ba sati biyu kawai zanyi na dawo" gaban Nu'aiymah yayi wata irin faɗuwa jin zaiyi tafiya kuma shi kaɗai ba da ita zashi ba, idanunta suka cicciko da ƙwallah sai kuma ta fashe masa da kuka. Aliyu ya tsaya yana kallon Ikon Allah dan shi dariya ma ta bashi, ganin ba tada niyyar tsaida kukan yace "yi shiru mana ƴar ƙanwa ta! faɗamin mecece matsalar"? ta tunzuro baki gaba tana maƙe kafaɗa still hawaye na sintiri a face nata, yana murmushi yace "kina son in fasa tafiyar ne"? ta girgiza masa yace "so kike in tafi dake"? da sauri ta gyaɗa masa kai tana washe haƙora gamida share hawayen fuskarta, kasa danne dariyar sa yayi ya fara mata dariya tamkar zai kife ƙasa, ganin dai yadda ta nace sai ta bishi yasa yace ta shirya kayanta.
ko da shagari ya yima su Baffah zancen duk su ka yi na'am da zancen, yammacin ranar duk suka ɗunguma zuwa gidan Abdull tare da Mlm Sule, da sallama suka shigo makeken falon, yau ma zaune suka samesa a falon yana aiki a laptop yana ganinsu ya miƙe tsaye yana musu iso da ƴar yaƙe a fuskarsa, duk suka samu wuri suka zazzauna, tun shigowar su falon Mlm ya tsare Abdull da idanu bbu ko ƙiftawa yayinda shi kuma gabaɗaya ya takura sai wani sunkuyar da kai yake irin wanda bashi da gaskiya ɗin nan, sai kuma ya miƙe zumbur zai bar falon Mlm ya yafito da hannu Alamun yazo garesa, Abdull ya tsaya a inda yake shi bai tafi ba kuma bai dawo ba, Mlm ya taso da kansa riƙe da lafcecen carbin hannunsa ya dafa kafaɗarsa, ya juyo a fusace yana aika masa da wani kallo mai ban tsoro da firgitarwa da manya eyes ɗinsa da su ka yi wani irin jaa mai ban tsoro da rikitarwa tamkar ba na mutum ba, da ido yayi ma su Qaseem mgn da zuso su kamasa su kuma rufe part ɗin dan muddun yasa ƙafa yabar falon da wuya su iya kamosa dan ya fahimci ƙoƙarin guduwa Aljanin jikinsa yake. da ƙyar da siɗin mutanen falon su ka yi nasarar gurfanar da Abdull a gaban Sule sannan suka rirriƙe masa hannu da ƙafa ta yadda bazai iya wani ƙwaƙƙwaran motsi, Mlm ya buɗe ƙur'anin gabansa ya fara karanto ayoyin karya sihiri ba ƙaƙƙautawa, tun Abdull na gurnani har ya faro ihu cikin wata irin murya mai firgitarwa yana basa haƙuri da kar ya ƙona sa shima aikosa akayi, Mlm yayi murmushi ya buɗe jakarsa ya fiddo ruwan zam-zam a zuba cikin cup ya zuba wasu magunguna a ciki sannan yayi addu'oi ya ɗura masa ruwan maganin ya shafa masa sauran a jiki, yacigaba da karatun da yake "ka ƙyalemu ka daina ƙona mu" "bazan daina ba sai kun gaya min me kuke a jikin bawan Allah'n nan kuma wa ya turo ku"? "bazamu faɗi wanda ya turo mu ba amma kayi haƙuri ka daina ƙona mu zamuyi tafiyar mu" "naji zan ƙona ku amma wlh muddun kuka sake dawowa sai na ƙona ku ƙurmus shaiɗanu kawai" "eh munji mun yarda kuma mun amince amma ka daina ƙona mu" Mlm ya dakatar da karatun da yake, wani baƙin hayaƙi ya fara fita ta baki da hancin Abdull lkc ɗaya ya fara tari sai jikinsa da yayi wata irin zufa ya zame ya kwanta ragwajab saman carpet sai bacci. Mlm Sule yace "Alhmdllh Allah mun gode maka da basu nuna taurin kai ba, Rabb ya ƙara kiyayewa ya nisantamu da mugun ji da gani, ina mai shawartarku da ku gaggauta nisantashi da gidan nan kafin ma ya farfaɗo dan sam! ban yarda da gidan nan ba, Allah ya bashi lfy ya kuma bayyana matarsa kuma In shaa Allah tunda mun shawo kan matsalar tasa itama zanyi listahara akanta zamu kuma tsananta addu'ar Rabb! ya bayyana ta" duk suka amsa da "Ameen" su ka yi masa godiya ta musanman, aka ɗauko Abdull sukasa a mota sannan suka kulle gidan duk suka fito aka ɗunguma zuwa Family house da shi.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na rana jirginsu Aliyu ya sauka a ƙasar *US* tunanin abinda zaice ma Amminsa akan Nu'aiymah kawai yake har drivern da Ammi ta turo ɗaukarsa ya iso, ya buɗe mata baya ta shiga shima ya zagaya ya shiga bayan driver ya saka kayansu a boot, daidai wani haɗaɗɗan madaidaicin gida driver ya fara horn har gate man ya ƙaraso ya buɗe ya danna kai cikin gidan, ita dai Nu'aiymah sai kallon garin take cike da shauƙi da annashuwa har motar tayi parking a harabar gidan, wata kyakkyawar budurwa ce tsaye a harabar gidan kusa da wasu kyawawan Furanni masu kyau da ƙamshi, sanye cikin doguwar rigar a baya baƙa mai manyan stones ruwan zinare ta yane kanta da ɗankwalin, sosai kayan suka karɓi fatarta kamar wata black american, kamar su ɗaya sak da Aliyu bbu wani bambanci. tana ganin motar tayi parking da gudu ta ƙaraso hakan yayi daidai da fitowar Aliyu a motar ya zagayo zai buɗe ma Nu'aiymah kenan Yasmine ta faɗa jikinsa tana masa Oyoyo, ya sakar mata murmushi cike da so da ƙaunarta kana ya buɗe murfin motar Aiymah ta fito, Yasmine tayi turus tana kallon ikon Allah baki hangame ganin yayanta da mace, Aliyu yasa hannu ya ɗalle mata bakin yace "baki iya gaisuwa bane kin sa ta gaba kina kallo iye"? ta ƙyalƙƴale da dariya ta saki hannunsa ta kamo na Aiymah ta riƙe tana murmushi hakan yayi daidai da fitowar Ammi ta fito tana welcoming ɗan nata, kallo ɗaya tai ma Aiymah gabanta yayi wani irin faɗuwa sakamakon kamannin da ta hango sak dangane da yarinyar amma bata nuna hakan a fili ba, sai kuma mamaki na biyu da take shine meya haɗa Aliyu da mace?? duk da tana buƙatar ƙarin bayani but ta tattare komai gefe ta tarbe ta hannu bibbiyu tamkar ƴarta ta ciki daga bisani duk suka ɗunguma zuwa makeken falon gidan. Yasmine ta sauke Aiymah a ɗakinta ta haɗa mata ruwan wanka sannan ta fito falo, zaune ta samu yayanta da Ammi har yayi wanka ya canja kaya Ammi ta sakashi a gaba tana masa tambayoyi ya fara bata amsa iya gaskiyar sa, ya bata lbrn duk abinda ya faru har rashin maganar ta, sosai su ka yi mamaki kuma yarinyar ta mugun basu tausayi, Ammi dai tayi zugum tana mamakin tsananin kamar da yarinyar take da tsohon mijinta kuma uba ga ɗanta Aliyu.
*TOH FAH MEKE SHIRIN FARUWA🥱NIMA DAI BANSANI BA MUJE ZUWA KAWAI, MASU GAJERUN COMMENTS DA STIKERS KO THANKS/ TNX ƊIN NAN KU DAINA WLH NA YAFE MUKU BANA SO😑MUDDUN BAZAKI MIN DOGON SHARHIN DA ZAI FARANTAMIN BA IRIN COMMENTS ƊIN NAN DA SAI MUTUM YA GAJI DA KARANTAWA TOU KI RIƘE ABIN KI BANI SO.* 😒