ONE BLOOD

83 2 0
                                    

⚡ *ONE BLOOD* ⚡

_Mallakin Nu'aiymah Abdull Tafida_

_Book Dedicated to My Tween Sis Na'imah Abdull Tafida._

_Episode 13&14_

_Assalamu alaikum Ma"abota karatun Littafan Hausa kama Daga Littafin Daya karkata kan Soyayyah ko ya karkata kan  Nishadantarwa ko ya karkata kan Fadakarwa,ko ya karkata kan Wa"azantarwa ko kuma ya karkata Wajen Ban Tsausayi da Rudani..Toh ku matso Kusa Nesa Tazo Kusa Ina Wadanda basu iya Juran karatu Saboda  Matsalan Ido kuma gajiya ko kuma ayyukan Gida na yau da kullum wanda baya basu Damar Lokacin karatu..? To ku kwantar da Hankalinku Kina Daga Dakinki kina aikin ki ko kuma kina Daga Zaunenki basai kin Wahala wajen karatu ba *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* Ba domin komai suka samar da wanman Channel din ba Sai Saboda Irinku masoya ma"abota Karatun Littafan hausa koma wani iri ne,Muna da Littafai ko wani iri kike Bukata wannan Channel Din ba iya littafan Hausa ya Tanadarmuku ba ya Tanadar muku Abubuwa Da yawa wadanda zaku karu dasu,Ga mai Bukatar kwasan garabansa Dake Cikin Wannan Channel Din zai iya Tafiya kai Tsaye Zuwa ga *YOUTUBE* Dinshi yayi Searching *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* Domin samun Duka Shiryan Shiryanmu akan Lokaci kada mutum ya Manta da Danna Mana *SUBSCRIBE* da kuma Allon kararrawan Sanarwa Domin ya sanar Daku da Zarar mun Dora muku wani Sabon Shiri In kuma kuna son Tafiya ne kai Tsaye zaku iya Shiga ta wannan Link din Batare da Bata Lokaci ba Zaku Tsinci kanku a   *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* sai kunzo muna Maraba Daku Masoyanmu..._👇🏻

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Bacci ne ya ɗauke shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali amma abun mamaki sautin kukan ta sam ya hanashi samun gamshashiyar nutsuwar baccin kalamanta ne suka addabi kunnen sa suka shiga masa yawo a brain ɗinsa cikin kuka da magiya. "Abdull don Allah kayi haƙuri ka barni wallahi ban saba ba! don girman Allah karka lalata min kima ta wlhy da zafi akwai ciwo don Allah ka bari na daina maka rashin kunya ka barni haka bazan iya jurewa ba." Zumbur ya tashi ya zauna tare da dafe goshin sa ya zira ƙafarsa yay ƙasa ya mik'e da sauri ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin da ya barta a yashe. tunda ya tura kofar idanun sa ya sauka a kanta, Mami da Baffa ne suka faɗo masa a rai a take jikinsa yay masifar yin sanyi a ransa ji yake ta gama masa komai tunda har ta iya kare kanta da mutuncinta, wani kima da darajarta yaji ya fara ji a zuciyarsa,takowa yayi har cikin ɗakin ya ƙura mata ido yana kallonta, buɗe kumburarrun idanuna nayi a kansa, a razane na rufe su dan abubuwa uku suka na keji a kansa, na farko ƙiyayyarsa da nakeji ta ƙaru a raina, na biyu tsoronsa da nake masifar ji na uku bana ƙaunar sake kallonsa a rayuwata. Yunkurin miƙewa nake amma bani da kuzarin yin hakan da zaran na tattaro ƙarfi na sai naji gabaki ɗaya jikina ya mutu, Abdull bai bi ta kanta ba ya shige toilet ya haɗa mata ruwa mai zafi sannan ya fito, ganin yadda take ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa ya sashi sakin murmushi ya taka a hankali ya isa inda take ya ɗauketa cak ba tare da yayi mata magana ba ya nufi toilet da ita, duka na shiga kai masa ina mutsu-mutsun sauka daga jikinsa cikin dishasshiyar murya ta nace. "Ni ka sauke ni mugu kawai azzalumi dama abinda kake so kenan ka lalata min rayuwa kuma ka samu kaga bambanci tsakanin tunaninka da zahiri ka sauke ni Allah sai ya saka min abun da kai min dan ka cutar dani bazan taba yafe maka ba." Shiru nayi ina sauke Ajiyar zuciya tare da wasu kwallar wahala sakamakon ajiyeni cikin ruwan zafi da yayi, riƙe wuyansa nai ina girgiza kai cikin kuka nace. "Ka cire ni a ruwan da zafi wlh." Rungumeta yayi tsam a jiknsa yace. "Am sorry my sis bazan iya cireki ba kiyi haƙuri kinji." kukan rigima na farayi ina dukansa a kirji, da ƙyar ya lallaɓata ya gasa mata jiki sosai tsabar taji ruwan zafi har wani ja tayi. Da taimakon sa tayi wankan tsarki kusan ma shi ya wanke mata gurin tana kuka tare da riƙe hannunsa, goshinta yayma kiss cikin tsantsar tausayawa haɗi da tattausar kalma yace. "Kiyi haƙuri kinji bazan kara ba gashi kema zaki ji daɗin jikinki." haka ya gama sannan ya naɗo ta ya dawo da ita cikin ɗakin yazo ya kwantar da ita a dogon kujeran ɗakin ya cire zanin gadon wanda ya ɓaci ya shimfiɗa wani sannan ya fita da wanda suka ɓata, ɗakin da washing machine yake ya kai bedsheet ɗin ya saka tare da zuba omo da ruwa ya kunna sannan ya fito ya shiga kitchen ya dawo ya haɗa mata tea mai zafi ya hauro mata dashi, wardrop ɗinshi ya buɗe ya ɗauko mata magani ya zauna a gabanta sai da ya tabbatar tasha har tana zufa sannan ya fita zuwa ɗakinta ya ɗauko mata doguwar riga ya kawo mata, cikin nutsuwa yasa mata sannan ya maida ita gadon ta kwanta, shima kwanciya yay a bayanta tare da zagaye hannayensa kan kirjinta ina murmushi. a halin da nake ciki bazan iya masa magana ba dan baccin gajiya ne sosai a jikina shiyasa nai masa shiru nayi banza dashi amma na shirya masa zallar rashin mutunci bayan warkewa ta. Basu tashi ba sai ƙarfe uku saura ya rigata tashi, toilet ya shiga yay wanka tare da alwala ya fito jallabiya ya saka ya fesa turare ya fice daga ɗakin ya nufi masallaci, ina jin ya fita nima na lallaɓa na miƙe ina takawa a hankali na fice zuwa ɗakina na sake gasa jikina sosai sannan nayi wanka da alwala na fito, cikin nutsuwa na gabatar da sallar azhar ina idarwa na sake ɓingirewa da barci. Kusan wunin wannan ranar Abdull shi yake ta ɗawainiya da ita dan ko office baije ba! tun daga kan girkin da yay musu zuwa irin kulawar daya dinga bata. zuba masa idanu kawai nake ina kallonsa tsaf ina Ayyanah irin tsantsar rashin mutuncin da zan shuka masa idan na gama wartsakewa na koma dai-dai duk da ina jin tsoransa amma sai na dau fansa. Bayan kwana biyar zuwa lkcn na warke na dawo normal kamar bani ba, tun daga wannan ranar ban sake shiga sabgarsa ba! Haka nake shiga dakina nayi bacci tun ina jin tsoron har na daina. Zuwa lkcn tuni Mami ta samo min mai aiki wacce zata dinga tayani ayyukan gidan, tunda Larai tazo gidan kwata² hankali na bai kwanta gare ta ba haka kawai naji batamin ba! Amma ban nuna mata ba sai dai sam! Bana sake mata. Ni nake gyaran sama da dakunan sama da girki, ita kuma ta gyara kasa da kitchen sai dakunan kasa da wanke² da dai sauran su. Kwanan nan ban cika zama gida ba kullum ina hanyar school tun karfe takwas idan na fita bana dawowa sai karfe biyar na yamma. Haka nan kuma bamu cika ganin juna da Abdull ba dan kwata² ya daina ganin fara'a ko wani abu makamancin hakan a fuskata tun ranar da abun ya faru, bana masa rashin kunya bana masa mgn daga gaisuwa sai amsa sallama idan na dafa abinci in ajiye masa idan ya gama in kwashe kwanukan, yayi rarrashin duniya da tambayar meke damu na? Amsar ita ce. "Ba komai." Tun yana kulani har shima ya share ni, a haka muka cigaba da zaman doya da man jaa. Sati biyu kenan da barin Zuhra a gidan Abdull amma bai waiwaye ta ba! Tsaya fada muku tashin hankalin da ta shiga kuwa wlhy bata lkc ne, Bbu kalar magiyar da bata yiwa Mama ba akan ta daure ta kira Abdull ta bashi hakuri dan yana jin maganar ta sosai amma Mama tace ita baza ayi wannan abun kunya da'ita ba! Tunda tazo gidan kuma Mama ta hana su Zainab yin komai Zuhra ce ke yin shara wanke² tayi musu girki. Kuma duk safiyar Allah Sai Mama ta tilasta mata yin wankan safe na rana dana dare. Yau ma kamar Kullum, zaune suke karkashin bishiyar gidan, Mama ta saka Zuhra a gaba akan sai ta tsefe kanta da ya kusan wata biyu a kitse har ynzu bata tsefe kan ba, ita kuma ta nace akan ba ynzu ba sai in zata koma gidanta, sai da Mama tayi mata tatas! Sannan ta yarda ta fara tsefe kan, fada sosai Mama tayi mata daga nan kuma ta zarce da yin nasiha, jin ta kawai Zuhra take amma tayi zurfi cikin wani tunanin daban, ana tsaka da wannan dramar kannin ta Zainab da Ummi suka kwada sallama suka shigo kasancewar su Hudu ne a wajen iyayen su, mahaifin su Malam Salisu ya jima da rasuwa tun Auta Ummi na da shekara uku a duniya, Jafar shine dansu Babba sai Zuhra sai Zainab sai Auta Ummi. Yayansu Jafar yaro ne mai kwazo da son neman na kai uwa uba wadatar zuci, duk da basu da wani hali Amma bai rage 'yan marayun kanninsa da komai ba duk da Abdull na taimaka musu sosai ta fannoni da dama, shekarunsa 26 yana da shago a bakin kasuwa amma duk da haka yana cigaba da karatunsa dan yana da burin zama babban Lawyer, Zuhra kam tunda aka yi mata aure da Abdull ta dakatar da karatun ta, bbu kalar rarrashin da ba'ayi ba amma tace sam! Baza ta koma ba shiyasa suka zuba mata idanu, Zainab da Ummi kam Abdull ne ya dauki nauyin karatun su kasancewar suna da kwazo sosai suka mayar da hankali dan sun san karatun shine gatan su. Wannan shine takaitaccen tarihin gidan su Zuhra, fira suke cike da Nishadi gwanin ban sha'awa bayan dawowar Yah Jafar daga kasuwa sabanin Zuhra da ta karkata kai gefe tana fixgar gashin kanta da karfin irin an mata dole dinnan. Ring din wayar ta ne ya dakatar da'ita, ganin no din Salima ya sata mikewa a zabure ta shige dakinta tana murmushi. Da kallo su Mama suka bita dashi suna mata fatan shiriya a zuciyar su, Jafar kam ko duban inda take bai yi ba dan idan yana kallonta ji yake tamkar ya tashi yaci ubanta ko zai ji sassaucin zafin da zuciyar shi take masa a kanta. Sai da ta kulle kofar dakinta sannan ta zube saman katifar tayi picking. "Hello! Tawan dan Allah kice min kun dawo." Salima tace. "Wlh tun jiya muka shigo gari ban ma huta ba nazo gidan ki ynzu haka gani tsaye a kofar gidan ki gate man yake sanar min 2week bakya gidan ko kunyi tafiya da mai gidan ne."? Numfashi ta furzar mai zafin gaske sai kuma tayi kwafa tace. "Ya koro ni gida." "Whatt! Sakin ki yayi? Me kika masa har haka."? Salima ta jero mata tambayoyin duka a time guda Zuciyar ta wasai. Share kwalla Zuhra tayi tace. "Bai sake ni ba kuma ban masa komai ba, ya koro ni ne Sbd tsinanniyar yarinyar can, yaci mutunci na ne duk Sbd ita, ynzu kuwa lkcn daukan fansa ne dan na rantse da Allah ko ana haa maza haa mata sai na koma gida na sannan in fito da'ita tsinanniyar can da yaci mutunci na akanta." Ta karashe tana share kwalla, a take wani sabon bakinciki ya mamaye zuciyar Salima ita da take tunanin Abdull ya sake ta ne da abun yazo mata da sauki dan ita fitar da Nu'aiymah a gidan Abdull ta maye masa gurbin duka biyun karamin abu ne a wajen ta, Zuhra ce babbar matsalar ta amma ba komai za tabi komai a sannu zata biye mata har nata burin ya cika sannan ita ta sake sabuwar damara, da wannan tunanin ta dan saki murmushi mai sauti tace. "Zaki samu fitowa ynzu."? Shiru tayi tana tunani can tace. "Yah Jafar yana nan kuma ba lallai Mama ta barni in fita ba, amma ya kike ganin za'ayi." Salima tace. "Kawai kisan karyar da za kiyi mata ki fito." "Ni ban iya karya ba please ki bani shawara." Shiru Salima tayi tana tunanin abinda zata ce mata can ta daure tace. "Kice mata za kije Saloon." Ihu Zuhra ta saki tace. "Good girl kin kawo shawara mai kyau ynzu kuwa na tsefe kai na." "Okay kiyi sauri ina jiran ki karki batamin lkc." Zuhra tace. "ban gane ba nifa ban fito da mota ba ke zaki zo dauka na a bayan layin mu." "Okay! Tou ki hanzarta." Daga haka su kayi sallama Ta karasa tsefe kanta zuciyarta Wasai, bayan ta gama ta fito tsakar gidan ta tari ruwa a bokiti ta shiga wanka. A gaggauce tayi wankan ta fito ta shirya cikin Atamfa riga da zani da katon hijab ta fito rike da purse dinta, ta durkusa gaban Mama tace. "Mama zan je wankin kai Saloon bazan jima ba zan dawo naga akwai hadari a garin." Mama tayi murmushi tace. "Iye 'yar gidan Mama ta fara jin magana ta, ke kanki zaki ji dadin kanki Amma kizo ki zauna da kitso kusan wata biyu ba gyaran kirki haba! Ni na rasa halin wa kika biyo Fateemah, Allah ya kara shirya min ke amma don Allah karki jima kinga akwai hadari a garin inba so kike ruwa ya doke ki." Mama ta karashe tana kokarin kunce habar zanin ta ta ciro dubu daya zata bata, tayi murmushin yake tace. "No mama ki barshi ina da kudi." Daga haka tayi musu sallama su Zainab suka mata a dawo lfy ta amsa musu ta fice, Jabir ya dubi Mama bayan fitar Zuhra yace. "Mama ta tambayi mijin ta kafin ta fita."? Sai a lkcn Mama ta saki salati tana tafe hannaye dan ita ta manta shaf! Kuma tana da tabbacin Zuhra bata fada masa ba dan tunda tazo bai waiwaye ta ba! Jafar ya sauke ajiyar zuciya cike da takaicin halin kanwar tasa yaci gaba da hidimar gabansa. Zuhra na fita ta kara kiran Salima tayi mata kwatancan inda take tazo ta same ta suka kama hanyar wani dan kauye da bashida nisa dasu sosai gidan wani Malamin tsubbu. Koda suka iso basu samu ganin mutumin da wuri ba dan sun tarar da mutane sosai, sai kusan karfe daya na rana layi ya iso gare su suka shige runfar suka zauna gaban shirgegem mutumin da halittar jikinsa ma abin tsoro ne dan suffar samudawa ne dashi ga kuma fuskarsa a fente da abubuwa na ban Al'ajab sai zara-zaran faraten yatsu da na kafa, sosai Zuhra ta tsorata Salima kuwa ko a jikinta dan ba yau ta fara ganinsa ba. Bayan sun sanar dashi abinda ke tafe dashi yace suje su dawo sati na sama zaiyi ma Zuhra wanka da ruwan magani wanda da zarar sun hada ido da Abdull zai haukace ya dawo da'ita dakinta. Su kayi masa sallama suka dawo, Saloon Salima ta sauke Zuhra tayi tafiyar ta. Zuhra ta shiga a kayi mata gyran gashi bayan an gama sai gashi ta dawo fess da'ita dan dama Zuhra ba tada muni, napep ta shiga ta karasa gida dan zuwa lkcn hadari ya kan kama sosai.

_Chaiiii jiya Abdull yasha zagi gun 'yan watsapp da Telegram_ 😂🏃🏼‍♀️ _Aradu ina jin dadin comments din ku fans dan Allah kuci gaba_ 🤣❤️🙏🏼

Watsapp no. 22793414725

ONE BLOODWhere stories live. Discover now