⚡ *ONE BLOOD*⚡
_Episode 23-24_
https://www.wattpad.com/user/AbdullNuaiymerh?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
A daddafe na dawo falon na zauna da kyar dafe da marata ina tunanin me yazo da mutane irin haka gidan nan? Minti goma da zamana na fara jiyo hargagi da hayaniyar mutane a farfajiyar gidan, kasa hakura nai na saka hijab na fito cike da karfin guiwa. Cincirindon mutane ne tsaye cirko-cirko sai hayaniya da kumfar baki suke, ga wasu tsaye a daidai part din Aunty Zuhra sai kokarin janye ta suke suna kokarin shiga da amarya amma ta tsare hanyar shiga sai fixge² take tana kokarin dukan su da ta6aryar hannunta, bude gate mai gadi yayi motar Yah Abdull ta kunno kai ciki, yana yin parking ya fito a fusace fuskarsa ba walwalah yazo ya fice ta gabana ko kallon inda nake bai ba ya karasa wajen su Zuhra. Bai yi wata² ba ya janyo ta kiii ya wurgata gefe gamida yin ball da ita ya kamo hannun amaryar sa ya shigar da ita falon gamida banko kofar ya rufe da key. Ba shiri 'yan kawo amarya suka fara jan kafa suka bar gidan jiki Bbu kwari zuciyoyi Bbu dadi ya rage Aunty Zuhra kadai durkushe a tsakar gidan tana gunjin kuka "Tirkash!" Shine abinda ya fito daga bakina dan gabadaya na kasa fahimtar yanayin da nake ciki, a sanyaye na juyo zan shiga part dina na hango Aunty durkushe a farfajiyar gidan tana wani irin kuka na fitar hayyaci, tsura mata ido nayi tsawon wasu 'yan mintuna tozarcin da Yah Abdull yayi mata a gaban jama'a ya fara dawo min sai naji gabadaya ta bani tausayi na tsinci kaina da son rarrashin ta. Kasa shiga falon nayi na nufeta na durkusa gefen ta na kamo hannunta cike da tausayi, dagowa tayi tana kallona da jajayan idanunta sai kuma ta kawar da kai tana kokarin fixge hannunta daga hannuna na rike mata hannu gam! Na fara mgn. "Dan Allah ki daina kukan nan ki tashi ki koma dakin ki dare yayi ga kuma sanyi sosai a garin kar yayi miki Illah." Cikin kuka da hargagi tace "ki rabu dani Wllh Tllh sai na kashe su! Ni zataci amana? Ashe son mijina take bansani ba! Na dauki amana da yarda da duk wasu sirrikana na bata ta koma gefe tana cin dunduniyata, ashe ita din tauraruwa ce mai wutsiya biyu ban sani ba."? Sai kuma ta girgiza kai ta share hawayen fuskarta lkci daya ta kece da wata kafirar dariya tace. "Na rantse da Allah ko zanyi yawo tsirara sai na raba kowa da mijina! Abdull nawa ne ni kadai nafi karfin kishi da ko wace kucakar mace." Kasa daurewa nai na fashe da dariyar rainin hankali sosai dan Tabbas furucin ta na karshe ya bani dariya, sai da nayi mai isana sannan ta mike tsaye na dan tabe baki nace. "Tou shikenan Allah shi kyauta ni wannan fadan yafi karfi na naku ne na manya kuma kunfi kusa tunda kawar ki ce." Daga haka nayi tafiya ta nabar zaune tana surutan ta marasa kan gado. Bedroom na wuce kai tsaye sai a lkcin tunani da tsantsar mamakin Abdull ya fara kamani tagumi nayi ina tambayar kaina anya lafiyar yah Abdull kuwa? Aure! Aure fah!! Kuma ya rasa wacce zai aura sai best freind din matarsa why? Me zai da mata uku tun yanzu kuma aure haka kai tsaye ba lbr ba gayyatar 'yan uwa da abokan arziki anya mutanen gida sun san da maganar nan kuwa? Na jima sosai ina tunanin sai kuma na janyo wayata na kunna data cikin sa'a kuwa naga Leylaa a online, stiker din sallama na tura mata ba jimawa ta amsa sallamar na danna mata recoding tare da zayyano mata abubuwa na ban Al'ajabi da suke faruwa da kuma matsalolin da suke kokarin kunno kai.
Leyla dake kwance saman gadon ta lullube cikin bargo ta mike zumbur dafe da saitin kirjin ta tana ware idanu, da gudu tayi hanyar fita dakin rike da wayar ta, Saif kadai ta gani zaune a falon Bbu Mum dinta, da hannu ta yafito sa yaron ya taso da gudu yazo wurin ta tace "Mum tana dakinta ne ko ta fita"? Saif yace "tana part din Mami" Leyla bata jira karshen zancen sa ba tayi hanyar fita da gudu sai part din Mami, da sallama ta shigo ta sami Mum Fareeda da Mami suna mgn, saman kujera Leylaa ta zube tana Numfarfashi, cikin fada sosai Mum Fareeda ta fara zazzaga mata bala'in yaushe zatayi hankali Mami na bata hakuri, Leylaa ta turo baki tace "wlh Mum Abun Al'ajabi na jiyo daga bakin Nu'aiymah shiyasa kuka ganni a firgice" Mami tace "lfy wani abun ne ya faru kuma"? Kamar jira take ta kwashe komai ta samar musu har voice note din Aiymah ta kunna musu suka saurara. Ba Mami ba hatta Mum Fareeda sai da ta girgiza dan har wani zufa ne ya fara keto mata tako ina tana sallallami. Duk da Mami ta girgiza da lbrin da Leylaa ta kawo musu but fuskar ta ya shanye komai ta kasa nuna masu ainahin halin da ta take ciki, murmushin karfin hali ta saki ta juyo ta dubi Mum Tace. "Wai ke lafiyar ki kuwa? Mene abun daga hankali dan kinji ance Abdull ya kara aure kin manta cewar shi mijin mata hudu ne? Haba! Ke kuwa kina abu kamar karamar yarinya dan Allah ki daina kuyi masa addu'a sannan ai mata fatan Alhairi Allah ya tayasa riko ya hada kan matan sa ya kau da fitina a tsakanin su." Doguwar ajiyar zuciya Mum ta sauke tace. "No wlh ba abinda kike tunani bane Maryam! Kawai abin ne ya bani mamaki ace yaron nan ya kara aure bamu da lbr? Anya iyayan sa sunsan yayi wannan aure kuwa? Babban abinda ya kara daga min hankali naji ance kawar matar sa ya aura shine abun ya mugun bani mamaki, ga kuma halin ko in kula da yake nuna wa ga Nu'aiymah da wanne za taji dan Allah? Ga laulayi ga bacin rai ga kuma kishiya da rashin kulawar miji ya Rabb! Ka iya mana ka rufa mana asiri, ya ilaihi ina rokon ka da ka nuna mata karfin ikon ka da karfin mulkin ka wajen Ganar damu abinda ya shige mana duhu, Ya Allah! In ma wani mugun abu ne aka yi ma yaron nan dan gusar da tunanin sa har yake aikata abubuwa marasa kan gado Allah ka tona asirin ko waye." Mum ta karasa fada tana share kwalla Mami ta amsa da "Ameen" tana murmushi. Sallamar yah Qaseem ce ya dakatar da Mum daga surutun da take, har ya karaso ciki ya samu wuri ya zauna yana gaishe su cikin girmamawa sannan ya sanar musu da sakon Baba Shagari.
Shiru falon yayi ba ka jin komai sai karar Ac da saukewar numfarfashin ilahirin jama'ar hadaddan falon Baba shagari, Baba shagari ne tsaye hannuwansa sakale a bayan hannunsa sai zagaye falon yake, sai a sannan na karewa mutanen falon kallo. Baba shagari, Uncle Malik, Baffah, Baba Manir, Uncle Sulaiman sai su Mami da duk sauran Matan gidan da su Yah Qaseem da duk yayyan su da Mazan da mata yara ne kawai basa nan, sai Hajiya Inna dake Hakimce a saman kujera ta zuba uban tagumi 'ya'yan ta da jikokin ta sun sata a tsakiya. Bayan kowa ya gama hallarar taron meeting din gaggawar ta da aka shirya akan Abdull Baba shagari ya gyara zama sosai cikin nutsuwa ya bude taro da addu'a sannan ya fara mgn cike da dattako da tausasa harshe. "Nasan duk kunsan abinda ya taramu anan dan na tabbata kun samu lbrn abinda d'an uwanku ya aikata! Ina son kusan cewa ni bazan masa baki ba, kuma bazan masa mugun fata duk da Abdull ya nuna mana iyakar mu da har zaiyi aure farat! D'aya haka ba tare da sanin mu ba! Kar naja ku da dogon surutu inason in takaice muku cewar a bisa butulcin da Abdull yayi min, ya nuna min cewar ban isa dashi ba sannan ya wulakanta zabin da nai masa, hakika kwanaki nayi masa uzuri da yarinyar nan tayi rashin lfy har ta warke baizo dubata ba, kwatsam jiya labarin auran sa yazo kunne na a bazata, dan haka ina mai bakin cikin sanar dake cewar duk inda yake a nemo shi a kawo min shi nan gabana yau² dinnan ina bukatar ya damka min takardar Nu'aiymah a hannu na sannan abu na gaba shine babu ni babu shi yaje yayi duk abinda yaga dama." Kit kake ji Kowa ya gaza furta komai sai saka da warwara kowa yake a zuciyar sa, wasu sunyi farincikin hukuncin da Shagari ya yanke yayinda wasu su kai bakin cikin hakan, tuni Ummah ta fara matsar kwallah Mami kuwa Ajiyar zuciya ta sauke tana addu'ar Allah yasa rabuwar tasu ita ce mafi Alhairi. A zafafe Baffah ya mike tsaye ya dakatar dashi ta hanyar fadin. "Haba Shagari wannan wace irin mgn ce kake? In hankali ya gushe nutsuwa ke dawo dashi, dan Allah ka yanye kudurin ka mu bi yaron nan da addu'a maganar raba aure kuma dan Allah ka daina mu tayasu addu'ar Zaman lfy." Wani mugun kallo ya watsa masa baice komai ba yayi hanyar fita falon cikin tsananin bacin rai, haka aka watse taron zuciyoyi Bbu dadi yayinda zuciyoyin wasu suke cike taf da farinciki.
*KU GAFARCE NI FANS! NA SHIGA GASAR MARUBUTA NE SHIYASA KUKE JINA SHIRU KWANA BIYU AMMA IN SHA ALLAHU KOMAI YAZO KARSHE! GAREKU MASOYA NA FILI DA NA BOYE NA NESA DAMA NA KUSA INA MAI FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA YAU ZAKU FARA GANIN LITTAFINA NA MASSIFAFFAN KISHI* *WANDA YA KASANCE LBRIN GASA, SOYAYYAR DA ZAKU NUNA MIN ITA CE TA HANYAR YI MIN VOTING WAJEN GANIN NACI GASAR NAN, DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA SHARE DA VOTING SHINE ABINDA NAFI BUKATA IDAN HAR KUKA YI MIN WANNAN ZANYI FARINCIKI FIYE DA TUNANIN KU NI KUMA ZAN FARANTA MUKU TA HANYAR KAWO MUKU WANI SABON LITTAFI NA DANA JIMA INA DOKIN RUBUTA MUKU SHI WANDA ZAI GIRGIZA KU.!🤟🏼WANNAN ALKAWARI NA NE!!.*
*IDAN HAR KIN SHIRYA MIN VOTE DAN GIRMAN ALLAH KI TUNTUBE NI KAI TSAYE SAMAN NUMBER NAYI ADD NAKI CIKIN GROUP DIN WA ENDA ZASU MIN VOTING* 🙏🏼🥺
22793414725