ONE BLOOD

103 6 0
                                    

⚡ *ONE BLOOD* ⚡

_Mallakin Nu'aiymah Abdull Tafida_

_Book Dedicated to My Tween Sis Na'imah Abdull Tafida.😍_

_Episode 9&10_

Wani matsiyacin kallo Zuhra ta watsa mata sannan ta daga mata hannu da fadin. "Ke! Dakata marar kunya, karki ce xa kiyi man rashin kunya naci ubanki ynxun nan wlhy, ba wani abu ne ya kawo ni ba! Dama naxo ne na gargade ki akan ki fita tsakani na da mijina! Wlhy kinyi kadan kice xaki rabani da mijina tunda a tare kika ganmu, so dan haka kice da uwarki ta koma wajen bokan ta su canja wata hanyar dan wallah ni nafi karfin ku.." wata wawiyar xuciya ce ta kwashe ni jin tana Ambaton sunan mahaifiya ta a shirmen ta, a xafafe nasa hannu na wanke fuskarta da wani mahaukacin mari ina nuna ta da yatsa jikina na 6ari amma na kasa furta komai. Dafe kunci Zuhra tayi tana bin Aiymah da wani kallo na tsantsar mamaki da Al'ajab, sai kuma ta kece da wata kafirar da dariya tayo kaina gadan², duk da nasan Zuhra tafi karfi na amma karfin hali irin nawa ya hanani ko motsi har sai da ta iso daf dani, ba tayi wata² ba ta shakeni jikin bango dakin iya karfin ta gamida saka tafin hannun ta saman hanci na ta toshe ta yadda ba xanyi lumfashi ba! Tuni na fara fita hayyaci na ina kokarin 6an6are ta a jiki na amma inaa! Karfi na da nata ba daya bane. Da sallama ya shigo Falon yana kokarin hawa sama dan daukar takardun sa masu muhimmanci da ya manta, jin saukar Numfashi a bayan sa ya sashi saurin duban wajen aikuwa idonsa ya sauka a kansu, ganin Zuhra tana shirin yin kisan kai ya sashi yin tsalle daya ya iso wajen, cikin hanxari ya tunkude ta gefe ya janyo Nu'aiymah jikinsa wacce tuni ta suma. Kitchen ya nufa ya bude Frij ya dauko gorar faro ya koma inda ya barta kwance ya kwara mata ruwan hannun sa. A take na sauke wani dogon Numfashi hannu na rike da wuya na, da kyar na mike xaune ina kifta idanu gamida sauke Tagwayen ajiyar xuciya, Abdull bai kara bi takan Nu'aiymah ba ya cire bell din jikinsa yayi kan Zuhra, ganin haka tayi hanyar waje da gudu taku biyu yay ya damko ta yayi wani bal da'ita ya shiga dukanta baji ba gani tamkar an aiko sa. "Kashe ta xa kiyi? Nace kashe ta xa kiyi? Yau xan nuna maki cewa ni nake da iko da gida na shashashar banxa kawai, maxa ki fice ki bar min gida na ki tafi gidan ubanki har kiyi hankali, kuma ina mai tabbatar miki da cewa in har wani abun ya samu yarinyar mutane wallahi ki kuka da kanki tunda ke mahaukaciya ce kuma dakikiya." Wani raxanannan ihu Zuhra ta saki cikin kuka mai game da ihu take fadin. "Wallahi Bbu inda xan tafi, kayi kadan kace xaka koreni daga gidan nan Sbd shegiyar.." bata karisa ba taji yace. "Okay! Ni kuma na rantse miki da Allah kika kara minti goma a gidan nan xan nuna maki na haifu, xan warware duk wata igiyar aure na dake kanki Bbu ni Bbu ke har abada." Bata tsaya jin sauran xancen nashi ba tayi hanyar gat da gudu tana kuka dan tasan xai aikata din tunda ya furta. Bai kara bi ta kanta ba juyo inda yabar Aiymah xaune har ta mike ta dauki jakar hannunta tayi hanyar waje cikin galabaita, "ki jira ni ina xuwa." Ya fada Bbu wasa a fuskar sa, minti uku sai gashi ya sauro rike da wasu files ya dube ta yace. "Let's go." Da mamaki nabi bayan sa dan bakina ya mutu Amma fa na dau Alkawarin daukar fansa akan Zuhra, ganin yayi hanyar motar sa inda driver ke jiran sa yasa na tsaya baya ina turo baki, juyowa yay ya watsomin wani kallo yace. "So kike in dauke ki in sakaki a motar."? Baki na kuma turowa gaba ina bubbuga kafafu na kasa still banyi magana ba sai key'n mota ta da na nuna masa alamun dai a tawa motar xan tafi. Sai yanxu ya fahimci abinda take nufi dan haka ya kara juyowa a karo na biyu yace. "Kika bari na riga ki shiga motar nan xaki raina kanki." Ya fada yana bude murfin motar, da gudu na karisa motar na bude daya bangaren na shiga na rufe ina matsar kwalla, shima ya shigo ya xauna nesa dani driver yaja motar muka fice. Sai da muka biya mu kayi shopping din biscutes da shocolates, na dauki kalar turaruka na da mayuka na masu kamshi, cike da mugunta nayi ta daukar Kayayyaki har da wanda bana bukata dan kawai yayi min magana amma naga ko kallo na baiyi ba yana tsaye yana danna waya, baki na ta6e ganin ina neman yin late yasa na dauko kayan na jibge aka kirga ya biye security's din suka kaisu mota. Tun a mota na dauki wasu chocolates da biscuites na saka a jaka na har muka iso gidan, maimakon su ajiye ni bakin gat din makarantar sai suka shigo dani har harabar makarantar inda dalibai suke ta kaiwa da komowa, harga Allah banji dadi ba dan ni na tsani kallo, hararar sa kawai nake ta kasan ido har driver yay parking nasa hannu da zimmar fitowa yasa yatsanshi ya bugemin baki nasa kuka nace. "Ban yafe ba." Dan nasan baxai yimin komai ba tunda driver yana motar. "Musa kaje waje ka jira ni ina xuwa." Manya fararan idanuna na waro waje nace. "Uhm Yah Abdull ni xan karisa ciki Allah ya tsare hanya." Na fada ina yin narai² da idanu, Tabbas! Ta bashi dariya ita ga shegen rashin kunya tsoro kamar farar kura, kwafa yay yace."dawa kike."? Da sauri nace. "Na rantse wasa nake." "Ni abokin wasan ki ne."? "A'a yi hakuri baxan kara ba, kuma dan Allah inason yau inje gida please Bro." Na karashe hawaye na sauka a idona. "Baxa kije ba, bacemin da gani ina sauri." A sanyaye na bude murfin mota ina share kwalla naci yace. "Idan kin gama kiyi min text xan sa Musa yaxo daukar ki." Bance masa komai ba na fice daga motar dan haushin sa nake ji. Tunda Nu'aiymah ta fito motar idanun mutane su kayo caa! A kanta dan tunda dalleliyar motar su ta tsaya suke tsumayen jiran fitowar na ciki. Tsaki naja ciki² ganin yadda suke kallona na karisa kofar classe dinmu na xauna kusa da Freinds dina muna gaisawa. Sai karfe uku muka fito daga Lectures, tun A class nai masa text ina fitowa kuwa na samu Musa driver yana jira na a harabar makarantar. Na karisa na shiga motar muka muka bar harabar gidan, ga mamaki na sai naga ya nufi hanyar Family house din mu dani, baki na ta6e na kwantar da kaina na lumshe idanu, horn din da Musa driver ya fara yi a bakin tangamemen kofar gat din Gidan mu ne yasa na bude idanu ina murmushi, yana yin parking na fito da gudu na nufi sashen mu cike da tsantsar farinciki, karo mu kayi da Leyla ta fito daga part din rike da plate, tana gani na ta kama ha6a tace. "Ikon Allah meye haka Aiymah wai ke kam yaushe xaki nutsu."? Hararar ta nayi ina kai mata duka a baya ta goce tana dariya, nima dariyar nayi naja hannun ta muka karisa cikin falon. Xaune muka samu Mami a falo tana waya ga wasu uban takardu a gabanta tana aiki wanda ya shafi Hospital din su. Ban damu ba da gudu na fada jikinta ina kiran sunan ta, a dai-dai Time din ta gama wayar ta dago tana duba na tace. "Wai dan Allah yaushe xa kiyi hankali? Kin shigo min falo xugum² Bbu sallama." Ta karashe maganar tana girgixa kai. "Haba Mami na wlhy duk murnar ganin ki ne I'm sorry kinji baxan kara ba." Na fada cikin marairaice fuska, murmushi tayi tana shafa kaina tace. "Ohk naji, ina my son." Fuska na yamutsa nace. "Yana wajen aiki ni daga school nake." "Kin sanar masa xa kixo."? A takaice nace mata. "Eh driver ne ma ya kawo ni." Ta jinjina kai nace. "Ina su Tweens."? "Sun wuce Slamiyya." Ta fada ba tare da ta dago ba ta cigaba da aikin da take, abin nan nata yana bani haushi kwata² bama fira da'ita a cewarta wai nice 'yarta ta fari na rasa yaushe Mami xata daina wannan kauyancin ta fuskanci cewa ynxu fah duniya ta canja, ga ilimi na boko ta yishi kamar ba gobe dan Babbar likitar mata ce amma Akwai wannan kunya tasu na Asalin fulani, jin shirun yayi yawa can nace. "Mami hira fah naxo muyi dake." Na fada ina turo baki. "Kinga ni banason rigimar nan taki ki fada ina sauraron ki, kuma maxa ki fice kije ki gaida sauran Baffan nin ki da matan su, amma ki fara xuwa bangaren Inna tun kafin ki ganta nan ni banason rigima." "Tou naji xanje amma dan Allah kice ma Son dinki ya canja mana gida ni da Aunty Zuhra wlhy ni bana son ina rigima da'ita ko ba komai ni naxo na sameta a gidan suna xaman su, wlhy Mami daxu da safe fah Sbd ni ya kora ta gidan su." Cikin Tashin hankali Mami ta ajiye biron hannun ta ta fuskancin 'yarta ta.sosai tace. "Meya hadaki da'ita har ya aikata wannan danyen aiki gareta Inji dai bai furta kalmar saki a kanta ba koh."? "A'a bai furta ba." Mami ta sauke ajiyar xuciya tace. "Meyasa bakya jin magana ta? Uban mi ya kai ki shiga sabgar ta har wani rikici ya bullo a tsakanin ku? Haka kika ga ina xaune da mutanen gidan nan?." Girgixa kai na shiga yi ina hawaye dan nasan na 6ata mata rai, duk da nasan ina da massifa amma bana fada sai da dalili, ni kaina bansan halin wa na biyo ba dan Mami mace ce mai hakuri da kawaici uwa uba kunya, da kyar na fixgo maganar a bakina nace. "Mami ki fahimce ni ai kema kinsan bana fada sai da dalili ita da kanta taxo ta sameni har part dina tana xagina, dalilin da yasa na tanka mata jin ta ambato sunanki a shirmen ta ni kuma baxan iya jure hakan ba." "Kin cika rigima Nu'aiymah, bai kamata ki tanka mata idan ta gaji ai xata daina, ynxu idan Hajiya Ummah taji maganar nan me kike tunanin xai faru." Cikin kuka nace. "No! Baxan iya jurewa ba, baxan tsaya wata banxa ta xagi mahaifiya ta xuciya ba tada kashi Mami, amma kiyi hakuri baxan sake ba ki lallabe sa ya dawo da'ita sannan ya raba mana gida please." Na fada cikin kuka sosai, Mami ta jawo ni jikinta tana bubbuga baya na har na daina kukan sai Ajiyar xuciya nake saukewa. A haka Noor da Saifudeen suka dawo daga Slamiyya suka same mu, rungume ni sukayi suna oyoyo Aunty Nu'aiymah munyi kewarki, rungume yaran nima nayi ina shafa kansu na bude jakata na ciro biscutes da chocolates masu yawa na basu yaran suka fara tsallan murna, Mami ta juyo ta kalleni tace. "Yarinyar nan bakida man kai wato har ynxu baki daina shan kayan xaki ba koh? Na tabbata Son baisan kina sha ba a boye kike siyan su." Ta fada tana kwace sauran, baki na turo gaba nace. "Tou ai shi ya siya min." "Okay! Ai xai dawo ya same ni." Daga haka bata kara ce min komai ba, nima nayi kwanciya ta saman kujerar ina turo baki gaba daga haka bacci ya kwashe ni, ban farka ba sai karfe biyar na yamma, Bbu kowa a falon sai Leyla da maryam ina tashi suka hau tsokana, murmushi nayi nace musu ina xuwa na shige tsohon dakina nayi wanka na fito na shige kitchen na xubo abinci na dawo falon inaci muna 'yar firar yaushe gamo, a tare muka dunguma muka xuwa gaida sauran mutanen gidan da banyi ba, yau ma kamar kullum Bbu wata gaisuwar kirki haka kanninsa Nasreen da Hadija wa'yan da suka hau xugin da uwar take musu suka xauna akai, baki na ta6e bayan fitowar mu, a karshe muka yada xango a falon Inna itama tana tamin tsiyar wai tun daxu ina gidan nan amma banxo gaishe ta ba wai Mami tana son rabani da'ita, 'yar dariya nayi nace. "Nifa haushin ki nakeji Inna tun ranar nan da kika xuga yah Abdull ya hanani kwana a gidan nan, amma ynxu in kinason mu shirya to ki bani dambun nama." Ta ta6e baki tace baxata bayar ba kuma mu fice mata daga daki ai dama tasan ba abun arxiki muka xo yi mata ba, nida Leyla muka shige har dakin ta muka fara laluban inda xamu samo danbun nama, ita kuma tana aikin xagin mu. Ban baro gida ba sai bayan Isha yaxo dauka ta muka tafi...Tunda Zuhra ta fito gidan take kuka Bbu ko Takalmi a jikinta, kallon ta kawai mutane suke cike da tausayi dan sunyi tunanin mahaukaciya ce, masu mata dariya nayi masu mata addu'ar samun sauki nayi har ta iso bakin Titi tana neman Abun hawa. Tana tsaye motar Abdull taxo ta fice ta gabanta, ba tayi wata² ba tabi motar da gudu ta laulayo ashar ta maka masa tana fadin sai taga bayan su, da kyar ta hakura ta tsaya gefen wani shago ta xauna jiran Abun hawa, kusan few minute kuwa sai ga wani mai napep tayi tsalle ta shige tayi masa kwatancen unguwar su, a napep din ma xai xage² take tana fadin sai taci abu kaxar ubansu Abdull da Nu'aiymah, sai taci mutuncin su sai ta sa sun xubar da hawaye fiye da wanda ta xubar. Girgixa kai kawai mai Napep din yay dan ya fahimci ba tada man kai, addu'a kawai yake Allah yasa su rabi lafiya da'ita, suna iso kofar gidan nasu ta sallami mai napep ta shige gidan a fujajan.....✍🏻

_Watsapp no._ 22793414725

ONE BLOODWhere stories live. Discover now