*ONE BLOOD*
_27-28_ ✍🏼
dare ya tsala sosai, bakajin komai sai kukan karnuwa da na tsuntsaye, gudu nake cikin tsananin fitar hayyaci da tarin damuwa, jini ne kebin ƙafafuna har yanzu, gashin kaina duk a barbaje, zuwa lkcn hatta takalman ƙafata nayar dasu, har na iso bakin titin ban tsakaita da gudun nake kuma bansan inda nake cilla ƙafata ba, burina shine kawai nai nesa da duniyar da na fito, nai nesa da ahalina da duk wani makusanci na. gudu yake sharawa saman titin cike da ɗokin ƙarasawa inda yake buƙatar zuwa, na bayansa hakimce cikin wata dakakkiyar shadda ruwan zuma fuskarsa cike da tarin damuwa, time to time yake kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa sannan ya kalli driven ya umarce sa da ƙara gudun motar, shekarunsa baza su gasa talatin a duniya ba, kyakkyawa ne dan bashida wata makusa a jikinsa, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba zamu iya kiransa chocolate color, duk da fuskarsa na ɗauke da matsananciyar damuwa hakan bai ɓoye tarin kamalarsa da cikar haibar sa ba, zazzafar iskar bakinsa ya furzar ya kwantar da kansa saman kujerar motar dafe da kansa dake masa ciwo kaɗan-kaɗan. hannunsa ya ɗago a karo na ba adadi da niyyar kallon agogon hannunsa yaji motar dasu tayi wani ƙiiii! alamun sunyi karo da wani abun ko sun bugi wani. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" faɗin mutumin kenan yana dafe kansa da yayi wata irin sarawa da gabansa da yayi wani irin mummunan faɗuwa. da taimakon Allah driven yayi saurin riƙe birgin motar shima yana salati kafin ya fito daga motar a hanzarce ya ƙarasa gaban motar su da yake hango mutum kwance cikin jini.
Ganin mace ce yasa driver saurin komawa gun motar su ya buɗewa mai gidan nasa bayan yayi masa bayanin komai, cikin tsananin tashin hankalin ƙaddarar da ta kuma afka masa ya fito yabi bayan driven nasa gabansa na tsananta bugu. tun kafin su ƙarasa idonsa ya sauka saman matashiyar yarinyar da shekarunta baza su wuce 20years ba kwance jikin jina-jina, gashin kanta duk ya rufe mata fuska amma hakan bai hanasa ƙare mata kallo ba. bai tsaya barin abinda ke tsirga masa yayi tasiri a kansa ba ya umarci driven da ya ɗauke ta su wuce hospital dan tana cikin mawuyacin hali daga haka ya koma motar gabansa na tsananta bugu. mintuna sha biyar suka ƙarasa wata prvt hospital dake kusa suka damƙa ta a hannun likitocin dan ceto rayuwar ta, mota ya koma yayi zamansa, ya jima sosai yana tunani sannan yayi dialing wata number ya kai kunnensa, banji abinda ya faɗa ba har sukayi sallama ya mayar da wayarsa a Aljihu ya fito ya tsaya a bakin motar hannayensa harɗe a ƙirjinsa. mintuna goma da tsaiyuwarsa wata mota tayi parking a gabansa, mutunan ciki ya fito ya ƙaraso wajensa suka sakar ma juna murmushi sannan sukayi musabaha suna ƙara gaisawa, Sultan ya gyara tsaiyuwarsa jikin motar ya dubi abokin nasa yace "Aliyu ka kirani kace kana buƙatar gani na, muryar ka kaɗai da naji ya tabbatar min da bbu lfy sai kuma gashi na sameka a asibiti don Allah meke faruwa naga yanayin ka a haka" Aliyu ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa ya zaiyane masa komai ya ɗora da faɗin "na rasa wace irin sabuwar massifa da mummunan ƙaddara ce take ƙoƙorin kunno kai a rayuwa ta, wacce nake ciki kaɗai ma ta isheni, Sultan bansan ta ba! bansan daga wace duniyar ta fito ba! ƙaddarar rayuwa ce ta haɗani da ita a daren jiya"
Sultan yay tsai yana sauraronsa har ya gama koro masa bayani, shiru duk su ka yi tsawon mintuna uku sannan Sultan ya soma magana cike da Alhini "danƙari! yanzu ina yarinyar take"? Aliyu na shirin bashi amsa sukaga driver ya nufo su, gaishe su yayi cike da girmamawa sannan yace "doctor yace ka shigo yana buƙatar ganin ka" duk suka jinjina masa kai yayi gaba suna biye dashi, har office ɗin doctor ɗin wata nurse tayi musu jagora, yana ƴan rubuce-rubucensa suka shigo, ya ɗago ya basu hannu suka gaisa sannan suka zauna saman kujerar dake facing ɗinsa, doctor yayi gyaran murya yace "inason sanin menene alaƙarka da wannan yarinyar" doctor ya faɗa cike da tuhuma, wani mugun kallo Aliyu ya watsa masa yace "me kake tunani? ince dai tun farko na gaya maka driver na ne ya buge ta da mota so yanzu banason ƙananan maganganu ka faɗamin idan ta farka zan je in ɗauke ta in sadata ga ahalinta tunda ni ban ma taɓa ganin ta ba tsautsayi ne ya haɗani da ita" ya ƙarasa faɗa fuskarsa na nuna zallar ɓacin rai, Sultan ya fara bashi haƙuri doctor ɗin kuma yace "no wlh ba haka nake nufi ba kayi haƙuri in tambayar ta maka zafi but ka sani ina kan aiki na ne, sannan kuma yarinyar tana ɗauke da ciki na kimanin wata biyu, cikin yaso salwanta da ƙƴar da siɗin goshi muka ceto rayuwar babyn amma fah har yanzu ita bata dawowa daidai, ta farfaɗo amma munyi mata allurar bacci dan ta ƙara samun hutu yanzu da zarar ta farfaɗo zaku iya tafiya da ita sai aci gaba da bata kulawar da ta dace" cikin marairaicewar fuska Aliyu yace "to ni ina zan kaita? hasalima ni ba mazauni bane ina kuke son in tafi da ita? gaskiya ni dai kawai zan jira ta farfaɗo ta gayamin da bakin ta inda ta fito" Sultan ya jinjina kai yace "yanzu haka ma ƴar garin nan ce, gwara ka kaita inda ta fito a rabu lafiya dan kasan matsalar gidan ku da ta gidan ka" Aliyu yace "ka bari kawai wlh, mai ɗaki shi kaɗai yasan inda ke masa yoyo, Allah sa mu dace" Sultan ya amsa da Ameen a daidai time ɗin da suka fice daga office ɗin doctor.
Misalin ƙarfe biyar na yamma na farka na tsinci kaina a gadon asibiti, tun ina ganin dishi-dishi har na fara ganin normal, cike da mamakin meya fito dani gida na miƙe daga kwancen ina bin ko ina da kallo hakan yayi daidai da shigowar wata mata, da kallo na bita har ta ƙaraso kan gadon da nake ta kamo hannuta leɓɓanta na motsi sai dai na kasa jin abinda take faɗa balle na fahimta, kallon ta kawai nake tamkar wata sakara cike da tarin damuwa da tambayoyin da bansan adadin su ba. tunda nurse ta shigo ta kamo hannun Nu'aiymah ta fara mata mgn cikin kulawa "ya jikin naki kinji sauƙi ko?" ganin taƙi mgn tana kallon ta nurse ta ƙara faɗin "tou ina ke maki ciwo"? nan ma taji shiru, haka taci gaba da jera mata tambayoyi amma ta kasa faɗan komai amma lips ɗin ta na motsi alamun tanason yin maganar amma ta kasa kuma har yanzu bata daina kallon ta ba tana hawaye ta riƙe mata hannu gam, fuska ɗauke da damuwa nurse ɗin ta fara ɓanɓare hannunta daga na Nu'aiymah dan ta fahimci akwai babbar matsala tattare da kyakkyawar yarinyar, da ƙyar tayi nasarar ƙwatar hannunta ta fice da sauri dan sanarwa doctor, sai girgiza mata kai Aiymah take alamun kar ta tafi ta barta. zata shiga office ɗin su Aliyu suka fito ta dube su tace "marar lafiyar ta farfaɗo amma fah akwai matsala ku yima doctor mgn yazo ya duba ta. a hanzarce Sultan ya koma ya sanar masa suka fito a tare gabaɗayansa suka ɗunguma zuwa ɗakin da aka kwantar da Nu'aiymah.
Tun bayan fitar Nu'aiymah daga gidan Mami take kiran wayar ta amma swich off, tun tana ɓoye damuwar ta har ta kasa ta samu Mum Fareedah a part ɗin ta ta buƙaci ta kira mata *AIYMAH* dan tayi tunanin tayi mata fushi ne shisa taƙi picking ɗin calls ɗinta, Mum Fareeda ma tayi ta kiran wayar amma bbu Amsa haka ma Leyla da Fareedah har da Yah Qaseem da Salim, tun ƴan uwan nata na ƙoƙarin ɓoye damuwar su har rana tayi sosai, ganin bbu wani lbr Qaseem da Salim sukaje gidan dan duba lafiya taƙi ɗaga wayar kuma tana ring ɗagawa ne kawai ba Tayi, suma tun rana da suka bar gidan basu dawo sun gaya masu halin da suka sami Nu'aiymar ba kuma ba'a samun wayar su biyun duka. zuwa yanzu kam haƙurin Mum da Mami ya fara ƙarewa shisa suka je suka sami Inna suka sanar mata, itama hankalin ta a tashe taje ta sami su Baffah ta sanar masu halin da ake ciki.
Misalin ƙarfe biyar na yamma, cincirindon ƴan sanda ne zagaye da gidan Abdull, fuskar ko wane ɗan uwanta ka kalla zaka hango tsananin tashin hankali da kiɗimar da suke ciki, masu raunin zuƙata tuni suka fara zubar da hawaye, Qaseem ne tsaye kan komai saɓanin Abdull da ya leƙo so ɗaya ya koma ciki abinsa, Acp ya dubi Baba mai gadi da kyau yace "kana ɓatamin lkc Baba, ya kamata ka nutsu kai min bayani yadda ya kamata tun kafin muje offise, Baba mai gadi ya sharce gumin da ya tsatstsafo masa, da zarar ya tuna gargaɗin da Salima tai masa jiya daddare sai yaji hantar cikinsa ta kaɗa, shi dai tabbas an shiga rayuwarsa kuma sun saka shi a tsaka mai wuya, amma ya zaiyi dole ya fito ya sanar masu gaskiyar abinda ya sani da kuma abinda kunnuwansa suka jiyo masa "ranka ya daɗe kai haƙuri zan sanar maka" faɗin mai gadi yana sunkuyar da kai ƙasa jikinsa na tsuma, a fusace Acp ya ɗaga gudumar hannunsa ya buga ta ƙasa da ƙarfin tsiya, hakan da yayi ba ƙaramin ƙara gigita mai yayi ba, cikin sarƙewar harshe yace "ni dai bansan komai ba dangane da ɓacewar matar gidan, abinda na sani kawai shine jiya na fito zan tafi masallacin magrib muka haɗu da ita a bakin ƙofa ta fito a napep tana kuka sosai dan bbu ko takalma a jikinta, naso tambayar ta ko lfy sai kuma nai shiru da bakina dan a yanayin dana ganta bana tunanin zata tsaya ta saurare ni balle ta bani amsa, ban dawo gida ba sai bayan isha, ina tura ƙofar na jiyo muryar amarya nama mai aikin ita hajiyar da ta ɓata mgn akan tayi nesa da gidan nan kar ta kuskura ta faɗawa kowa abinda ta gani, maganganunta sun tsorata ni sosai naƙi fitowa a inda na maƙale har Larai mai aiki tayi tafiyar ta tana kuka sannan na fito sai na samu hajiyar a tsaye tana jiran fitowa ta ashe ta ganni tunda na shigo, tou nima dai tayi min gargaɗi mai rikitarwa muddun na saki na faɗi wannan maganar yanzu ma dan yana kai ne shisa na gaya maka, amma dan girman Allah ku taimaka ku nisanta ni da gidan nan bayan ƙurar nan ta lafa" cike da tausayin tsohon Acp ya sauke ajiyar zuciya yaci gaba da faɗin "a wane lkc ita Larai ta fara aiki a gidan nan? yaushe mai gidan nan ya ƙaro aure? ita matar ƴar gidan waye? ina buƙatar waƴan nan amsoshin nan zuwa gobe sannan ina buƙatar ku kamo amaryar ku kai mana ita offise dan akwai tarin amsoshin da muke buƙata" faɗin Acp kenan yana kallon abokanan aikin nasa, ɗaya daga ciki ne ya ɗaga hannu alamun yana da mgn, aka bashi dama yace "yallaɓai kar ka manta fah shi kanshi mai gidan nan babban jami'in ɗan sandar farin kaya ne, to naga ya banzantar da batun sai kace ba matsalar gidan sa bace, hasalima ɗazu ce mana yayi shi matar sa bata wani ɓata ba tunda yasan inda take dan haka mu fice masa daga gida, to yallaɓai sai nake ganin..." tsawar da babban cikin su ya daka masa ne ya dakatar dashi yayi ɓam da bakinsa, daga nan suka ci gaba da tattaunawa yadda zasu kamo bakin zaren dan sun sami hanyoyi da dama masu ɓillewa. A tare suka tura ƙofar ɗakin da Aiymah take, zumbur ta ɗago tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, ganin bbu nurse ɗin da ta shigo ɗazu a cikin su yasa ta ɓata fuska tana turo baki gamida kawar da kanta gefe tayi tamkar bata gansu ba tana zumɓuro baki