*ONE BLOOD*
*@Wattpad AbdullNu'aiymerh*
_Episode 41-42_✍🏽
https://www.wattpad.com/1115555552?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AbdullNuaiymerh&wp_originator=GZaTKERMmlyI7IVWlqK12p%2F9f%2B3td7jeBOARtLS0A6wfu9Q%2BgVcuyndOSEA7hlcRalXfHDawlFmKwNBBLIX%2F74hIogLjN3Dd67kjyQ%2Fu5fzqqHOQKj6x2I3CIUqTde4qA mugun firgice na farka daga nauyayyan baccin dana lula mai nisan zango wanda bansan iya adadin lkcn da na ɗeba ina yinsa ba, gumi ne karyomin tako wane lungu da saƙo na jikina, sai yanzu na samu ƙarewa falon da mutanan ciki kallo, a tsorace na miƙe tsaye na farayin baya-baya dan ban gane fuskokin mutanen falon ba! cikin zafin Nama Ammi ta kamo hannun Nu'aiymah ganin tana ƙoƙarin ficewa daga falon, saman kujera ta zaunar da ita tace "ki nutsu mana ina zaki je"? cikin kuka sosai na fara ƙoƙarin fixge hannuna daga hannun matar da yau ne farkon ganin da nai mata a rayuwata kai ba ita kaɗai ba hatta mutanen falon baki ɗaya bansan kowa cikinsu ba, Mlm yayi wani murmushi irin nasu na manya yace da Ammi "ƙyaleta ta faɗa mana inda za ta je" ba musu Ammi ta saki hannunta ta samu wuri ta zauna tamkar yadda Aliyu da Yasmine ke zaune suna kallon ikon Allah, "oya faɗa mana ina zaki kuma daga ina kike kuma ƴar gidan wacece ke! ina nufin sunan mahaifin ki" duk a lkc ɗaya Mlm ya jero mata waƴan nan tambayoyin yana kafeta da idanu, kawar da kai nai gefe dan sosai Malamin yayi min kwarjini, a hankali na kai hannu saman matashin cikina ina shafawa, idanu na lumshe inajin wani sanyi na ratsani jin yana nan shi ba'a cutar dashi ba, lkc ɗaya kuma na waro idanu na sauke su akan Mlm, cikin nauyin baki nace "ina son naga Mami na ne dan Allah ku kai wajen ta kar ku kaini gidan Yaya Abdull wlh mugu ne dashi da matar sa kashe ni suke son yi" na ƙarasa faɗa cikin gunji kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, a hankali na zame na zauna ƙasan kujera dafe da saitin ƙirjina dake min wani irin zafi da raɗaɗi, na haɗe kaina da guiwa ina sauke ajiyar zuciya Still hawaye basu daina sintiri a fuskata. kallon ta kawai suke cike da tausayi da mamakin kalaman ta, ganin ta fara tari Aliyu ya miƙe ya buɗe ɗan ƙaramin frij ɗin dake falo ya ɗauko gorar faro da cup ya dawo ya ɗurƙusa gefen ta ya tsiyaya mata ruwan ya meƙo mata, da ido nabi hannun dake miƙo min ruwa har na ɗago gabaɗaya na sauke su akan fuskarsa, a mugun razane nai baya har ina ƙoƙarin buge kaina da kujera, cikin tsantsar mamaki da Al'ajab nace "yaya Qaseem!" sai kuma na girgiza kai bayan na ƙarewa wannan na gabana kallo, yafi Qaseem tsayi da ɗan duhun fata dan shi ya Qaseem fari ne tass! kamar ni, wannan kuma dake tsaye gabana zamu iya kiran hasken fatar sa da chocolate color banda wannan komai nasu iri ɗaya ne hatta idanun su da hancin su, sai kuma kamannin Baba Shagari dana fara tsinkayowa tattare dashi kaɗan-kaɗan wanda hakan ya ƙara ruɗar dani sosai, duk da nasan ni ɗin ƴar dangi ce ban taɓa ganin waƴan nan mutanen a cikin ahalina ba, cikin rawar baki nace "please su waye ku dan Allah"? Ammi ta sauke doguwar ajiyar zuciya bayan ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, Mlm ya miƙe yayi musu sallama yayi tafiyar sa, suka tsaya suna kallon-kallo a tsakanin su, Ammi ta ƙaraso ta rungume Aiymah a jikinta tana goge ƙwallah, few minutes kuma ta ɗago tace "ko ban tambaye ki ba nasan daga tsatson maragayi tsoho Sulaiman kika fito, ko ki kasance ƴar Shagari ko ƴar Abdallah(Baffah) saboda kaff yaran Mlm Sulaiman tsoho Shagari da Abdallah su ke matuƙar kama, ni kuma tun ranar da ɗana Aliyu ya kawoki garemu na fara hango tarin kamar ki da wannan ahalin, nasan duk za kuyi mamakin meya haɗani da wannan ahalin ko"? da sauri na gyaɗa mata kai nace "eh Tabbas! Baffah shine mahaifina Shagari kuma yayansa, amma dan Allah su waye ku ni ban sanku ba and ban ma taɓa ganin ku ba sai yau" Ammi tayi murmushin da yafi kuka ciwo duk ku samu wuri ku zauna zan faɗa muku komai kuma zan warware muku dangantakar dake tsakaninku da Aliyu" ta faɗa tana nuna Aliyu dake zaune saman kujerar dake facing ɗinsu yana sauraron su, sake kallonsa nai ina ƙara tambayar kaina meya kawoni wajen mutanen nan? a ina na baro dangina kuma a ina ne nan? but duk banida mai bani amsar tarin tambayoyin da nake dasu, Ammi ta ƙara gyara zama sosai tace.