55-56

58 7 0
                                    

*ONE BLOOD*

*55-56*

*Not Editing*

_Ya Allah Kai ne mafi tausayin masu tausayi, mafi karamcin masu karamci, Ya Allah don tausayin nan naka gare mu ka kyautata rayuwarmu, ka ji kanmu duniya da lahira, Ya Allah Ka kiyashe mu daga zafin fitar rai, da azabar kabari da kuma mummunar makoma. Don karamcin nan naka Ya Allah ka bamu mafi kyawu a duniya da lahira, Ya Allah Ka kiyaye mu daga sharrin masu sharri, Allah ya bamu albarkar da yake cikin rayuwar mu na duniya da lahira Alfarmar shugaba (S.A.W). Ameen Barkan mu da wanda rana mai tarin daraja da Ni'imomi Fans, ina godiya da Addu'oin ku da comments._

_Garaɓasa!! Garaɓasa!! wata miyar sai a maƙota Tabbas! ƴar uwa karki bari ayi wannan tafiyar babu ke! a cikin Littafin *SIRRIN MU* tafiya ce mai nisan zango mai shimfiɗe da tabarmar ƙaya da ruguntsumi wanda ni karan kaina bansan yadda zan fahimtar daku irin tarin baiwa da fasahar da Marubuciyar ta zuba a cikin ƙayataccen wannan Littafi, so a hanzarta a kakkaɓi zani a biya kuɗin Littafin *Sirrin mu*  domin ganewa idonki ƙarshen sarƙaƙiyar dake ƙunshe a cikin wannan lbrn,_ _Idan soyayyar *Moon*  da *Deen* na birgeka to tabbas ba kaga komai idan baka karanta SIRRIN MU💋❤️ daga jin sunan kasa akwai zanba cikin aminci kada kai ƙasa a guiwa domin mallakar naka akan 300 tarayyya mai ban mamaki suna aikata abu ba tare da sanin muhimman alaƙar dake tsakaninsu ba, koda ya yaushe ya hjyarsa ta ratsa jikinta yana jinsa wani nada ban da sauran mazan,amma mene yasa baya iya gane abinda yake ba dai-dai ba ne??? Uhmmmm tashin hankalin an sauya mata fuska zuwa wata daman a yayinda da yake mata kallon biri ita kuma take masa kallon... Ya kusance ta alhalin ita ɗin like mother take a wajansa kai SIRRIN MU daban yake ysin kada kuyi missed posting kullum babu fashi it's 300 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 ga ƴan Niger 84506476 idan ta bank zaka tura 300 idan airtime ne 400_

Idanu duk muka zaro a tare lkcn da mu ka yi ido huɗu da Anty Zuhra, nayi saurin ɗauke kaina tare da ƙoƙarin barin wajen jin wani abu na taso min, cikin zafin nama ta riƙo hijabina tana ƙoƙarin tsaidani, a fusace na fizge nayi gaba abuna ina jin Leila na bata haƙuri sannan itama ta biyo bayana, kasa haƙura Zuhra tayi tabi bayan su cikin sassarfa amma kafin ta ƙarasa har sun shige fasalin su kuma ta rasa ainahin inda suka shige a taƙaice dai sun ɓace mata, ƙarfe sha ɗaya muka taso ban tsaya jiran Leila ba na kamo hanyar gida cike da takaici abubuwa dadama da suka wuce suna ƙoƙarin taso min, ina tafe ina goge ƙwalla har na iso ƙofar gida, kamar a mafarki na hangosu tsaye su uku su maza biyu da mace guda duk cikin uniform ɗinsu na aiki suna mgn, macen dake tsaye a gefensa sai wani iyayi take tana kwarkwasa shi kuwa ya fuske fuska ba walwala yake duba files ɗin hannunsa, wani wawan tsaki naja ciki-ciki a daidai sa'ilin da nazo shiga cikin gidan nai wuff! na shige ba tare da na bari sun ganni ba, juyowa duk su ka yi dan tabbas! sunji an tsaki amma gashi wayam ba kowa, basarwa su ka yi suka cigaba da abinda suke, Amanda kuwa sai wani rausaya take duk dan ta burge Abdull abinda bata saniba shine bai ma san tana yi dan shi abinda ya damesa daban!. ni kuwa ina wuce su da ƙyar na iya kai kaina ɓangaren Inna, da sallama ciki-ciki na shigo na zube saman kujerar, tana zaune tana cin dambu tana ganin na shigo ta rufe kwanan ta ture gefe ta fara sababi "ya ya wannan kuma wane irin sabon salon iskanci ne haka za'a shigo min ɗaki bbu sallama tsakani da Allah ana shiga haƙƙina a gidan wannan sam ba tarbiyya bace, in ma ƙamshin dambun nan da kikaga inaci ne ya shigo dake kima koma wllh dan bazaki ci ba, sirikar ƙawata ta kawo min ke kuwa tunda aka kaiki gidan miji ko ɗan kofin shayi baki taɓa kawo min ba a matsayi na kakarki haka ma mijin ki na jima ban gansa ba ma balle naci kuɗinsa kai hatta uwarki an kusa sati banga kwanon abincinta a ɓangaren nan dan haka ki maida zalamarki dan bazan bayar ba" duk maganganun da take ɗaiɗaiku kawai na iya fahimta dan abinda ya dameni daban amma take ƙoƙarin fassarani, kukan da ni kaina bansan dalili ba na fashe dashi harda shashsheƙa, ina jin Inna ta rafka salati tana surutai tana faɗin ita bata min komai ba sharri nakeson mata,surutan ta ne suke ƙoƙarin haifo min da wani sabon ciwon kai, na miƙe da ƙyar riƙe da hijabi na a hannu nai ficewata, a daddafe na ƙarasa part ɗin mu sakamakon jirin dake ƙoƙarin kwasata. Allah ya taimake ni bbu kowa a falon sai Hadiza mai aiki dake kaiwa da komowa tana aikace-aikacen Papi na goye a bayanta yayi bacci, nasan Mami tana aiki su Noor kuma sun fice school shisa ban tambayi kowa ba na wuce ɗakina, ina shiga na murza key na faɗa kan gado gamida sakin wani mahaukacin kuka wiwi ko zanji daɗin abinda ya tokare min maƙoshi. ko da su ka yi sallama da abokansa cikin ya komo dan yana buƙatar hutu a yanzu, kusan 10 minutes yana tsaye a harabar gidan yana son ganin ta inda zata ɓullowa, har ya ƙaraci tsaiyuwarsa bbu ko alamarta, jiki a sanyaye yaja ƙafafu ya shige sashen su, Ummah da Khadija ne kaɗai zaune suna kallo, yana ƙoƙarin hawa sama ta dakatar dashi da faɗin "daga zuwan ka har ka fara yawo ko hutawa bakayi ba? and kuma ina zaka ga abinci nan an shirya maka" gefen fuskarsa ya shafa yana murmushi yace "bbu inda naje mun tsaya mgn da su Abbas ne, abinci kuma zanci anjima nafi buƙatar hutun a yanzu" baki kawai Umma ta taɓe taci gaba da kallonta shi kuwa ya haye sama cikin sauri-sauri har yana haɗa steps ɗin da bibbiyu sai kuwa ƙarar footsteps ɗin da ya karaɗe tangamemen falon, gefen gado shima ya zauna ya dafe kansa dake barazanar tarwatsewa da hannu biyu, a halin yanzu bbu abinda yake buƙatar gani kamar ita da yaron shi, kowa na gidan yazo masa sannu da zuwa da fatan Alkhairin nasarar da suka samo shi da abokan tafiyarsu amma banda ita, why yarinyar nan taƙi yafe masa? shin ita wace irin baƙar zuciya ce da'ita har haka da bata yafiya? ubangijin da ya halicce mu ma sau dayawa mu kan masa laifi ya kan yafe mana tou ita meyasa ta kasa fahumtar cewa duk abinda yayi mata cikin gushewar hayyaci ne, shi kam Allah ya jarabcesa da so da ƙaunar ta wanda shi kansa baisan yadda zai kwatanta mata ba, amma taƙi ko saurarensa balle ya samu damar fallasa mata sirrin Zuciyarsa, har yanzu baya tunanin zai iya yafe ma Zuhra da Salima, domin kusan duk halin da ya tsinci kansa a ciki sune sila, addu'arsa a kullum itace in har akwai Alkhairi a komensa da Nu'aiyma to Allah ya taƙaice masa wahala yayi gaggawar shawo masa kanta ta karɓi soyayyarsa, in kuma bbu Alkhairi Allah ya zaɓa masu abinda yafi Alkhairi a rayuwarsu ya kuma cire masa Massifaffiyar ƙaunarta dake nuƙurƙusar zuciya da gangar jikinsa, da ƙyar ya aro jarumta ya shiga Bathroom yayi wanka ya ɗauro Arwalah, jallabiya ya zura ya shimfiɗa darduma ya data sallah, raka'a biyu yayi a sujjadar sa ta ƙarshe ya jima sosai yana roƙon Allah kafin yayi sallama nan ma ya jima yana addu'oi sannan ya miƙe ya cire rigar yabar wandon jikinsa kawai, yabi lafiyayyan gadonsa ya kwanta yana lumshe idanu, ya jima yana tunanin ta kafin bacci ya ɗaukesa mai cike da mafarkanta. naci kuka har na gode Allah kamar ba gobe, bansan sanda bacci yayi awon gaba dani, ban farka ba sai yamma liƙis, "Innalillahi wannan wane irin bacci ne ya kwashe ni" na faɗa ina sakkowa daga gadon tuna cewa ko sallar azahar banyi ba gashi har la'asar tayi, sai da nayi wanka na ɗauro arwala na fito ɗaure da Towel, riga da zani na saka na ɗora dogon hijabi na fara rama sallolin da banyi ba, ina kan sallayar Mami ta turo ƙofar ta leƙo tana faɗin "lfy kuwa kusan zuwa na uku kenan ɗakin nan kina bacci ko dai bakida lfy ne" kai na jinjina mata nace "eh bana jin daɗi ne, sannu da dawowa" "sannun ki dai ke dan nikam na jima a gidan nan" ta faɗi tana ƙara kallon yanayi can kuma tace "kukan me kikayi"? na sunkuyar da kai nace "ba komai" tace "ok to Allah ya sawwaƙe miki ki sakko kici abinci kisha magani." tana kaiwa nan ta fita ni kuma na miƙe ina naɗe sallayar na biyo bayanta, karo mu ka yi da Hadiza ta kawo min Papi da ya fara kuka, na karɓesa na dawo ɗakin nai masa wanka, pampers kawai na canja masa na goyasa na sake fitowa, Mami ce kaɗai zaune tana kallo, wuceta nai na shiga kitchen dan haɗa tea dan yanayin da nake jin kaina bana tunanin zan iya cin wani abinci, Mami ta bini da kallo ganin yadda nake tafiya kamar wata marar laka ga kuma ɗan rikicin yaron nan dake ta kyankyara kuka nasan yunwa yakeji kuma da gangam naƙi sakko da shi, jira kawai nake wani yayi min mgn na sauke masa ruwan massifar dake kaina mai neman kuka aka jefeshi da kashin shanu me zai jira? sai da na gama tsaf! na fito riƙe da kofin, ƙamshin turaransa wanda ba baƙo na bane na fara juyowa tun ban ƙarasa fitowa ba, hakan ya tabbatar min da lallai shine, kasa fitowa nayi na tsaya riƙe da kofin kamar wata sakarya, ciki na koma na ajiye kofin a fusace na fito na tsaya kuma na kasa fita, kusan 6 minutes ina tsaye da ƙyar na aro jarumta na fito falon, mgn suke da Mami kowannensu na murmushi, ni dai kallo ɗaya nai musu na koma ɗakina ba tare da nace dasu uffan ba,Mami kam da idanu tabi Nu'aiymah dashi ganin yadda ta fito kitchen ɗin a fujajan tana yin komai cikin rashin nutsuwa, girgiza kai kawai tayi tana mata fatan shiriya, Abdull ɗin ma da kallo ya bita dashi ganin yadda mood ɗin ta ya sauya yana mamakin ƙarfin halinta. sun jima sosai suna ƴar taɓa fira sannan Mami ta haye sama bayan tace ya zauna yanzu zata sa Nu'aiymah ta kawo masa Papi ya gansa tunda ina batada wannan azancin, ya amsa da "To" yana danna wayarsa,turo ƙofar Mami tayi ta dubeni rai a ɓace tace "in kin gama shashancin naki ki sauka ki kai masa ɗansa yana ƙasa yana jiran ki" bata jira amsa ta ba tayi ficewarta, ni kuwa na turo baki na sake gyara zama tare da janyo wayata ina operating ina jin kukan Papi nai masa banxa, Mami ta idar da sallah tana zaune kan sallaya tana azkar tun daga ɗakinta take juyo kukan Mami, ganin dai abun bana ƙarewa bane ta shafa addu'a ta fito zuwa ɗakin Nu'aiymah, ta tura ƙofar ta ganta zaune saman sallayar tana addu'a Papi kuma na kan gadon yana ta kyankyara kuka kamar me, a fusace ta ƙarasa ta ɗaukesa ta jijjigasa aikuwa yayi shiru yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, hakan yayi daidai da miƙewarta tsaye ai batayi wata-wata ba ta ɗauke ta da mari tana nuna ta da yatsa kafin ta soma mgn rai a ɓace "sabon salon iskancin da kika tsiro dashi a kwanakin nan kina amfani da ƙaramin yaron da baisan hawa ba baisan sauka dan kawai ki ƙuntatawa ubansa da bai masan kina yi ba, tou wllh tllh ki shiga hankali shashasha marar wayo kawai, maza ki karɓe shi ki shayar dashi sannan ki sauka ki kaisa gun ubansa yana ƙasa yana jira a kawo masa ɗansa! wannan umarni na ne in har na isa dake, wllh da kinsan irin matsalar da muke fama da ubanki kwanakin nan duk akan ki da tuni kin rufamin asiri kin rufawa kanki kin koma gidan mijin ki, gani yake ni nake zugaki baisan cewa nima bakyajin mgn ta ne da yanzu kinbar gidan nan, tabbas a farko naso hana masa ke amma a ƙarshe dana fahimci baya cikin hayyacinsa komai ya faru na dawo daga dokin fushin da na hau, da wanne kike so inji? da zagin da mutanen gidan nan suke min ko kuma rigimar da muke fama da ubanki? mene ne amfanin zamanki a gidan nan wace riba kike samu? wllh Nu'aiyma bbu gidan da yafi gidan miji daraja da rufin asiri, shikenan kinfi ƙaunar mu zauna dake muna gogar kafaɗu kamar sa'annin juna? ba komai in kika kashe nawa auren kinga shikenan duk mun huta daga ni har ke!" Mami ta faɗa tana share ƙwalla ta bar ɗakin da sassarfa. wani rikitaccan kuka na saki gamida faɗawa kan gadon dafe da kuncina, sai da nayi mai isata tausayin yarona ya kamani da yayi kuka har yayi bacci, ɗaukar sa nai na rungumesa tsam a jikinta ina kuka da nadamar abinda nake ƙoƙarin yi, zip ɗin rigata na zuge na ciro abinsa na saka masa a baki, duk da yana cikin bacci sai da yayi caraf ya fara sha yana sauke ajiyar zuciya sai wata muguwar tausayin sa ya ƙara kama ni, sai da na tabbatar Papi bacci na kwantar dashi na saka Hijabi na sakko ƙasa, 'ɗan Mayya kawai' na faɗa a zuciyata ganin har yanzu yana zaune a falon yana danna waya fuskar nan ba yabo ba fallasa, sanye yake cikin ƙananan kaya riga da wandon jeans farare tass! ya manna wani baƙin eyeglasess wanda su ka yi bala'in yi masa kyau, hannunsa na hagu kuwa wani masifaffan agogo ne mai shegen kyau da sheƙi ɗaure a tsintsiyar hannunsa, yatsun hannunsa sanye wasu fararen zobuna na azurfa masu shegen kyau, takalman ƙafarsa ma farare 'mutum sai kace shi yayi kansa' na sake faɗa murya can ƙasan maƙoshi, na jima a tsaye kafin na aro jarumta da kuzari na ƙaraso tsakiyar falon ina goge hawayen da suka bushe a fuska, fuska ba walwala na zaune ɗan nesa dashi ina wasa da yatsun hannuna, tun sanda ta fito yake kallonta ta ƙasan ido har lkcn da ta kafesa da ido duk yana ganinta har ta ƙaraso ta zauna bai ɗago kai ya kalleta ba, falon yayi shiru ba ka jin komai sai ƙarar Ac da na fitar numfashin mu. ganin bashida niyyar mgn yasa na tattare duk wani girman kai na ajiye gefe, na riga na sakawa raina cewa zanyi wannan abin ne sbd farinciki mahaifiyata, bazan so ɓacin ran mahaifiya ta har ta kaisu ga samun saɓani da mahaifina, hawayen da ta zubar ɗazu a kaina kaɗai idan na tuna sai naji wani tashin hankali da damuwa ya lullaɓeni da tarin nadama, jira kawai nake ta huce inje in sameta in bata haƙuri, zan basa haƙuri sannan na koma gidana bawai dan ina wani sonsa ba aa kawai dan farincikin iyayena domin banida sama dasu a rayuwata bazan so ƙuntata musu ba! murya can ƙasan maƙoshi nace "ina wuni anzo lfy" shiru Abdull yayi bai amsa ba sai da ya ɗago ya ƙare min kallo sannan yace "lfy lou" daga haka ya mayar da kansa kan wayarsa da yake operating tun ɗazu, wani haushin kaina ne ya kama ni but na daure na haɗiye wani abu mai ɗaci nace "daman nazo baka haƙuri ne" na faɗa ina sunkuyar da kai ina wasa da zoben hannu na. "Ohk yayi" kawai ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, zamewa nai na zauna saman carpet na haɗa kai da guiwa na fashe da kuka harda shashsheƙa, mamaki da Al'ajab yasa ya kashe wayar ya saka a Aljihu tare da miƙewa daga kishingiɗen da yake yana kallon ikon Allah, then ya zare glashin fuskarsa yana ƙare mata kallon mamaki jin yadda take rera kuka tamkar wacce aka doka, jin kukanta yake har a cikin ransa, ganin ta ɗago tana goge hawayen dake rige-rigen zubo mata yace "lfy wa ya dake ki" hararansa nayi na ƙara fashewa da kuka dan sosai naji haushin yadda ya gwasaleni shisa na ɓige da kukan dan dama mai neman kuka ne aka jefa da kashin shanu, shagala yayi da kallonta yana danne dariyarsa, a zuciyarsa yake faɗin 'Ikon Allah wasu kuka kan sakasu muni ita kuma kyau yake mata' ganin dai taƙi mgn ya ɗaure fuska yace "lafiya kika zo kika sakani a gaba kina kuka"? yadda yayi mgn bbu wasa yasa nace "tou ba kai bane ba" yadda tayi maganar yasa shi ƙara shagala da kallonta har ta ƙarasa goge fuskarta da gefen hijabinta, ta ɗago suka haɗa ido yayi saurin ɗauke nasa yana basarwa tare da zaro tissue cikin Aljihun wandonsa ya cilla mata yace "Oya! tel me meyasa kike kuka ko dai Mami ce ta dokeki"? baki na kuma turowa gaba nace "ba kai bane ka haɗani da ita ba!" idanu ya zaro kamar da gaske yace "ni kuma? me nayi"? zan basa amsa phone ɗinsa ta fara ring, ya ciro ta a Aljihun wandonsa yana murmushi yayi picking ya kai kunnensa, banji me aka ce ba naga dai ya kwantar da kansa saman kujera yana lumshewa then yace "Matar mijin ta! I missed U too dear ya kike ya gajiya" wata irin zabura nayi na juyo gabaɗaya ina son tantance daga ina maganar take fitowa, sanda na gano lallai shine har wani dishi-dishi na fara gani dan wata baƙar massifar da take taso min, bakina yayi nauyi na kasa furta komai sai kawai na kafesa da ido ina kallo kamar na samu Tv, murmushi yayi ya sake gyara zaman sa a jikin kujera yace "Ayyah! Sweetheart nima kina raina na dai ƙyaleki ne ki huta tukun, kina kirana kuma naji wani farinciki da kwanciyar hankali ya sake lulluɓe ni, tunda na tabbatar kina lfy yakamata kije ki kwanta ki huta kinsan banason kina wahalar min da kanki Amarya ta kuma gimbiyata ƴar gaban goshin mijinta nan da ƴan kwanaki In shaa Allah" wani shegen gumi ne yake karyomin tako ina, ƙirjina kuwa kamar zai fito waje sabida yadda sautinsa yake fat-fat, nasan da za'a auna jinina yayi mummunan hawa, tsam na miƙe tsaye ganin asirina na daf da tonuwa, steps na fara takawa tamkar zan kife ba tare da nasan inda nake cilla ƙafata, ina ƙoƙarin shiga ɗaki ya kira sunana yace "ina kuma zaki je ke da kikace zamuyi mgn ko kin fasa ne"? yayi tambayar cikin sigar rainin wayau, cikin daburcewa da gushewar hankali nace "za...zan ƙarasa wani abu ne zuwa dare zan ƙiraka muyi maganar" ina kaiwa nan nayi wuff na shige ɗakina tare da murza key, jikin ƙofa na tsaya ina numfarfashi ina jin zuciyata tana min wani mugun zafi kamar garwashin wuta, ƙafafu na sun gasa ɗaukata shisa na sulale ƙasa na zauna jikin ƙofar gamida sakin wani firgitaccan kuka mai game da zallar tashin hankali da ɗimuwa. dariyar da yake ɓoyewa tun ɗazu yana ganin ta shige ɗakinta ya tintsire da dariya tamkar zai kife ƙasa, sosai ta bashi mugun dariya da tausayi, kenan dama tana kishin sa iskancine kawai da iyayyi, ya jima sosai yana dariya shi kaɗai har Mami ta sakko tana tambayarsa dariyar me yake, ya guntse dariyarsa yace "wani posting na gani a facebook da ya mugun bani dariya da sanya ni nishaɗi" Mami ta girgiza kai kawai shi kuma ya miƙe tsaye da zimmar tafiya tace "abinci fa"? yace "a ƙoshe nake yanzu zanje na duba yadda aka shirya gidan ne ɗazu ƴan company suka kirani suka ce an gama komai" Mami tace "Owk to shikenan Allah ya taimaka yayi jagora, wani sabon salo ne wannan kuma da dole sai ƴan company ne zasu gyara maka gidanka sai kace wanda zai yi sabon aure"? Murmushi kawai yayi yana sosa ƙeya yayi mata sallama ya fice yana murmushi.

*Namesake Tabbas kina son Ya Abdull ɗinmu shashanci ne ya hanaki fahimta.*

ONE BLOODWhere stories live. Discover now