⚡ *ONE BLOOD*⚡
https://www.wattpad.com/user/AbdullNuaiymerh?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
_Episode 17-18_
تَقَبَّلَ اللهُ مِنَّا وَمِنكُم
_Taqaballahu minna wa minkum May the eternal peace from heaven embrace your life on this Eid ul Adha and fill it with uncountable blessings. Eid Mubarak!_ 🥰Sakkowar ta daga napep yayi daidai da fara sakkowar ruwan sama Bbu kakkautawa, da sauri ta sallame sa ta shige gidan da gudu, Bbu kowa a tsakar gidan hakan ya sata nufar dakin Mama, zazzaune ta same su duk sunyi tagumi Jafar baya wajen, Mama na ganinta ta mike a zafafe ta iso gabanta ba tayi wata² ba ta wanke fuskar ta da wasu lafiyayyun marika guda biyu tana huci, cikin tsananin bacin rai Mama ta nuna kanta da yatsa tace. "Ni zaki rainawa hankali Fateemah! Kice min zaki je Saloon ashe yawan gantalin ki kika tafi? Allah ubangiji yayma Jafar Albarka da yabi bayan ki har ya gano min motar da kika shiga sai dai abin tambayar shine motar ubanwa kika shiga kuma daga gidan ubanwa kika fito."? Ganin fuskar Mama ta nuna tsantsar bacin rai da damuwa ya sa Zuhra tsorata sosai, cikin inda² tace. "S..Salima ce fah tazo ta dauke ni muka je Saloon." "Karya kike Zuhra, wlh ba iya nan kawai kukaje ba, ni na haife ki nasan halin ki fiye da yunwar ciki na, na rasa wane irin hali ne dake da shegen taurin kai, so nawa nake gargadin ki akan ki fita a harkar yarinyar nan Salima amma da yake ni din ban isa dake ba har ynzu kina mu'amala da'ita, ba za ki fahimci abinda nake hango miki ynzu ba dan dama ance abinda Babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai ga komai ba! kici gaba dayi Akwai ranar kin dillanci kuma za kiyi kuka da idon ki muddun bakya jin abinda nake fada miki." Daga haka Mama ta shige dakinta, Jafar dake tsaye a kofar dakin yana sauraron su ya karaso dakin fuskar sa Bbu walwala ya dube ta yace. "Abu na karshe da zan fada miki shine, na rantse da Allah duk ranar da kika sanya kafar ki kika bar gidan nan ba tare da izinin mijin ki ba! Hum." Sai kuma yaja kwafa yabar dakin suka bar Zuhra da cizon yatsa. Tun daga wannan ranar Zuhra ta daina fita ta daina walwala ta shiga damuwa fiye da tunanin mai tunani gashi kuma gobe zasu koma kauye wajen malam dan karbo maganin and kuma ba da ko kwandalah anan gida duk kudadan ta suna gida Bbu halin fita balle ta nemo bashi ko da gun kawayen ta ne, ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin mafita dan ynzu babban burin ta shine ta koma gidan mijin ta dan ta gaji da azabtarwar Mama da Yah Jafar, tsakanin ta da Allah ta shirya zaman aure da masoyin ta, ta yarda ta amince zata dinga kula da kanta da gidan da duk wani abinda zai sashi farinciki, amma fa ta dau Alwashi ko ba jima ko ba dade sai ta raba Nu'aiymah da Abdull dan ita kadai ce zata zauna dashi har karshen rayuwar ta. Dubarar kiran wayar Salima ne ya fado mata ko zata bata shawara, cikin sand'a ta leka tsakar gdan taga su Mama na can zaune karkashin iccan magoro suna hira, rufe dakin tayi sannan ta dawo ta zauna tayi dialing no din Salima, ring biyu tayi picking cikin dariya tace. "Kin samu fitar ne gobe ne tafiyar fah." "Akwai matsala wlh." Salima ta gyra zama tace. "Wace irin matsala ce." "Matsalar biyu ce na farko yadda zan samu fita gidan na biyu kuma Bbu ko sisi a hannuna duk na baro can gidan gashi kuma inason fita na nemo kudi sai dai Bbu damar yin hakan." Salima ta saki murmushin mugunta tace. "Karki damu zan baki rance amma da sharadi, maganar fita kuma ke da kanki ya kama ta ki samo wannan mafitar." "Okay! Zan san abinyi Ngd Besty." "Karki damu Bbu godiya a tsakanin mu Sweetheart, karki manta tun karfe tara zamu kama hanyar kauyen Sbd inason mu dawo kafin sha daya dan zanyi bako." Kai kawai Zuhra ta jinjina mata tamkar tana ganin ta daga haka su kayi sallama. Washe gari tun karfe bakwai ta kammala duk wasu ayyukan ta, karfe bakwai da rabi Jafar da su Zainab suka bar gidan ya rage daga ita sai Mama, bayan tayi wankanta ta shirya tsaf tana zaune a tsakar gidan tana sak'e-sak'e a ranta ta tsinkayo Mama cikin shirin fita, wani irin farinciki ne ya mamaye mata zuciya amma ta danne ta danyi murmushi tace. "Awn Har kin fito Mama."? "Eh wlh kin ganni ma fitar gaggawace ta kamani shaf na manta yau ne bikin gidan kawun ku sule sai dazu mukayi waya da Rabi take zancan na tuna, kuma ya dace kuje sunan nan fah musanman ke da kwata² bakya zumunci da 'yan uwanki." Zuhra ta yamutse fuska tace. "Kiyi tafiyar ki kawai ni ba inda zani ta kaina nake so nake na koma gidan miji na amma kowa ya shashantar da zancan." Ta karashe tana wani bata fuska, Mama ta tabe baki tace. "Ai duk ke kika jaa ni dai Bbu ruwana in Allah ya nufa zaki koma gidan sa ai zaki koma tunda Bbu abinda ya gagare ikon Allah, addu'a ita ce kawai mafita Allah ya zaba miki abinda yafi Alkhairi ke kuma bakya addu'ar." "In shaa Allahu zan ma koma ne." Mama tace. "Allah yasa hakan shi yafi Alhairi." Ta amsa da Ameen daga haka tai mata sallama tayi tafiyar ta, da gudu ta shige daki ta saka hijab ta fito ta kulle gidan itama ta fice daga gidan bayan sunyi waya da Salima. Cikin Ikon Allah yau suna zuwa suka tarar Bbu mutane sosai mutum uku ne kawai a gaban su sune na hudu layin yana kaiwa kansu suka shiga, shirgegen mutumin ya dube su yace. "Kun cika Alkawari dan haka nima doli in cika muku Alkwari ta hanyar biya muku bukatar ku." Murmushi duk su kayi suna masa godiya, ya dauko wani garin magani kulle a cikin farar leda yace. "Ki barbada wannan garin maganin a idonki sannan ki tabbatar kun hada idanu dashi, za kiga abun Al'ajabi." Ya fada Bbu ko digon murmushi a fuskarsa, a tsorace ta karbi maganin Zuhra ta tambaye shi adadin kudinsa ya fada musu ta biya suka fito, tafiya suke suna tattaunawa har suka iso gaban motar Salima Zuhra tace. "Ynzu Babban tashin hankalin yadda za'ayi mu hadu har muyi ido hudu dashi." Tsaki Salima taja tace. "Amma fa ke banza ce Besty! Ai wannan shine mai wuyar gashi kuma mun samu a saukake." "Hum kin manta cewar gidan akwai security's ya za'ayi su barni shiga." "Tou ke ba matar gidan bace kuma Allah na tuba ynzu ba duniya ta zama abinda ta zama ba, muna bawa ogan nasu 'yan canji zai barki shiga." Zuhra tayi murmushi tace. "Kin kawo shawara amma yaushe zamu je."? "Yau² din nan zamuyi komai wlh daga nan sai gidan ni in tsaya a bakin gate ke ki shiga bayan mun bawa security's din cin hanci, sannan ki tabbatar kun hada ido dashi to wlh yau zakiga abin mamaki dan ni na yarda da aikin mutumin nan sosai tunda ba yau aka fara ba." Zuhra ta saki murmushin farinciki cike da kaunar kawar tata mai son ganin Farincikin ta, motar suka shige suka bar dajin direct sai a gidan Abdull. Tun ina kukan kadan² har na dawo sauke ajiyar zuciya time to time duk da banji zafi sosai kamar na farko ba amma na gurzu sosai a hannun sa, kusan awa daya curr! Yayi a kaina yana abu daya sai daf da magariba ya shafa min lfy ya mirgina gefen gadon ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Mikewa nayi a hankali ina dingishi nayi hanyar fita dakin daure Towel a kirji na, ganin zata fice daga dakin ya sashi mikewa da sauri ya isa gareta ya dauketa cak! Sai Bathroom, wanka yayi mata ya gasa mata jiki shima yayi wanka suka fito bayan sunyi arwalah, a rungume ya fito da'ita kamar wata baby girl ya nad'eta cikin Towel ya dire ta kan gadon ya dauko mai ya fara shafa mata yana murmushi, bayan ya gama ya dauko doguwar rigar shan iska ya saka mata ya saka mata hijab ya shinfida musu darduma ya jasu sallah. Bayan sun gama ya juyo yana kallon ta yace. "Me zaki ci."? Dagowa nai na kallesa sai kuma na sunkuyar da kai na fashe da wani matsanancin kuka harda shashsheka, a rikece ya riko ta yana tambayar ta lfy? Cikin gunji kuka nace. "Kashe ni zakayi Ya Abdull wlh bazan iya ba don Allah karka kara min irin wannan nuguntar pls bana so." Na karashe cikin kuka sosai, rungumota yay jikinsa yana bubbuga bayanta can ya farayi mata rada a kunne yana murmushi, d'if kake ji ta daina kuka sai ta kwanta a wajen ta daura kanta saman cinyarsa cike da gajiya da bacci ga kuma yunwa sai dai bata jin cin komai a halin ynzu. Muna dakin har akayi sallar Isha da kyar nayi shi na zame na kwanta saman gadon shi kuma ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo rike da plate da ruwa a cup. Ganin har bacci ya fara daukar ta ne yasa ya fara tashin ta, a hankali na bude idanu na da suka kumbura Sbd kuka na sauke su akan sa, murmushi ya sakar min nayi saurin kawar da kaina gefe. "Tashi kici abinci kar ki kwana da yunwa." A takaice nace masa banso! Murmushi Abdull yayi yace. "Yi hakuri karki wahalar min da kanki Popyluv tashi kisha ko tea ne please." Harara na watsa masa sannan na mike a hankali na karbi tea din daga hannunsa na fara sha..
_Allah ya rufa asiri na gama aiki na da wuri na muku typing but ba yawa, ba lallai ku jini gobe ba Sbd aikin gobe yafi wahala._ 🥱
NU'AIYMAH ABDULL TAFIDA✍🏻