*ONE BLOOD*
*SHAFI NA 51-52*
_Alhamdulillah Ala kulli halin haƙiƙa ciwo ba mutuwa ba ne! ngd sosai da addu'oinku gareni ƴan uwa, musanman masu kiran ƴar uwata Na'ima suna tambayar ya jikina, da masu turo mata saƙonni tako ina wllh duk tana sanarmin kuma nayi farinciki, Allah ya saka maku yabar zaman tare, my Habibtii kema bazan manta dake ba! saƙon kyawawan addu'oinki gareni kullum sun iso gareni ina godiya Alkhairan Allah ya riskeki har gadon baccin ki,i'm back again wllh tllh na dawo ne kawai badan ina jin kaina normal ba so dan haka kuyi haƙuri zan gajarta lbrn zanyi ƙoƙarin ƙarasa shi kwanan nan In shaa Allah........._ ✍🏼
a sume aka fita da Humaira a ɗakin suma duk suka fito daga ɗakin aka ɗauki gawar Mumcy zuwa wani ɗakin daban, cikin ƴan lokuta ƙalilan mutuwar Mumcy ta zagaye ƴan uwa da abokan arziƙi, bayan sallar la'asar akayi mata wanka aka rakata zuwa gidanta na gaskiya...Haj Jameela bata koma gida ba tayi zamanta nan gidan Mumcy aka cigaba da karɓar gaisuwa har akayi sadakan uku, har a lkcn Humaira bata dawo daidai ba har akazo akayi sadakan kwana bakwai, zuwa lkcn kowa ya watse aka bar su ƴan gidan kaɗai, a ranar Haj Jameela tayi shirin komawa gida ita da yaran amma fafur Salima tace bbu inda zataje bayan ta gama zageta tass! shi dai Dad baice da'ita komai ba yaja hannun matarsa da ƴarsa suka baro gidan suna mata fatan shiriya dan Salima tayi nisa bata jin kira, tun a lkcn riƙon Humaira ya dawo hannun Hajiya Jameela mace mai kirki da sanin yakamata, sosai ta riƙe amanar da Mumcy ta bar mata bbu tsangwama ko wani abu makamancin haka dan sai ka rantse ita ta haifi Humaira. washe gari tun safe Abdull yayi shirin fita Office ba tare da yabi takan kowa na gidan ba, kallo ɗaya za kai masa ka fahimci yana da damuwa, direct Office ɗin shugaban su ya nufa, a mutunce suka gaisa sannan ya samu wuri ya zauna yana fuskantarsa, cikin tsananin mamaki *DG* ya zare eyes glasess ɗin fuskarsa ya ajiye saman teburin gabansa daga bisani kuma ya fara girgiza masa kai yace "no!! Abdull hakan ba zaiyu ba, kai haƙuri muna buƙatarka a kusa damu badan komai ba sbd ƙwazonka da hikimarka, irin ku sunyi ƙaranci a ƙasarmu and ƙasarmu na buƙatar gyara, gida bai ƙoshi za'aba na waje? ya za'ayi kace mu turaka wata ƙasa daban kaje kai musu aiki Alhalin ga tarin ayyuka birjik da kuma gyararrakin da ƙasarmu ke da buƙata" ya haɗiye wani yawu mai ɗaci sannan yace "I'm sorry sir! I know bazakaji daɗi ba, but ina son ka fahimceni inada babban dalilin da yasa nazo maka da wannan batu, ba wani daɗewa zanyi ba, wata biyar ko shidda ma ya isa" DG ya jinjina kai cike da gamsuwa yace "Okay! ba damuwa but zanyi tunani tukun dan bana buƙatar kayi nesa damu, ina tsoron mu turaka wata ƙasa kaji daɗin ƙasar ka nemi Afectation na zama dindindin" murmushin ƙarfin hali kawai yayi yace "In shaa Allah! hakan bazata faru ba sir" yace "to Allah yasa" shima ya amsa da "Ameen" yana murmushin da iyakarsa fuska dan shi kaɗai yasan irin tarin damuwar dake nuƙurƙusar zuciyarsa shisa ma yake ƙoƙarin nesanta kansa da ƙasarsa ta haihuwa gabaɗaya ko zai samu salama daga suyar da zuciyarsa take masa, nan dai suka cigaba da taɓa ƴar fira akan ayyukansu daga bisani Abdull yayi masa sallama ya koma office ɗinsa dan ƙarasa wasu ayyukansa da ya fara. bayan kwana biyu takardar tura Abdull ƙasar Somaliya ta fito daga babban offishinsu na ƴan sandan farin kaya, tun a daren ranar Abdull ya sanar da Baba da Ummah, Baba dai baiji daɗin tafiyar da zaiyi amma dai ya masa fatan Alkhairi da Addu'ar samun nasara, sosai Ummah taji daɗin tafiyar da zaiyi dan ita gani take ko ba komai sunyi nisa da Nu'aiymah hakan kuma babban farincikin ta ne, cikin kwana biyu lbrn tafiyar da Abdull zaiyi ta gama zagaye Family house ciki kuwa harda Nu'aiymah dasu Mami, sauran sun masa fatan Alkhairi da Addu'ar sauka lfy wasu kuwa ko a jikinsu, duk wannan abun da ake Abdull baije falon Mami ya gaya mata ba duk dan kar su haɗu da Aiymah, ya dai kirata ya gaya mata tayi masa fatan Alkhairi da nasara, a daren ranar da zai tafi kaff dangin babba da yara yayye da ƙannai bbu wanda baizo masa bankwana ba amma banda Nu'aiymah, duk yadda Mami ta tursasata zuwa ƙin zuwa tayi a ƙarshe da taga ta tursasata sai kawai ta fake da bata jin daɗi ƙafafunta ke mata ciwo, haka Mami ta haƙura taxo part ɗin su Abdull ita kaɗai sauran ƴan uwanta ma sai tambayar Mami ake da ita sai dai tace musu bata jin daɗi ne, a ɓangaren Abdull ma sai zuba idanu yake yaga ko zata zo masa bankwana amma shiru kakeji, sai yanzu ya sake tabbatar da irin ƙiyayyar da take masa ba kaɗan bane, washe gari tun ƙarfe bakwai sauran ƙanninsa da su Baba su ka yi masa rakiya har Airport, ƙarfe tara jirginsu ya lula saman gajimare zuwa ƙasar Somaliya. bayan kwana uku da tafiyar su Ya Abdull safiyar ranar wata lahadi ina kwance a ɗaki na tashi da wani matsanancin fushi wanda ni kaina bansan dalili ba, gabaɗaya haushin kowa nakeji banason ganin kowa hakanan kuma banason a ɗaki, na tare a ɗaki tun safe naƙi fitowa ko breckfase a ɗaki nayi, ina kwance sai juye-juye nake kan gado naji wayata tayi ƴar ƙarar shigowa saƙo, tsaki naja kamar zan share sai kuma na janyo wayar na kunna, ganin baƙuwar number ce nayi saurin buɗe saƙon na fara karantawa. "Assalamu Alaikum ƴar uwa, barkanki da safiya fatan kin tashi lafiya ya gida, ina miki fatan Alkhairi daga nan har inda kike Alkhairin Allah ya lulluɓeki har gadon baccinki, ubangiji ya kare gabanki da bayanki ya warware miki duk wata matsala da kike ciki cikin sauƙi ya biya miki buƙatunki na Alkhairi, na barki lafiya" a daidai nan saƙon ya tsaya, na karanta yafi sau uku ina ƙara kallon numbar dan ban ganeta ba, harga Allah naji daɗin addu'oin amma fa na tsorata sbd bangane no ɗin ba, na jima ina tunanin ya akayi wanda ya turo saƙon yasan ina cikin damuwa kuma a ina ya sanni? na gama ƴan tunane-tunanena sannan na ajiye wayar ba tare da nayi reply ba na koma na kwanta. ina nan kwance har akayi la'asar ban fito ba sallah kawai ke tadani, ina zaune kan darduma nayi nisa sosai cikin tunani Mami ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, wuri ta samu ta zauna tana fuskantata da kyau, na ajiye carbin hannuna ina kallonta da ƴar murmushin yaƙe a fuskata na gaisheta, "anya kuwa hanyar da kika zaɓa mai ɓillewa ce Nu'aiymah? gabaɗaya na rasa gane kanki kwanakin nan tunda Abdull ya tafi nake lura dake karki maidani warce batasan me take ba! kin shige ɗaki kin hana kanki fitowa kamar matar mamaci da ubanwa yayi maki dole da barin gidanki? ni na haifeki kuma nasan halinki wallahi tallahi kina ƙaunar Abdull har gobe so ki daina wata burga indai sbd ni ce dan kar nake kallonku daga ke har shi so ki daina wani nuƙu-nuƙu, sannan ba wnnan ba dan ubanki tun ɗazu kusan sau uku ina turo Noor kiranki inason fita bbu Hadiza bare ta kula dasu dan ba daɗewa zanyi ba amma kince acemin kinyi bacci shisa na tako da ƙafata nazo inji dalilin ɓoye-ɓoyenki a ɗaki matar Liman"? baki na turo gaba nace "ni dai karki fassarani Mami da gaske fa banida lfy" Mami taja wani wawan tsaki ta buɗe jakarta ta cilla mata key tace "kanki ake ji ni dai ba wannan ba, in kin gama shiriritarki ki shiga ki gyara min ɗaki Saif zai taimaka miki ya dai fiye miki zaman banzan da kike, ke da kike a irin wannan halin sai kina ɗan motsa jiki kina ɗan ayyukan da basuda nauyi ko jikin ki ya ɗan saki bawai kizo ki jibge waje ɗaya ba kamar buhun kwaki" murmushi ne ya suɓuce min nace "to a dawo lfy, Allah ya tsare" ta amsa da "Ameen" ta fita da kullomin ƙofar. bayan wata biyu a lkcn cikin Nu'aiymah na cikin watansa na haihuwa, yammacin wata ranar laraba, zaune take a harabar gidan tana yankan farce Laila a gefenta suna fira sama-sama, time to time nake jin murɗawar da cikina yake min kamar ƙasan marata zata zazzago ƙasa dan azaba, rumtse idanu nai cike da baƙar azaba ina taune lips, mutsu-mutsu na fara addu'a ɗauke a fatar bakina, ba shiri na cillar da rezar hannuna ina karato duk addu'ar da tazo bakina,sai a lkcn Laila ta fahimci halin da nake ciki dan gabaɗaya hankalinta ya tafi ga wayar hannuna, ta kamo hannuna tana jeromin sannu, cike da tausayawa tace "sannu kinji? ko zamuje assibiti ne mu tadda Mami a dubaki wannan ciwon ciki dana mara tun safe abu yaƙi ci yaƙi cinyewa? gaskiya na fara tsoraka ko in sanarwa Inna ko Mum"? a hankali na girgiza kai bayan ciwon ta ɗan lafa nace "a'a karki gayama kowa In sha Allah! komai zai wuce." Laila ta girgiza kai cike da damuwa tace "wai meye haka ne? bakida lfy tun safe amma kike wani pretending ɗin lafiyar ki ƙalau sannan ki hanani faɗawa kowa? wallahi bazai yiwu ba nidai bbu ruwana nasani ko labour kikeyi bamu sani ba sai in zuba ido ina ganin ciwo na nuƙurƙusarki na ƙyaleki salon ki haifo mana baby a nakashe bazai yiwu ba wallahi" bata tsaya sake sauraron Nu'aiymah ba tayi hanyar part ɗinsu da sassarfa, ba jimawa sai gasu sun dawo ita da Mum Fareeda, ganin halin da Aiymah ke ciki yasa ta tsorata, ta kamota ita da tutsetsen cikinta da ƙyar suka nufi part ɗin Inna, ta zauna da ita ƙasan carpet tana jero mata sannu, a lkcn bbu bakin mgn jinsu kawai nake ina gyaɗa masu kai, kusan mintuna talatin abu yaƙi lafawa sai ma gaba dayake, zuwa yanzu ni kaina na gama fahimtar lallai naƙuda ce tazo min gadan-gadan hakama su Inna, da gudu Mum tayi waje tana kiran driver kan yayi sauri ya fito mata da mota waje, sannan ta shiga part ɗin su Abdull ta gayama Ummah sannan ta dawo suka kamani itada matar Uncle Nasir suka nufi mota dani sai matar Sulaiman dake biye a bayanmu riƙe da kayan da za'a iya buƙata na haihuwa, baya aka zaunar dani suka zauna gefena su biyun gabaɗaya na gama fita hayyacina, Mum Fareeda ta shiga mazaunin driver tana shirin barin harabar gidan Umma ta fito a gadarance tana yamutse fuska, har Mum ta tada motar amma ganin ta nufosu yasa ta kashe motar har ta ƙaraso ta buɗe gaba ta shiga ta zauna tana latsa waya ba tare da tace ma kowa uffan ba, cike da takaici Mum Farida ta figi motar dan yanzu bbu lkcn kace-nace ta Nu'aiymah suke yanzu, Hospital ɗinsu Mami suka nufi cikin ƙanƙanin lkc ƙwararrun likitoci suka karɓeta, sai da suka fara dubata sukaga bbu wata matsala naƙuda ce kawai sannan suka nufi labour room da'ita, bayan an shigar da Nu'aiymah ɗakin haihuwa Mum ta samu ƴar nutsuwar kiran Mami ta gaya mata suna hospital sun kawo Nu'aiymah, sannan ta kira Abdull shima ta gaya masa dan kullum sai ya kirata yaji ko tana lafiya ko bata lafiya ba tare da sanin kowa ba, ta wajenta kaɗai yake samun lbrn ta dan tun zuwansa ƙasar bai sake ɗaukan waya da sunan ya kirata ba sai dai suna chat da wata numbar daban inda ya fito mata da wani sabon salo yace shi mace ne yanason su zama ƙawaye, tun a lkcn shaƙuwa mai tsanani ta shiga tsakaninsu, ba jimawa sai ga Mami tazo wajen nasu cikin uniform ɗinta na manyan likitoci, waje ta samu ta zauna kusa dasu kowanne na tsumayen jiran ta sauka, tun ƙarfe biyar Nu'aiymah take labour har goshin magriba ta gabato, tun zuwansu wajen mata bakwai suka haihu har wanda sukazo a gabanta, amma ita shiru kakeji tamkar mallam yaci shirya, gabaɗaya hankalin doctors ɗin ya tashi da na Family nata dan duk wata dabara da zasuyi sunyi amma haihuwa ta gagara sai baƙar azaba takeci, duk taurin zuciya da taurin kai irin nata sai gashi ta kasa jurewa sai kuka take tana kiran sunan Mami, a ɓangaren Abdull kuwa tunda Mum ta kirasa ta gaya masa gabaɗaya hankalinsa ya kasa kwanciya, ba'a minti ashirin ya kirata yana tambaya ya ya har yanxu bata haihu ba, ganin har ƙarfe shidan yama babu wani lbr yasa ya hau shirin dawowa ƙasar sa ta haihuwa bayan ya sanar da manyan shi da sauran abokan aikinsa. Dr Samir ya fito daga ɗakin yana share zufar da ta tsatstsafo masa ya nufi Office ɗinsa, Uncle ya taresa da sauri yace "dr wai har yanzu shiru"? jiki a sanyaye Dr Samir yace "muje Office mu ƙarasa zancen dan maganar gaskiya akwai matsala sannan kuma muna buƙatar mijinta a yanzun nan, Dr Maryam kema ina buƙatar ganinki a tare dasu plx" yana kaiwa nan ya fice zuwa Offishinsa, jiki a sanyaye duk suka bisa da kallo har ya ɓacewa ganinsu, Mami ce ta fara bin bayansa ita jiki a mace sannan Uncle, Baba, sai Baffah, Dr Samir ya gyara zaman kujerar sa yana kallon Mami yace "nasan ke ƙwararriya likitar mata ce Maryam! so nasan dole kisan ire-iren waƴan nan matsalolin da mata ke fuskanta musanman a wajen haihuwa, munyi iya yinmu wlh abun ya gagara, yarinyar nan bazata iya haihuwa da kanta ba cikin biyu dole ayi ɗaya, ko muyi mata aiki ko kuma tana gaf da rasa ranta dan wlh ta jigata hakama yaron cikinta, ina tsoron ya samu matsala ko ita kanta yarinyar, kinsan illar jinkirin naƙuda yana canyowa mace matsaloli dadama, irinsu yoyon fitsari...etc" ajiyar zuciya duk suka sauke, ita dai ta kasa faɗan komai tana jiran amsar su Baffah, Baba ya kaɗa babbar rigarsa cike da damuwa zaiyi mgn kenan sukaji an banko ƙofar office ɗin a haukace, duk suka zaro idanu suna rige-rigen faɗin "Abdull!!" Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da kansa jikin ƙofar zuciyarsa na buguwa dan ya gama jin komai, few minutes ya ɗago yace "na amince Dr! muddun zata sauka lfy, Allah yasa ayi komai cikin nasara" duk suka amsa da Ameen but tambayoyi ne birjik a cikin ransu amma bbu lkcn yinsa, Dr Samir ya miƙo masa wata doguwar takarda da biro yace yasa hannu, jiki na kyarma Abdull ya karɓa yasa hannu sannan ya fice daga Offise ɗin, cikin mintuna ƙalilan ƙwararruun Doctors ɗin suka shirya komai aka shirya Nu'aiymah cikin doguwar riga green da farar huta aka fito da'ita zuwa theater room, ta gabansu akazo ficewa da ita duk suka bita da kallon tausayi ana mata fatan fitowa lafiya, Abdull da Dr dake tsaye ƙofar ɗakin Theater suna mgn sukai shiru ganin ana ƙoƙarin shiga da ita, cikin zafin nama Abdull ya dakatar dasu ya ƙarasa gaban gadon da sauri, bacci take tana jan zuciya a hankali sbd kukan da tasha, kyakkyawar farar fuskarta tayi wani irin fayau na rama sai idanunta da suka kumbura, tattusan tafin hannunta ya kamo yana murzawa a hankali idonshi nakan baby face ɗinta, a hankali laɓɓansa ke motsi kana gani kasa addu'a yake karantowa, sai da ya tofeta da addu'oi kala-kala sannan yayi kissing ɗin hannunta, yana ji yana gani suka tura gadon zuwa cikin ɗakin da za'ayi mata aikin sai fatan Alkhairi. ana shiga da Nu'aiymah a ɗakin Mami ta fice daga Hospital ɗin gabaɗaya jikinta duk a sanyaye, awa ɗaya da shigarsu Theater Room wata nurse ta fito da sauri ta nufo su Mum Fareeda, a gaggauce ta buƙaci da su bata kayan baby da Towel, cike da farinciki ta miƙo mata su sannan nurse ɗin ta koma da sauri, da kallo Abdull ya bita dashi yana addu'ar Allah yasa anyi komai cikin nasara, ko minti goma ba ayi ba sai ga nurse ɗin ta sake fitowa tana murmushi naɗe da baby cikin farin towel ƙal, cikin tsananin farimciki Mum ta ƙarasa da sauri ta ƙarbi jinjirin hannunta dake ta ƙwala kuka, Hamdalah gabaɗayansu sukayi ganin an fito da Nu'aiymah an nufi wani special room da ita dan hutawa, tsaya rubuta muku irin tsananin farincikin da Abdull ya shiga wlh ɓata lkci ne, yana tsaye a wurin nurse ta wuce gabansa da babyn hannunta zuwa ga su Mum, ji yayi kamar ya ƙwato yaron daga hannunta ya rungume shi a jikinsa shima yaji ɗumin ɗansa na jini, abinda ya jima yana nema yana bala'in son yara amma Allah bai bashi haihuwa ba, shekarunsu huɗu da aure da Zuhra amma ko ɓatan wata bata taɓayi ba, ashe rabon samun gudan jininsa na wajen wadda ya wulaƙanta ya ƙasƙantar yaci mata mutunci haƙiƙa mahaifinsa yayi masa gata sai, wai yau shine ya samu ɗa na kansa? Allah mai iko! mai yin yadda yaso da kuma yadda yaga dama, buwayi gagara misali, lumshe manyan idanunsa yayi cikin tsananin farinciki da annashuwa marar misali yana tsarkake sunayen ubangiji Al'arshi a zuciyarsa, sai da kowa ya karɓi kyakkyawan ƙaton jaririn a hannunsa wanda kamar ɗaya sak! da mahaifinsa tamkar yayi kaki ya tofar, farin uwar kawai ya ɗakko amma komai na Abdull ne, cike da farinciki ƴan uwa da abokan arziƙi suka fara ɗaukan yaron suna masa addu'oin tsari da kuma farincikin shigowa duniya gidan gwagwarmaya! Ummah dai na rakuɓe gefe kunya ta hanata karɓan yaron, Abdull ma na tsaye can ɗan nesa dasu kunyar Iyayensa da suke wajen ya hanasa cewar a basa yaron su kuma basuyi azancin basa ba amma idonsa na kan yaron ƙur kamar zai haɗiye duk gittawar da Mum tayi da shi, Inna kuwa har rawa ta taka a wajen wasu mata dake wajen dasu Mum na tayi mata dariya, Mum tace "kai Inna sai wani murna kike wannan angon mu ne fa mu kaɗai bbu ruwansa da tsohuwa ehe" ta faɗa a daidai sa'ilin da ta ɗaura yaron saman cinyar Umma ta komo wajenta ta zauna,Nan ma dariya sukayi cike da farinciki kowannensu na kallon Yanayin Umma ganin yadda sukaga ta ƙurawa yaron ido bbu ko ƙiftawa. hana kowa shiga ɗakin da Aiymah take Doctors ɗin su ka yi acewarsu tana buƙatar hutu sosai domin ta jigata, misalin ƙarfe ɗaya da ƴan mintuna na farka, a hankali na buɗe idanuna tun ina ganin dishi-dishi har na fara ganin komai tarr, cikin wata irin kasala data saukarmin na yunƙura zan tashi sai dai zafin da naji ƙasan marata kamar na ɗinki yasa nayi saurin komawa ina "wash!" hawaye na taruwa a idona, Mum Farida dake zaune gefenta saman dogayen kujerun da aka ƙawata speciale room ɗin da aka ƙawata ɗakin dashi har ta fara gyangyaɗi tana jijjiga jaririn da ya fara kukan yunwa, da sauri na waiga ina duban ɓangarenta jin kukan jinjiri kenan hakan na nufi na haihu kenan? cike da son gaskata hasashena nasa hannu na shafa cikina, jin sumul bbu komai yasa na yunƙura cikin zafin nama zan tashi, azabar da naji a ƙasan marata da yayi min yauni ga wani mugun zafi da raɗaɗi da nakeji yasa nai saurin kwantawa ina "wash!" da ɗan ƙarfi. Mum da baccinta baiyi wani nisa ba ta juyo tana duban ɓangaren Nu'aiymah da jajayen idanunta da suka canja kala irin na mai jin bacci,cikin tsananin farinciki Mum ta ƙaraso wajen Aiymah riƙe da jinjiri da ke ta kyankyara kukan yunwa, ta taimaka min na tashi zaune ina yamutse fuska tare da ƙurawa jaririn daketa ƙyalla kuka ido cikin tsananin farinciki da ƙaunar sa tun banji ɗumin jikinsa ba! maganar Mum ne ya katsemin tunani. "Alhmdllh how are u feeling now dear? fatan bbu wata matsala"? ta ƙarasa da sakarmin ƙasaitaccen murmushi, kunya ce ta hanani mgn na gyaɗa mata kai kawai gamida sunkuyar da kai ina ɗan satar kallon yaron, ba zato ba tsammani naji ta ɗaura min shi saman cinya tana faɗin "ina zuwa yanzu" daga haka tayi ficewarta ni kuma nayi saurin riƙo yaron cikin zumuɗi jikina har ɓari yake, ɓata fuska nai ina turo baki sanda na gama ƙare masa kallo naga komai na ubansa ne farina kawai yaron ya ɗauko, cikin tsananin so da ƙaunar yarona na rumgumesa tsam a jikina ina tofesa da addu'oin tsari da kuma nema masa kariyar ubangiji, aikuwa yayi shiru ya daina kukan da yake, hannuna na kai saman kumatunsa ina masa wasa caraf ya kamo hannun yana tsotsa ni kuma na fara dariya kamar zautacciya dan jin abun nake kamar yana min cakulkuli, a haka aka turo ƙofar ɗakin na ɗago da sauri, Doctor ne ya shigo wata nurse biye a bayansa, ita ta karɓi yaron shi kuma ya ƙara duba jikina yana min tambayoyi ina basa amsa kai tsaye sannan yayi min sallama bayan ya umarci nurse da ta taimaka min in shayar da yaron dake ta kukan yunwa tun ɗazu, ta ɗora min shi saman ƙafafu sannan ta nunamin yadda zan shayar dashi, rumtse idanu nai lkcn da yaron ya cafki abincinsa ya fara sha nan ma kamar nayi kuka dan azaba, then nurse ɗin ma tayi min sallama ta fita, na dawo da kallona ga yarona dake ta tsotsar abincinsa har yanxu yaƙi saki, turo ƙofar ɗakin da akayi ne ya sani saurin ɗagowa.
#Nu'aiymah Abdull