ONE BLOOD

78 5 1
                                    

⚡ *ONE BLOOD*⚡

https://www.wattpad.com/user/AbdullNuaiymerh?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

_Episode 21-22_

Surutun Inna na fara jiyo sama² A hankali na bude manyen idanuna na sauke su akan mutanen dakin, tun ina ganin dishi² har na fara ganin kowa, da kallo na dinga bin mutanen gidan mu da suka cike dakin Mami da Yah Abdull sai uwarsa da kaninsa sune kawai basa nan! Hawayen da nake kokarin boyewa suka silalo saman kunci na. Ji nai an dafe hannu na da sauri na juyo na sauke su akan Aunty Maryam, girgiza min kai tayi alamun na daina kuka, sake lumshe idanu nai wasu zafafan hawaye suka sake zubomin na koma na kwanta. Hakan yayi daidai na shigowar wata nurse ta duba jiki na ta kuma bukaci sauran mutanen su fito waje su barni ina bukatar hutu, kamar kyaftawar ido duk suka fice harabar asibitin inda su Baffah suke ya rage daga ni sai Aunty Maryam sai Inna. Aunty Maryam ta taimaka min nai wanka na canja kaya sannan ta hada min tea mai kauri nasha da kyar na koma na kwanta, kwanan mu biyu a Hospital ina jinya ko sau daya baizo dubani haka ma matar sa acewar sa shi ayyuka sun masa yawa tunda ga 'yan uwa duk suna kusa Allah ya bani lfy, ganin yadda yake musu maganar yasa basu ma sanar dashi maganar cikin dan zuwa ynzu sun fara zargin baya cikin hankalin sa, ranar cikon na uku aka sallame mu bayan sun rubuta min magunguna wanda zasu taimaka min sosai, ga mamaki na maimakon naga an nufi gidan mu dani sai naga sabanin hakan dan kuwa gida na suka kawo ni bisa umarnin Baffah da Baba shagari. Kuka da rigima Bbu kalar wacce banyi ba dan zuwa ynzu wata muguwar tsanar sa nake ji a raina fiye da tunanin mai karatu dan ko fuskarsa banason gani balle zaman gidansa haka zalika banason ganin duk wani abinda ya shafi rayuwar sa ji nake tamkar ina zaune kan kaya, bayan tafiyar su Leyla na kira Mami cikin kuka sosai akan Wllh Tllh ni bazan zauna gidan sa ba dole a raba auren nan dan dama ba son sa nake ba! Tun tana saurara ta a karshe ta kashe wayarta ba tare da tace min Uffan ba, kan gado na fada na sake sakin wani sabon kukan tausayin kaina da tausayin halin da nake ciki. Bayan na tsakaita kukan da nake na saka hannu na shafa ciki na da zarar na tuna cewar ina dauke ta cikinsa sai naji wata muguwar tsanar cikin da ko iskar duniya bai shaka ba kuma baiji ba bai gani ba, wallahi badan nasan hukunci kisa ba da bbu abinda zai hanani halaka cikin tun kafin yazo duniya. Idan na tuna cewa ina dauke da gudan jinin sa a jikina nakan ji mugun zafi da radad'i harga Allah banso haka ta faru ba! Amma a 'yan kwanakin nan na barwa ubangiji gagara misali komai, nayi Alkawarin bazan sake yiwa Allah shishigi akan Lamuran sa ba! Shi kadai yasan baiwar dake tattare da wannan cikin kuma shi kadai yasan dalilin samuwarsa cikin sati biyu kacal...da karfin gaske tace. "No!! Mlm bazan iya ba gaskiya! Wlh bazan iya jiran har nan da sati biyu ba! Please ka taimake ni hakuri na yazo karshe wlh bazan iya cigaba da ganin Zuhra cikin farinciki ba, ka duba ka gani daman taimako na take bukata tunda ta koma gidan mijinta ko kira na bata tabayi ba! Dan haka lkci yayi da zan nuna mata iyakar ta sannan na kafa tawa gwamnatin a zuciyar Abdull." Mlm yay murmushi yace. "Ba damuwa daman naso nai maki aiki ne irin wanda har duniya ta nade bazai taba waiwayar wata mace ba sai ke! Ciki kuwa harda uwarsa, amma tunda kina gaggawa zamu baki zuciyar sa a tafin hannun ki." Daga haka ya jiya ya dauko wata jaka ta fata ya bude ya fara sarrafa wasu abubuwa, da mamaki Salima take duban sa jin ya furta zai bata zuciyar Abdull a tafin hannun ta! Amma ta boye mamakin ta ta zuba masa na mujiya tana kallon abinda yake. Wani abu mai kama da mukulli ya dauko ya mika mata da key dinsa a jiki, ta amsa tana bin mukullin da kallo lkci daya kuma ta dago tace. "Wannan kuma ne meye."? Ya gyra zama yace. "Zuciyar sa ce aciki ynzu da kanki zaki kulle zuciyar amma fah sai kin saka masa wannan layar a karkashin gadon da yake kwanciya ya kwanta akai sannan zaki burda wannan key din da kika gani a jikin mukullin ki adana inda Bbu wanda zai gani sai yadda ki kayi dashi." Wata kafirar dariyar farinciki ta kece da'ita sannan ta zuge zip din jakarta ta dauko damin kudi ta ajiye a gabansa sannan tai masa sallama ta fice. Tunda Salima ta dawo gida take tunanin yadda zata saka layar a karkashin pillow din Abdull ta rasa yadda zatayi dan dama tun can ita ba mai shiga bedroom din Zuhran bace iyakar ta falon ta, dabarar kiran ta ne yazo mata bata tsaya wani dogon tunani ba tayi dialling numbar ta cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, bugu biyu Zuhra ta daga tana dariyar shakiyanci, bayan sun gaisa Zuhra ta fara kame² tana bawa Salima hakuri, Salima ta tabe baki tace. "Tace dan Adam kenan! But ba komai karki damu dama inason in sanar miki ne gobe zanso miki ziyara kinsan bana iya fushi dake besty." Zuhra tace. "Dan Allah kiyi hakuri wlh ba haka bane kinsan ynzu kullum yana gida bai cika fita aiki ba shiyasa ko chats ban cika yi ba! Amma kiyi hakuri kinji Allah kaimu goben lfy sai kinzo." Daga haka tai mata sallama ta kashe wayar ta tabar Salima da cizon yatsa, kwafa tayi tace. "Wlh nafi karfin ki wulakanta ni dan ubanki, kiris ya rage na tarwatsa rayuwar ki shashasha! Kawai."

ONE BLOODWhere stories live. Discover now