⚡ *ONE BLOOD*⚡
_Episode 25-26_
_NACI WUYA FAH FIYE DA TUNANIN KU, BUT YANZU ALHAMDULILLAH ALLAH YA TASHI KAFAƊU NA DUK DA NAJI ANCE NA FIYE RAKI😅IN SHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA._ 😍🤟🏼
two week da auran sa kenan, zuwa yanzu zan iya ce maku gidanmu ya zama filin dambe dan tun washe garin ranar da amarya Salima ta tare a gidan suka soma kafcen dan tamkar wasu dambobi haka suke rayuwa, a rana ɗaya za suyi dambe sama da biyar ko shida dan wataran kafin ayi breckfase a gidan ma har sun tafi zagaye na biyu. ganin rigimar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Abdull ya raba masu part, ya ɗauko Salima ya kawo ta part ɗinshi da zama amma duk da haka bata canja zani ba. tunda Salima tazo gidan ko da wasa bata taɓa shiga sabgata ba ko nemata da fitana ko wani abu makamancin hakan dan hatta gaisuwa bata taɓa haɗani da'ita ba hasalima tun zuwan ta gidan sau biyu kawai muka haɗu da'ita shima a hanyar shiga da fice na gidan ne shisa kowa yake rayuwar sa ba takura. ako da yaushe Zuhra ita ke cin wuyar kuma ita take tsokana, bawai Salima tafi ƙarfin ta bane a'a kawai dai ita Abdull yake zagi yana ci mata mutunci dan yanzu Abdull ya zama abinda ya zama, akan amaryar sa tsaf zai ci maka mutunci ya keta maka rigar mutunci kuma ko a kwalar rigar sa, shisa tunda naga take-takensa na ƙara kame kaina ya zamana ko ina jiyo hargogin su ko leƙowa bana yi balle su isheni kallo. ɗazu da safe da mu ka yi waya da Leyla take sanar min hukuncin da Baba shagari ya yanke akan aure na da Abdull, wlh bansan yadda zan musulta muku irin tsananin farincikin da nai dan har wani tsallan jin ɗaɗi nai, lkci ɗaya kuma murnata ta koma ciki tuna cewar ba'a sakin mace da ciki, tsaki naja ciki-ciki na tashi na hau shirin tafiya gidanmu ba tare da neman izinin kowa ba. a balcony mu ka yi cikiɓus da Salima sai waige-waige take tamkar mai neman wani abu, tana gani na tayi saurin kashe wayar hannunta tana murmushin yaƙe na mayar mata da martani na ratsa ta gefen ta zan wuce bayan mun gaisa. da wani kallo mai tarin ma'anoni Salima tabi Nu'aymah dashi bbu ko ƙiftawa, wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke taci gaba da wayar da take tana saƙe-saƙe a zuciyar ta. "ni dai na gaya maki bazan koma wancan baƙin gidan ba, ni ƙaɗai nasan baƙar azaba da baƙincin da nake ƙunsa a ciki, a rasa wanda zai tsaya min tsayin daka wajen ƙwatar min ƴanci sai kace tsintacciyar bakin asibiti, tou menene amfanin zama na a gidan? wanda nake zaune dan shi baya ƙauna ta bbu ruwan sa dani dan haka ni nazo kenan bazan koma ba ki rabu dani kawai" na ƙarasa faɗa cikin tsananin ɓacin rai sosai dan yanzu kukan ma yaƙi zuwar min. ɗauke kai Mami tayi daga kallo na bayan ta gama saurara na sai kuma ta miƙe tsaye riƙe da laptop ɗinta ƙirar companyn Apple ta haye uptairs. na gyra zama da niyar kwanciya saman 3seater ɗin da nake zaune kai idona ya sauka akan Baffah dake tsaye ƙofar falon yana bina da wani mugun kallo, sai yanzu na fahimci dalilin da ya sa Mami ta tashi kuma taƙi tanka min, a ɗan tsorace na tashi zaune na zame daga kujerar ina gaishesa.
"tashi ki fice daga gidan nan" kuka na fashe dashi ina yarfa hannuwa tare da faɗin "dan Allah kuyi haƙuri ku tausaya min ku rabani dashi wlh baya ƙaunata kuyi haƙuri ku raba auren nan Baffah kullum cutata yake har duka na fah yake" duk da ta bashi tsananin tausayi amma shi bazai goyi bayan ta ba kuma bazai zama sanadiyyar rabuwar auren ta ba and kuma ya ɗau alƙawarin ko da za'a raba auren zai bi yadda tsarin addinin musulinci ya faɗakar dashi kuma ya koyar dashi dan bbu wata gamsashshiyar hujjar da aka ce a saki mace da ciki, tsawar da ya daka min na miƙe da kƴar cikin gunjin kuka na fita, maimakon na shiga mota ta sai nai ficewata gabaɗaya daga gidan cikin fitar hayyaci bbu ko takalma a jiki na, tafiya kawai nake bansan inda nake cilla ƙafata ba! hawaye kawai ke bin kunci na da taimakon Allah na ƙaraso bakin titin mutane sai bina da kallo suke, ban damu dasu ba da ƙyar na samu abun hawa na shiga nai masa kwatancen inda zai kai ni naci gaba da kukan da nake.
cikin tsananin damuwa Mama ta rungumo Zuhra a jikinta cike da tausayin ta, Zuhra ta share Ƙwalla taci gaba da faɗin "Mama dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min dan na tabbata Alhakin kine ke biye dani, sai yanzu nake kirbar abinda na shuka, sai yanzu nake danasanin sanin Salima a tarihin rayuwata, sai yanzu nake ganin illar dake tattare da Salima wanda kike hango min tuntuni, ashe ita ɗin guba ce bansani ba, ta tarwatsamin farincikin gida na, wayyo na cuci kaina! Mama ki daure ki yafemin ko zan samu sassaucin ƙuncin rayuwar da na tsinci kaina a ciki kwanan nan." sosai jikin Mama da na ƴan uwanta yayi sanyi kuma ta mugun basu tausayi, bubbuga bayan ta Mama ta fara tana rarrashin ta har ta daina kukan sai ajiyar zuciya take saukewa time to time, bayan kukan nata ya lafa Mama ta kira sunanta ta miƙe zaune tana ƙara share hawayen fuskar ta, cikin tausasa harshe da kwantar da hankali Mama ta fara magana "na yafe maki Fateema! kuma naji daɗi sosai da kika ga abin da nake guje maki, yarinyar nan bata taɓa min komai ba haka kawai naji sam bata kwanta min ba shisa nai ƙoƙarin rabaki da ita amma kika ƙetare magana ta, Allah yasa mu dace kici gaba da haƙuri sannan ki daina rigima da ita tunda ke kika janyo ma kanki komai" Zuhra ta share ƙwalla tace "bazan koma ba Mama ni duniyar ce ma ta fice min arai kiyi haƙuri ki barni na zauna gida dan banga amfanin zamana a gidansa, ina da tabbacin Abdull baya cikin hankalinsa, Salima ta gusar masa da tunani sai yadda tai dashi, ita kanta ƴar uwar tasa ya daina shiga shirgin ta bashida lkcn kowa sai na Salima! wlh Mama Salima ta gama dani ta gama da rayuwata, idan na koma can gidan na tabbata baƙinciki da damuwa zai iya sa na kamu da hawan jini daga nan kuma zuciyata ta buga tarwatse kuyi asara ta" Mama ta sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa taci gaba da lallaɓata da kalamai masu daɗi da kwantar da hankali har ta sakko suka fara kwasar fira da ƴan uwan nata.
Salima ce durƙushe a gaban shirgegen bokan ta, bayan ta gama yi masa bayanin komai ya ɗago ya kalle ta da ƴar damuwa a fuskar sa yace "tou yanzu sai dai kiyu haƙuri dan zakiji lbrn da ba daɗi a bakina" Salima ta share zufar da ta keto mata cikin tsananin tashin hankali tace "dan Allah karka ce min zargina da kuma hasashe na ne ya zama gaskiya" Mlm yace "eh tou kusan hakane amma karki damu kanki dan za'a iya samun mafita duka-duka cikin watansa biyu kinga akwai hanyoyi da dama da za mubi mu salwantar dashi" farincikin ta ne ya kasa ɓoyuwa ta saki murmushin jin daɗi ta muskuta kusa da Mlm ta fara magana "Alhmdllh tunda akwai mafita, ni kuma na maka alƙawarin zan mallaka maka duk abinda kake so, na rantse da Allah Mlm in har buƙata ta zata biya zan mallaka maka kaina ka shiga gonar da mijina yake shiga yayi shagalinsa, zan mallaka maka maƙodan ƙuɗaɗe da gida da mota, nidai kawai a mallaka min shi ni ɗaya, sannan a hana ko wace mace ta haifa masa sai ni kaɗai, in taƙaice maka zance so nake a sanya tsanar duk wata mace a zuciyar sa, a rabasa da ƴan uwansa da duk wani makusancin sa, a maye masa gurbina na zama uwarsa na zama ubansa kuma matar sa uwar ƴaƴansa" Mlm ya sauke numfashi yana lasar lips idonsa ƙurr akanta yace. "tou karki damu, In sha Allahu kinzo inda zamu share maki hawaye, amma kafin nan zaki fara bani haɗin kai wajen samar min da natsuwa sannan mu shiga aiki gadan-gadan, murmushi ta saki dan ta fahimci abin da yake nufi, a take ta fara cire kayan jikinta ganin haka ya miƙe ya rufo bukkar kafin ya dawo ya sameta tayi ɗaiɗai saman yaloluwar tabarmar sintir haihuwar uwarta, Mlm ya saki murmushi yana lashe lips tsuntsu daga sama gasashshe, basu tsaya wasu wasanni ba tayi masa goho suka fara aikata masha'arsu.
kuka sosai nake ina sumbatu, tun mai napep ɗin yana bani haƙuri har yayi shiru ya ƙyaleni, muna isowa na sauka nace masa zan turo a kawo masa kuɗin sa sannan na juya na ƙwanƙwasa gate ɗin mai gadi ya buɗe min na shiga, zaune na samu Larai tana kallo, na zame na zauna saman kujera nace ta ɗauki ɗari biyu taje ta sallami mai napep ta amsa da toh ta fita, ni kuma na haye uptairs, saman gado na zube naci gaba da kukan, a hankali ta fara jin sauƙin raɗaɗin da zuciya ta take min. kiran sallar magriba ce ta tashe ni, na faɗa wanka na ɗauro arwalah na tayar da sallah, ban tashi daga dardumar ba har akayi isha, bayan na gama na kwanta ƙasa. bacci ne ya ɗaukeni sai misalin ƙarfe tara na farka a gigice addu'a ɗauke a fatar bakina, yunwa nakeji sosai dan haka na sakko ƙasa dan samun abinci, bbu kowa a falon dan hatta tvn a kashe take, haka kawai naji gabana yana wani irin faɗuwa, ban bari tsoron yayi tasiri a kaina ba na shige kitchen na haɗa tea na dawo falo ina sha. kamar daga sama naji shigowar Larai babu ko sallama, ta tsaya a kaina sai zazzare ido take tana waige-waige irin wanda bashida gaskiya ɗin nan, a fusace na ajiye cup ɗina dan tabbas ta bani haƙuri dan dama a tsorace nake "mahaukaciyar ina ce ke da zaki shigo min ɗaki bbu sallama and kuma daga gidan ubanwa kike"? shiru tayi jikinta na kyarma hawaye na bin kuncinta, cikin matsanancin fushi nace "ba dake nake magana ba"? shiru tayi still ta kasa faɗar komai idon ta akan ƙofar falon jikinta na wani irin rawa kamar mazari, bakinta na motsi tamkar mai son faɗin wani abu amma ta kasa faɗi sai dai ni Allah bai bani ikon Kallon ƙofar ɗakin ba sai ji nayi an kai min naushi a ƙasan marata, cike da azabtuwa na saki ƴar ƙara na sauke idona akan Salima dake riƙe da wata ƙwarya tana murmushi, ruwan cikin ƙwaryar ta zubamin daga haka ban sake sanin inda kaina yake ba, na sulale a wajen na ɓingire da bacci, wani mugun kallo Salima ta watsa ma Larai, da hannu ta nuna mata hanyar waje. cikin tsananin tashin hankali da damuwa da kuma tausayin Nu'aymah Larai tayi hanyar fita waje da gudu wasu zafafan ƙwalla na rige-rigen zubo mata, har ta kai bakin gate Salimah tabi bayanta ta dakatar da ita, sai da ta ƙare mata wani kallon ƙasƙanci sannan tace "inason kiyi nisa da gidan nan, kiyi shiru da bakinki, muddun maganar nan ta fito waje ko naji ta a bakin wani, hum!" daga haka tayi komawarta part ɗinta ta tsaya a bakin window tana tsumayen fitowar Nu'aiymah. bacci ne ya ɗauke ni na tsawon lkc, ban tashi farkawa ba sai ƙarfe ɗaya na dare, dafe kaina dake bala'in sarawa nayi, naji duniyar gabaɗaya ta fara juya min, na kasa fahimtar inda nake, na miƙe tsaye ina bin falon da kallo, wani irin kuwwa mai amo nake jiyowa a kunnuwa na tamkar ana kirana, waige-waige na farayi inason gano inda ake kirana sai dai babu kowa sai ni kaɗai, cike da son isa ga wanda yake kiran sunana na buɗe ƙofar falon na fito harabar gidan ina bin ko ina da kallo, kasancewar dare ne sosai babu kowa a harabar gidan sai kukan tsuntsaye dana karnuka, gudu-gudu sauri-sauri na ƙaraso bakin gate, cikin sa'a na tura ƙofar ta buɗe, haka kawai na tsinci kaina da son cire hijab ɗin jikina da takalma, gashin kaina ya zubo saman fuskata sai jini da ya fara bin ƙafafu na wanda bansan na meye ba! da mugun gudu na yanki babban titin har na fice daga layin mu, koda na juyo da niyar tsayawa na huta sai inji tamkar wani abun mai cutarwa ne ke biye dani a baya, babban burina a yanzu bai wuci na isa ga wanda ke kiran sunana wanda nake ji gabaɗaya ƙatuwar muryar sa ta cika min dodon kunne.
_dan soyayyar ki da ma'aiki s .a.w. kiyi share da comment._
'''#NU'AYMAH ABDULL'''