Bismillahi Rahmanin Raheem
HAMMAD SANAA
Page 1
Wattpad PhartyBBNagarta Writers Association
Work And Housing Estate, Gwarimpa garin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya. Birni da yake ciki da abubuwan more rayuwa.
Ƙarfe goma sha biyu na daren Talata. Safa da marwa take cikin ɗakin nata da yake ƙawace da abubuwan more rayuwa. Ta kasa zaman waje ɗaya duk da yadda take ji a jikinta, sai dai yanayin da take ciki ya danne wannan. A cikin lokaci ƙanƙani komai ya canza mata, ba haka ta yi buri ba. Sai dai ya ta iya? Ƙaddara da take tafe da burgewa ta canza mata komai.Ita kanta ba haka taso ba balle iyayenta da suka ci buri akanta. Allah kuma da ya tashi nuna musu ikonsa sai ya bada misali a akanta, wanda yanzu a wannan zamani kowa burinsa ya nuna burgewarsa ta hanyar nan.
"Me yasa ni?"
Ta faɗa tana zama daɓas saman gadonta ta dafe kanta. Hawayen da take maƙalewa suka samu damar zuba, tun da abubuwan suka faru kullum sai ta zubar da hawaye. Hukuncin da iyayenta suka yanke mata shi ne daidai, kuma babu yadda ta iya dole ta karɓa.
Kwantar da rabin jikinta ta yi saman katifar jin yadda kanta yake sarawa. Idanuwanta suka fara lumshewa, a haka har barci ya fizgeta. Ƙiran sallar farko cikin kunnuwanta ta farka, cikin sauri ta miƙe da ƙyar tana bin ɗakinta da yake hargitse da kaya da kallo. Ta rasa ta ina za ta fara haɗawa balle ɗaukar na amfani. Ganin tunanin ɓata lokaci ne ta miƙe ta wuce bathroom, alwala ta ɗaura ta fito ta fara nafila kafin a fara sallah, ta yi mintuna talatin sannan aka fara sallah ta miƙe ta gabatar, bayan ta idar ta zauna tana addu'o'i da neman mafita da yafiyar Allah. Ta jima tana addu'a ba ta tashi a gurin ba har sai da gari ya fara haske.
Tana zaune taji bugun ƙofa, zama ta gyara cikin dashashshiyar muryarta ta ce.
"Shigo ciki."Turo ƙofar aka yi Dattijuwar mace ta bayyana mai cike da kamala daga shigar jikinta, da kallo ta bi ɗakin har zuwa kanta, guri ta samu ta zauna a bakin gadonta tana kallonta.
"Kin yi barci Sanaa?"Girgiza kai ta yi idanuwanta na cika da hawaye, barci idan ba ɓarawo ba ba ya ɗaukarta. Ajiyar zuciya matar ta sauƙe ta ce.
"Kin san in da za ku je da nisa, akwai tafiya kuma har yanzu ba ki shirya ba."Kukan da Sanaa ta samu yi cikinsa ta ce.
"Momma don Allah ku yi haƙuri, ku fasa hukuncin nan a kaina ya yi tsauri.""Sam Sanaa haka ba zai faru ba, ke kika zaɓi haka. Don haka ki tashi ki shirya ku kama hanya."
Kuka bilhakki Sanaa take yi ta kasa cewa komai. Har tsawon yaushe za ta yi ta roƙar su su janye hukuncin nan a kanta.
"Momma ku ka jawo min komai fa."
Ta ce cikin kuka.Murmushin taƙaici Momma ta yi tana kallon ƴartan ta ce.
"Haka ne Sanaa. Sai dai da sa hannunki komai ya lalace."Girgiza kai Sanaa ta yi cikin kuka tana kallon mahaifiyarta jin abin da ta ce. Bayan duk sune sila yanzu kuma za ta ce da sa hannunta, sau nawa za ta faɗa musu cewa cin amanar yarda shi ne faruwar wannan ƙaddarar. Bayan sun nuna mata cewa hakan shi ne jin daɗin su yanzu kuma su ce ita ta jawo komai.
Shurunta ya sa Momma sake kallonta ta ce.
"Tashi ki shirya. Idan na barki babu abin da za ki yi. Tashi nace!"
Ta ƙarasa a tsawace.
Babu yadda Sanaa ta iya haka ta miƙe ta zare hijabin, da kayan jikinta ta wuce bathroom kai tsaye, ruwa kawai ta watsa ta fito daga ita sai towel, samu ta yi Momma tana haɗa mata kayanta cikin akwati biyu manya. Gaban mirror ta wuce ta shafa mai ta saka turare, wajen wardrobe ɗinta ta isa inda Momma take, abaya ta ɗauka da undies ta saka sannan ta zurma abayan. Jaka ƙarami ta ɗauka ta koma gaban mirror ta kwashe mayukanta da turare da komai da za tayi amfani da shi. Da ta gama ta koma wajen wardrobe din ta ɗauko purse nata mai ɗauke da kuɗi da ATM da ID card ta jefa ciki, ta ɗauki ledan magunguna masu yawa ta jefa ciki ta rufe. Lokacin Momma ta gama haɗa mata akwatin biyu da kayayyakinta."Wannan sun isheki har nan da watanni. Idan kin gaji da su za ki iya waya a siya miki sabi."
Faɗin Momma tana yin gaba ta ƙara da cewa,"ki fito kar Abbanki ya zo nemanki."Babu musu Sanaa tabi bayanta bayan ta ajiye ƙaramar jakar wajen biyun. Wayarta ta ɗauka ta fice a ɗakinta da bata son bari. Har down stairs ta sauƙa ta hango Momma tare da Abbanta suna magana daga alama maganarta ne. Jiki a sanyaye ta ƙarasa don ita kam ta zama mujiya a idanuwan su, basa duba da cewa sune silar faruwar komai da sunan jin daɗi a gareta, sai kuma hakan ya zamto mata illa.
Kasa zama ta yi da ta isa kanta a ƙasa, jin muryar Abbanta ya sa ta kallon shi."Zauna ki yi breakfast ku kama hanya."
Kujera ta ja ta zauna ta kasa taɓa komai. Ganin haka Momma ta tashi ta zuba mata ta tura mata plate ɗin gabanta da fork, tana ƙoƙarin ɗaukar plask na tea cikin sanyin murya Sanaa ta ce.
"Ki bar tean Momma."Bari ta yi ta zauna jin abin da ƴartan ta faɗa. Sanaa fork ɗin ta dauka ta fara cin dankalin kaɗan kaɗan, yunwar da ta kwana da shi yasa ta cusa kaɗan. Ganin haka Abba ya kwala ƙiran matar da take musu aiki. Cikin sauri ta fito a kitchen ɗin tana amsawa.
"Ki je ɗakin Sanaa ki ɗauko akwatinan da suke jere."
Momma ta ce jin Abba ya yi shuru yana bin Sanaa da ta fara hawaye da kallo. Babu wanda ya mata magana har matar ta dinga sauƙo da akwatinan tana kaiwa waje. Bayan ta gama ta dawo ta sanar musu ta koma kitchen. Miƙewa Abba ya yi haka Momma ma, jin maganarsa ta yi yana faɗin.
"Tashi muje."Kuka Sanaa ta fashe da shi ta kasa tashi.
"Abba don Allah ka yi haƙuri.""Sanaa kina ɓata kanki lokaci, ke za kiyi tafiyar rana. Ba za ki zauna a gidan nan ba sai lokacin da kika ɗauka ya cika. Ko kin manta ke kika zaɓi haka?"
Girgiza kai ta yi da sauri jin abin da ya ce, dole ta haƙura bisa hukuncin da ta fara ɗauka. Haka ta miƙe ta bi bayan mahaifinta da mahaifiyarta har waje filin gidan su. Driver ya gama saka komai nata a motar da za su tafi. Gurin motar suka dumfara haka ita ma da jikinta har rawa yake.
Tana isa ita kam gurin Abba ta nufa za ta durƙushe ƙasa ta roƙesa, ba za ta taɓa gajiyawa da roƙarsa ba ko zai janye. Fahimtar haka ya sa ya janye gefe yana kallonta.
"Sanaa ki daina wahalar da kanki damu.""Momma ki sa baki."
Ta ce tana kuka ta nufeta. Zuciyar Momma cike take da tausayinta amma haka take dannewa tun ranar da abin ya faru, wannan shi ne kaɗai mafitar su.
Hannun Sanaa ta kamo da ɗayar hannunta, ta buɗe motar da ɗayar hannunta ta ce.
"Shiga ku je Sanaa. Kar ki damu za muna waya."Tana ji tana kallon Momma ta taimaka mata ta shiga ta rufe ƙofar, hawayenta ya ƙi tsayawa. Abba ne ya sanarwa driver ya shiga su je, babu musu ya shiga ya kunna motar tare da yin riverse ya kalli get, ya sauƙa ya buɗe ya fitar da motar ya sake komawa ya rufe get ɗin sannan ya dawo ya shiga ya ja suka bar ƙofar gidan.
Alhaji Hussain da Hajiya Amina suna kallon fitar ƴar su suka koma falo yana faɗin.
"Anjima za a kawo min Mai Gadi Malam Aminu, wannan buɗe buɗe idan Isa driver baya nan akwai wahala.""Ya yi kyau."
Kawai Hajiya Amina ta ce tunanin ƴarta fal a ranta....
Sanaa idanuwanta ta lumshe a hankali ganin da gaske fa barin gidan su za ta yi, za ta tafi wani gurin can ta fara sabuwar rayuwa. A zuciyarta ta yarda cewa ƙaddarar bawa na canza masa cikin lokaci ƙanƙani, amma nata ƙaddarar ya zamto silar cin amana ne da ba ta taɓa tsammani iyayenta za su ƙi karɓa ba.
'To me ya sa suke ganin laifina kaso tamanin ciki ɗari? Suma da nasu gudummawar faruwar komai.'
Ta faɗa a ranta tana buɗe idanuwanta tare da bin garin sun da kallo da yake ɗauke da abubuwan burgewa na rayuwa. Tana kallo haka suka fita a garin tare da ɗaukar hanya zuwa inda suke ganin nan shi ne daidai da ita kafin wucewar komai. Shi ne rufin asirin su gaba ɗaya....
#vote
#freebook
#comments
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...