HAMMAD SANAA
Page 22
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookTuraki kallon Kulsum ya yi, ita ce ta fito amsa mishi sallamar da ya yi kamar kodayaushe, bai tsammaci ganinta ba sai Sanaa dalilin papern da ya aika mata, a tunaninsa ita za ta fito, hakan yasa ya ce.
"Ina take? Fatan tana lafiya?"Kulsum ta ji zafin dawowar shi kamar kullum don dalilin Sanaa, numfashi ta ja, kanta a ƙasa ta ce.
"Ta haihu kusan kwana goma yau."Da mamaki Turaki yana ci gaba da kallonta ya ce.
"Don Allah! Ki min izinin shiga ciki in gansu."Kulsum ba ta ƙara kalma ko ɗaya ba ta juya ciki. Da kallon mamaki ya bita da shi, ba ta ce mishi eh ko a'a ba. Ya lura yarinyar kullum babu fara'a a fuskarta.
'Ko me yasa hakan?"
Ya tambayi kan shi yana taɓe baki, haka ya ci gaba da tsayuwa akan idan ta wuce minti biyar ba ta dawo ba zai tafi gobe ya dawo.
...Kulsum tana shiga cikin gida ɗakin Sanaa ta wuce, anan ta samu Maah tana yi wa Nanah Firdaus wanka, Sanaa ta yi nata tana zaune tana cin abincin da Maah ta dafa mata, idan ka ganta tamkar ba jego take ba ko ta haihu, ta yi fes da ita ta dawo daidai yadda take kwanakin baya.
Kulsum ƙarasawa ta yi ciki wajen Maah, durƙusawa ƙasa ta yi tana faɗin.
"Turaki ya ce zai shigo su gaisa."Cak Sanaa ta tsaya da cin abincin da take ta kalli Kulsum, sannan ta kalli Maah jin me za ta ce.
Maah kallon Sanaa ta yi ta mayar kanta ƙasa tana shafawa Nanah mai ta ce.
"Ya shigo Sanaa?"Kai Sanaa ta ɗaga tana sunkuyar ƙasa, cikin zuciyarta tana jin farin cikin dawowar shi gareta.
Kulsum a tunaninta Sanaa za ta ce a'a kamar kullum, ganin ta amince yasa ta ƙara jin haushi sama da na farko. Miƙewa ta yi ta fice a ɗakin zuwa waje. Tsaye ta samu Turaki har lokacin, ƙarasawa ta yi wajen shi sannan ta ce.
"Ta ce ka shigo."
Tana faɗin haka ta juya ta wuce ciki.Turaki ƙafafunsa yaja, bayanta ya bi zuwa cikin gidan tare da sallama a bakinsa, filin gidan babu kowa. Ganin ta nufi wani ɗaki yasa yabi bayanta yana tsayawa daga bakin ƙofa ya yi sallama.
Muryar Sanaa ya ji ta amsa daga ciki tana faɗin.
"Ka ƙaraso ciki."Labulen ɗakin ya ɗaga yana sake sallama ya shiga ciki. Amsawa Sanaa ta yi tana gyara zama, ta nuna sallayar da Maah ta ɗauko ta shimfiɗa ta ce.
"Ga gurin zama."Babu musu ya zauna yana binsu da kallo ita da Nanah, sun yi kyau abinsu. Kulsum ficewa ta yi tuni.
Murmushi ya yi ya kalli Sanaa ya miƙa hannunsa ya ce.
"Kawota na ganta, she's so pretty."Sanaa dauƙar Nanah ta yi wacce take cikin towel sai bacci take bayan mata wanka, miƙa mishi ita ta yi ya karɓa yana kallonta ya ce.
"Ma sha Allah, Allah ya raya ya ɗayyabata. What's her name?""Nanah Firdausi."
Sanaa ta faɗa tana amsawa da amin a zuciyarta. Ji ta yi Turaki ya sake faɗin.
"Sannu, haihuwa akwai wahala ko?"Murmushin dole Sanaa ta sake tana sunkuyar kanta ƙasa, cike da kunya ta ce.
"Sosai ma."Shi ma murmushin ya yi ganin ta fara sakewa da shi ya ce.
"Allah ya ba ku lada."A zuci Sanaa ta amsa har lokacin kanta a ƙasa. Shuru ne ya gifta tsakaninsu duk sun rasa abin cewa. Ɓangaren Turaki ya zo domin su yi magana ya tarar wannan lamari, Sanaa kuma tana jira ta ji ta ina zai fara mata tambayoyin da take tunanin ta ina za ta fara amsa su.
Ganin shurun ya yi yawa yasa ya miƙa mata Nanah Firdausi, karɓarta Sanaa ta yi ta kwantar da ita, kallon Turaki ta yi da ya miƙe tsaye.
"Za ka koma har?"
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...