HAMMAD SANAA
Page 14
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookSanaa tana kwance a ɗakinta, minti minti take duba agogon cikin wayarta da babu caji sosai, duk da tana sawa a caji lokaci zuwa lokaci, amma yana yin kaɗan take cirewa, don ba amfani take da shi ba.
Tana gani ƙarfe biyar ta yi ta miƙe, hijabi sabo ta ciro cikin akwatinta, sakawa ta yi saman riga da skirt na ƴar kanti da yake jikinta.
Tana sawa ta ɗauki flat shoe ɗinta ta fito waje, Maah ta hango zaune a taburma. Kusa da ita ta ƙarasa ta jawo kujera ta zauna."Ya jikin? Fatan babu wani matsala?"
Maah ta tambayi Sanaa tana binta da kallo.
Ɗaga kai Sanaa ta yi alamar babu komai, matar tana burgeta don halarcinta, ta iya kula da mutum da damuwa da damuwarta, ba kamar nata iyayenta, waɗannan suka manta da ita da lamarinta. Idanuwanta ta ji ya cika da hawaye tuna ahlinta. Ta yi kewarsu sosai, bayan su har Uncle da Ilham da suka mata nisa.
Sallamar Kulsum yasa a hankali tasa gefen hijabinta ta share hawayenta. Ɗago kanta ta yi, gani ta yi Kulsum ta shige ɗaki, ba ta jima ba ta fito bayan ta ajiye allonta.
Wajen da suke ajiye bucket na deɓo ruwa ta nufa ta ɗauki ɗaya, waje ta nufa ba ta nemi Sanaa ba ko rakiyarta.
Sanaa da ido ta bita, ganin za ta fice ta miƙe da sauri tabi bayanta. Gani ta yi tayi nisa, cikin sassarfa ta bita ta isota suka jera.
Kulsum ganin Sanaa ta dakata da tafiyarm
"Kin ji sauƙi ne?" Ta tambayeta tana binta da kallo.
Ɗaga kai Sanaa ta yi tana yin gaba ta fara tafiya.
"Sosai ma."Da sauri Kulsum tabi bayanta, bata so haka ba, tafi so su biyun su haɗu kamar kullum, duk da har lokacin tsoron shi bai bar ranta ba, kuma Sanaa yake tambaya ba ita ba, amma hakan take ji tafi son su biyu su kasance tare, ta ci burin su haɗu su biyun.
Shuru suke tafe babu wacce ta yi magana. Sun zo wucewa ta wajen bishiyar Sanaa ta juya taga wayam babu kowa. Ɗauke kai ta yi tana kallon Kulsum.
"Ina Turaki? Ko bai fito ba?""Ban sani ba, kuma ina jin ya koma."
Kulsum ta faɗa ba ta ko kalli hanyar bishiyar ba. Shuru Sanaa ta yi jin abin da Kulsum ta faɗa.
A haka suka ƙarasa wajen deɓar ruwan, bayan Kulsum ta ɗeba suka kama hanyar komawa, suna isowa layin bishiyar Sanaa ta canza hanya tana nufar wajen.
Da sauri Kulsum tabi bayanta tana faɗin.
"Me za ki yi? Idan ya zo fa.""Idan ya zo sai na bar mishi wajen shi."
Sanaa ta ce ko juyawa ba ta yi ta kalleta ba.
Kulsum ka sa hanata tafiya, bin bayanta ta yi har ƙarƙashin bishiyar suka shiga, kamar kullum da sanyi sosai a wajen sai kaɗawa yake.
Kulsum sai lokacin ta kalli bishiyar da kyau, bishiyar ceɗiya ce mai cike da ganye sosai.
Sanaa kam ido ta lumshe ta buɗe tana kallon reshen bishiyar. Maganar Kulsum taji ta juya tana kallonta."Mu tafi, ga shi can zuwa.."
Faɗin Kulsum tana nuna mata Turaki da ya dumfaro bishiyar. Kulsum mamaki take ashe dama yana nan bai tafi ba, ko don da safe take fitowa yasa basa haduwa.
Sanaa kanta ta ɗauke, tana juyawa gefe ta ce.
"Bar shi ya ƙaraso, mu ji kuma me zai ce yau.""Ni dai mu tafi."
Kulsum ta faɗa da sauri, duk da ƙasan ranta yana danne tafiyar akan tsayuwar.
Shurunta ya yi daidai da isowar Turaki, kai tsaye wajen Sanaa ya nufa yana fuskantarta.
"Assalamu alaikum."
Ya mata sallama, fuskarsa cike da murmushin da yake fitowa daga zuciyarsa. Ya ji farin cikin ganinta cikin ƙoshin lafiya.
Sanaa kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kai. Yana sanye da yadi ruwan kasa, kansa da hula, kayan ya mishi kyau. Baƙi ne shi, amma baƙinsa mai kyau ne, don yana ɗauke da dogon hanci da madaidaicin baki, ba shi da ido sosai amma yana da kyan gani, ba shi da saje sai gemun da ya ajiye ba shi da yawa.
Sallamar da ya yi yasa ta sake kallonshi, ba ta ɗauke idonta ba cikin nashi ta ce.
"Walaikum salam. Lafiya?"
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...