Page 7

279 32 2
                                    

HAMMAD SANAA

Page 7
Wattpad PhartyBB
NWA
#FreeBook

"Allah ka yafe min."
Sanaa ta faɗa a fili tana kai hannu ta sake ɗauke hawayen da ya gangaro mata saman kumatunta. Sallama ta ji daga bakin ƙofa na Kulsum. Da sauri ta hau goge hawayen fuskarta tana cewa.
"Shigo ciki."

Ciki yarinyar ta shigo tana cewa Sanaa.
"Kawu yana miki magana."

Sanaa kallon Kulsum ta yi don ba ta fahimta ba, ganin haka Kulsum ta ce.
"Wanda ya kawoki."

Jin haka Sanaa ta miƙe tana gyara mayafinta tana cewa.
"Bai tafi ba dama?"

"Eh, ya so juyawa tun safe Baah ya tsayar da shi."
Kulsum ta ce tana yin gaba Sanaa tabi bayanta. Har ƙofar gida suka fita, anan suka tsame shi da Baah a tsaye, kusa da su Sanaa ta matsa tana duƙawa ta gaishe da Baah, da ya amsa suka gaisa da driver yana faɗin.
"Hajiya zan koma, ki yi ta haƙuri a yadda kika samu kanki, balle nasan Maah za ta kula dake da Kawu. Idan kina buƙatar wani abu a gida, ki faɗawa Momma zan kawo miki. Komai zai wuce kamar yau ne."

"Na gode."
Sanaa ta ce muryarta ya karaya tana neman kuka. Shi ne ya fara fahimtarta bayan samuwar ƙaddararta har ya nemi taimaka mata, shi ya ɓullo musu da wannan hanyar da ta zaɓe shi akan wanda iyayenta sukasa tabi.
Tana kallo ya shiga motar ya kunna yana yin riverse yaja yabar harabar wajen su, sai da ta daina ganin motar kafin a hankali taja ƙafafunta cikin sanyin jiki ta koma cikin gidan, ɗakinta kai tsaye ta wuce tana faɗawa saman katifar ta fashe da kuka. Tunani take ta ina za ta fara rayuwa a gurin da babu nata ko ƙwaya ɗaya. Babu Momma babu Abbanta balle makusantarta.

***

Abuja

Daren jiya bai yi bacci ba, ido biyu ya kwana a dole shi zai yi gadi, duk yadda bacci ya so kwasar shi haka ya daure ya ƙi. Sai bayan sallar asuba da ya gabatar, sannan ya shige ɗaki tare da kwanciya saman babbar katifar ɗakin da aka ba shi. Ai kuwa tuni bacci ya ɗauke shi, bai san inda yake ba har ƙarfe sha ɗaya ya yi juyi tare da jawo wayarsa yaga sha ɗaya da kwata.
Da sauri ya miƙe zaune yana murza idanuwansa da suke cike da gashin ido zara-zara. Hamma ya yi tare da rufe bakinsa yana salati a zuci.
Miƙewa ya yi tsaye yana miƙa don ji ya yi jikinsa duk ciwo. Fita waje ya yi yana duba harabar ajiye motoci yaga Alhaji bai fita ba, hamdala ya yi ya zauna bakin baranda. Ya share mintuna goma zaune yana bin filin gidan da kallo kafin ya miƙe ya shiga ɗakinsa.
Zama bakin katifar ya yi yana ɗaukar wayarsa, babu ƙiran kowa. Cikin wayar ya shiga ya laliɓo lambar ƙaninsa ya ƙira. Ringing biyu ya ɗauka ta ɓangaren shi ya yi sallama yana faɗin.
"Ina kwana Yaya? Ya hanya?"

Amsawa ya yi yana sauƙe numfashi ya ce.
"Lafiya lau Sultan. Ina Ummi?"

"Ga ta kusa da ni, na shigo gaisheta kenan tana faɗin in ƙiraka."
Sultan ya amsa ta ɓangaren shi cikin sauri.

"Ba ta wayar."
Ya faɗa mishi, yana ji ya cire wayar ya miƙa mata. Jin ta karɓa ya yi saurin cewa.
"Ina kwana Ummi?"

"Lafiya lau. Fatan an yi nasara?"
Ta amsa cikin sanyin jiki jin muryar ɗanta mafi soyuwa a ranta.
Numfasawa ya yi ya saki murmushi don kwantar mata da hankali ya ce.
"Na yi Ummi. In sha Allah komai zai zo da sauƙi."

Yana ji ta sauƙe gwauron numfashi ta ce.
"Haka ne da yardar Allah. Allah ya ƙara taimaka maka."

"Amin Ummi. Ki ba Sultan wayar."
Ya faɗa mata, bayan ta miƙa mishi ya ce masa.
"Ina Bashar da Bushara?"

HAMMAD SANAADonde viven las historias. Descúbrelo ahora