HAMMAD SANAA
Page 2
Wattpad PhartyBB
Nagarta Writers AssociationDa sauri ta fito a motar tana kwasa da gudu ta yi cikin falon gidan. Tun a falo ta yi cilli da jakar makarantarta tare da cire ƙaramin baby hijab da yake wuyanta. Saman upstairs ta nufa ganin babu kowa a falon tana kwala ƙiran.
"Abba! Abba!!"Jin shuru yasa tana hawa ta nufi ɗakin mahaifinta tare da addu'a da fatan ya dawo tamkar yadda aka sanar mata. Cak ta tsaya a ƙofar ɗakin tana bugawa.
"Abba ka dawo? Abba na shigo?"Daga ciki taji an amsa mata.
"Shigo ciki Sanaa."Jin muryar Abbanta ta buɗe ƙofar da sauri tana shiga. Cikin sassarfa ta ƙarasa wajen shi tana faɗawa jikinsa.
"Sannu da dawowa Abbana, na yi kewarka."Da murmushi ya shafa kanta yana cewa.
"Ni ma haka Sanaa."Ɗagowa ta yi ta kalleshi tana murmushi, sakinta ya yi ya riƙo hannunta suka nufi waje yana cewa
"Muje Momma ta canza miki kaya."Waje suka fita har zuwa ɗakinta suka shiga sannan ya sake hannunta.
"Bari in turo miki Momma.""Zan iya Abba."
Sanaa ta faɗa tana fara cire rigarta, a ganinta shekarunta goma sha biyar za ta iya komai. Ganin haka Abba ya nufi waje yana faɗin.
"To idan kin gama ki sameni a falo."Cikin sauri ta canza kayanta zuwa ƴar kanti, ba tabi ta kan sallar azahar da ya sameta a makaranta ba ta fice a ɗakin. Falon ƙasa ta samu Abbanta da Momma zaune, kusa da Abba ta zauna tana faɗin.
"Abba tsarabata, i hope ka kawo min abin da na faɗa.""Na kawo, da dare zan ba ki."
"Na gode sosai Abbana."
Ta faɗa cikin murna. Momma na kallon su tana jin farin cikin soyayyar uba da ƴar.
Haka suka zauna tare har la'asar ya miƙe ya hau sama ya yi bai nufi masallaci ba, haka Momma ma. Sanaa ba ta yi tunanin zuwa ba har sai da Momma ta zo ta korata ta wuce tana gunguni. A gurguje ta yi sallar ta sauko falon ta ci gaba da zama wajen Abbanta tana kallo, shi kam waya yake, rabi kuma yana hira da matarsa Hajiya Amina.
Har dare suna tare, da Sanaa taga dare ya yi ta sake maumaita Abba maganar tsarabarta, dole ya miƙe suka hau sama zuwa ɗakinsa har Hajiya Amina. Wardrobe nashi ya buɗe ya ciro kwalin iPad madaidaici ya miƙa Sanaa da take tsaye gefensa.
Ihu ta fasa tana karɓa ta rumgumesa.
"Thank you Abba, i love you my dearest father. I'm really proud of you.""I love you too my daughter. Promise me ba zai yi failing karatunki ba."
Ya faɗa yana sakinta ya dafa kafaɗunta yana kallonta. Kai ta ɗaga tana murmushi cikin farin ciki.
"In sha Allah Abba i promise you that.""Good girl."
Ya faɗa yana jan kumatunta. Gurin Momma da take zaune bakin gado ta ƙarasa tana nuna mata, cikin murmushi Momma ta ce.
"Sai ki dage dai da karatu banda wasa zallah.""In sha Allah Mommana."
Ta ce tana fita da sauri tabar ɗakin. Ɗakinta ta shiga ta haye saman gado tare da buɗewa ta fara kiciniyar kunnawa, tsaf kuwa ya kawo duk da ba ta sa caji ba ta hau taɓe taɓe a ciki. Ta jima tana daddannawa kafin ta miƙe tasa a caji, bathroom ta wuce ta sakarwa kanta shower ta yi wanka, ta ɗaura towel ta fito, rigar barci ta sa ta hau gadonta tana yin ɗaiɗaiya ta kwanta. Babu sallar isha'i balle addu'ar bacci.
Da safe sai ƙarfe shida ta farka, bathroom ta wuce ta yi brush tare da yin wanka sannan ta ɗaura alwala ta fito, sallar asuba ta gabatar bayan ta idar ta hau shirin makaranta, kafin ta gama sai da ta hargitsa ɗakin gaba ɗaya. Tana kammalawa ta cire iPad ɗin a caji tasa a drower ta ajiye, sannan ta ɗauki jakar makarantarta ta fita.
Falon shuru alamar babu wanda ya farka cikin iyayenta, dinning ta wuce tana kwalawa ƴar aikin gidan ƙira.
Cikin sauri matar ta fito zuwa wajenta tana amsawa."Ki zuba min abinci."
Sanaa ta ce tana jan kujera ta zauna. Matsawa matar ta yi ta zuba mata dankali da ta soya da ƙwai ta ajiye gabanta, za ta haɗa mata tea ta dakatar da ita, bari ta yi ta wuce kitchen ta haɗa mata lunch box nata wanda bayan indomie da ta dafa da kwai ta saka mata juice da biscuits babba ɗaya, haka ake mata kullum. Bayan ta haɗa ta ɗauka ta fito ta ajiye mata saman dinning ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta.
Sanaa tana gama ci ta mike ta zari tissue ta goge bakinta tare da ɗaukar lunch box nata ta fita, samu ta yi driver ya yi parking yana jiranta, motar ta shiga, shi ma ya shiga yana danna horn Mai Gadi ya buɗe sannan yaja motar suka bar harabar gidan.
A ƙofar makarantar su FUNTAJ ya ajiyeta ta shiga ciki kafin ya bar wajen.Sanaa Hussain kenan ƴar gata gaba da baya wacce iyayenta sai da suka shekara goma da aure kafin su sameta.
Alhaji Hussain ɗan siyasa ne babba da sunansa ya zaga garin, haka Hajiya Amina babbar Malama ce a School Of Nursing.
Suna son Sanaa kasancewar sun jima kafin su sameta, suna bata dukkan gata da kulawa. Makarantar kuɗi take yayinda islamiyya kuma Malami suka ɗauka mata yana koya mata karatun AlQur'ani da salloli kaɗai, hakan yasa tafi ba boko ƙarfi musamman da iyayenta suka sa mata burin zama likitar mata, wanda mahafinta ya mata alƙawarin turata ƙasar waje karatu, yayinda yanzu tana aji uku na Secondary School....
Ƙarfe biyu ta dawo gida ta samu babu kowa, sama ta hau zuwa ɗakinta ta samu an gyara mata tsaf kamar kullum idan ta hargitsa. Kayan makaranta ta cire zuwa kayan gida, tana canzawa ta fita zuwa ɗakin Momma, samunta ta yi tana zaune gabanta takardu yayinda da idanuwanta suke sanye da gilashi.
Kusa da ita ta zauna tana ɗaukar text book da yake ajiye.
"Momma ina Abba?""Kin ci abinci?"
Momma ta ce tana ɗagowa ta kalleta. Gani ta yi ta girgiza kai, haɗa rai ta yi tana kai hannu ta cire gilashin idonta.
"Tashi kije ki ci, kinsan bana son zamanki da yunwa."Turɓune fuska Sanaa ta yi tana kallon Momma.
"To ina Abba?""Ya fita sai dare zai dawo. Oya get up!"
Momma ta faɗa tana nuna mata alama ta tashi. Dole ta miƙe tana gunguni ta ajiye text book ɗin ta nufi ƙofa, tasa kai ta ji Momma ta sake cewa.
"Kuma maza ki yi sallah."Ƙafa ta buga ta fice a ɗakin, ƙasa ta sauka ta zuba abincin kaɗan ta ci tabar wajen haka, ɗakinta ta wuce ta shiga bathroom ta yi alwala a gurguje ta fito ta yi sallah. iPad nata ta ciro a drower ta hau saman gado tana fara dannawa.
Haka ta wuni a ɗaki har dare ta fita lokacin Abbanta ya dawo. Daren har ƙarfe sha ɗaya kafin ta tafi ɗakinta don bacci.Kamar yadda Sanaa take rayuwarta haka komai ya ci gaba da tafiya mata cikin kwanciyar hankali da gata, karatu take sosai don tana da burin karantar likita. Ba ta neman komai ta rasa, Abba duk tafiyar da zai yi da tsarabar da zai kawo mata, a wannan lokaci ya saya mata babbar waya ganin ta isa riƙewa, tare da kashedin banda shige shige. A haka abubuwan suka ja har tsawon shekaru uku yau, a wannan rana ake murnar shagalin yaye ɗalibai da suka gama, ciki har da Sanaa.
Iyayenta sun halarta bikin ƴar su ƙwaya ɗaya. Sanaa taji daɗi musamman da aka ƙirata a matsayin ɗalibar da tafi kowa fita da maki mai kyau, mai kwazo da kula da karatu.
Ta yi farin ciki haka iyayenta ganin abin da suke so ƴar su tana da shi. Haka aka gama shagalin biki suka dawo gida.
A falon suka zauna gaba ɗaya suna tayata buɗe kyautattukan da ta samu. Sanaa tana zaune gefen su tana shan chocolate tana kallon su ta ce."Abba maganar party? Na faɗawa Uncle da Ilham."
Dakatawa ya yi da abin da yake yana kallonta ya ce.
"Wa ya ce ki faɗa musu?"Karya wuya ta yi tana rau rau da ido.
"Sorry Abba. Gani na yi family ya kamata su zo."Numfashi Abba ya sauƙe yana cewa....
...
#KeepCommenting
#KeepVoting
#Love
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...