HAMMAD SANAA
Page 43
Na Pharty BBHammad da ƙyar ya iya saita nutsuwar shi yabi jam'in sallah a masallaci da ya nufa bayan shigar Sanaa cikin gida. Ya rasa wani irin yanayi yake ciki na farin ciki, ji yake tamkar ya bita cikin gidan ya rumgumeta ya nuna mata tsantsar farin ciki da ya shiga na haɗuwa da ita, bayan nema da damuwa mai cike da wahala da ya shiga na rashinta.
Har lokacin idanuwansa suna hango mishi Nanah da take hannunta tana riƙe da ita, bai bambance mace ko namiji ba ne, kuma bai tabbatar nasa ba ne amma rabi da kwata zuciyarsa ta bashi tabbacin cewa nasa ne, shi ne uban ɗanta ko ƴarta don yasan shi kaɗai ne ya kusanceta a yadda take har ta samu ciki, don bai kai ace ta yi aure ta haifi kamar wannan ba tun da duka-duka idan ya lissafa yanzu wata goma cib da faruwar komai.
Ana idar da sallah ya dawo gida cikin sauri, a farar kujera ya zauna yana baza ido ko zai ganta, sai dai tsawon mintuna babu ita ko alamarta. Ƙofar falon su ya zubawa ido tamkar yana ganin za ta fito amma shuru.
Ɗauke idanuwansa ya yi yana ci gaba da zama har tsawon awanni. Ƙarfe sha ɗaya ya miƙe ya shige ɗakinsa ganin dare ya shiga kuma ga sanyi ya fara sauƙa.
Saman katifarsa ya hau ya kwanta, idanuwansa ya lumshe tamkar mai bacci, a hankali rayuwar da ya gudanar bayan barin Sanaa makaranta ya fara dawo mishi.
***Tun yana baza ido don ganin Sanaa har ya zo ya haƙura. Tun ranar bai ƙara ganin ko mai kamarta ba, duk inda yasan zai sameta ya duba babu ita ko alamarta, hakan yasa dole ya haƙura ya mayar hankali kan karatun sa.
Ya kauracewa Khaleed da Amir ganin sun fara wasa da karatun su, musamman Amir da ya fara ɓullo da wasu dabi'u. Har lokacin ya ka sa tunkarar Khadeeja akan abin da ya faru, burinsa kawai ya samu Sanaa.
Haka ya mayar hankali kan karatunsa har na tsawon watanni uku, a haka suka yi jarabawar ƙarshe suka gama suka fito da sakamakon manyan likitoci. Kwana uku da gamawar su suka bar ƙasar shi da Khaleed, anan suka bar Amir don shi da saura.
Hammad tun da ya dawo gida hankalinsa ya ka sa kwanciya. Aikin da mai martaba ya samar musu a babban asibiti da kyar yake zuwa, shi ma baya awanni biyar yake dawowa ya kulle kanshi a ɗaki, duk ya rame sai haske.
Gimbiya Rabi'atul Adawiyya ta ka sa gane kan yaronta duk da dama haka yake, amma tasan yana sake mata ba kamar sauran jama'a ba hatta Mai martaba.
Haka ɓangaren mai martaba da ya ga sauyi tare da Hammad. Dole ya samu Gimbiya Rabi'atul Adawiyya da maganar.
Shuru ta yi don ita kanta ta rasa me ke damun shi. Maganar mai martaba yasa ta kalle shi in da ya sake tambayarta. Girgiza kanta ta yi fuskarta cike da damuwa ta ce.
"Ni kaina ban sani ba. Sai dai mu gwada tambayar shi.""Ki sanar mishi anjima ina neman shi, har da ɗan uwan shi Khaleed."
Faɗin Mai martaba yana miƙewa ya fita, dogarai suka bi bayan shi.
Gimbiya Rabi'atul Adawiyya baya ta yi ta gishingiɗa, idanuwanta ta lumshe damuwar da Hammad yake ciki yana jefata cikin tunani da damuwar ita ma.
Tunawa da cewa mai martaba ya ce a sanar mishi yana neman shi yasa ta buɗe ido, ta kalli Baiwa Samira ta ce.
"Ki duba Hammad yana nan ki sanar mishi saƙon mai martaba, har da Khaleed.""An gama ranki daɗe."
Faɗin Samira ta miƙe ta fita. Ɓangaren Hammad ta nufa, dogarai da suke tsaye a bakin falon su ta gaisar sannan ta sanar musu saƙon Gimbiya Rabi'atul Adawiyya.
Ɗaya ne ya shiga ciki ya fito ya faɗa mata ya sanar mishi, a haka ta isa ɓangaren su Khaleed ta sanar mishi, sannan ta koma bangaren Gimbiya Rabi'atul Adawiyya ta faɗa mata.Hammad tun da saƙon Gimbiya ya same shi ya shiga tunani akan me ya faru mai martaba yake neman shi? Shin damuwar da yake ciki ya fara bayyana ne ko ko wani abu daban ne?
Hakan ya ƙara jefa shi tunani da ya haddasa mishi ciwon kai, wanda yasan duk na damuwa ce, dole ya nemi magani yasha ya kwanta.
Sallar la'asar yasa ya miƙe ya shiga bathroom, alwala ya ɗaura ya fita a ɗakinsa. Suka haɗu da Sultan a falo suka fita tare zuwa Masallaci da yake cikin masarautar.
Bayan an idar da sallah suka fito, Hammad yabi bayan mai martaba. Sultan ganin haka shi ma yabi bayan shi yana mishi surutu wanda ko a Hammad bai tanka ba, shi kuma ko a jikinsa don ya saba da halin shariyar Hammad duk da a baya yana tanka mishi da eh da a'a idan ta kama ma suna taɓa hira, amma ban da yanzu.
A haka suka isa fadar mai martaba, suka nemi waje suka zauna tare da gaishe da mai martaba cikin girmamawa.
Mai martaba ya amsa musu, ya kalli dogari da yake gefensa ya ce.
"Ina neman kaɓewa da su."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...