Page 38

270 45 38
                                    

HAMMAD SANAA

Page 38
NWA



Sanaa dakatawa ta yi da tafiyar da take yi, a hankali ta dawo baya ta zauna saman gadon Khadeeja wanda ta fi kusa da shi. Idanuwanta sun cika da hawaye suna neman zubowa ta kalli Khadeeja.
Khadeeja da sauri ta ƙaraso ta zauna gefen Sanaa tana binta da kallo. Sai da ta ƙare mata kallo tsaf sannan tace.
"Kar ki ce min wani abu ya shiga tsakaninku?"

Sanaa idanuwanta ta runtse hawayen suka samu damar zuba a fuskarta, da ƙyar ta ɗagawa Khadeeja kai, cikin rawar murya ta ce.
"Friendy kin ga illar da nake faɗa miki na kusancinmu da shi, ke ki ka fara nuna min illar hakan, kar na zama abin kwatance abin nuni da ƙyama, amma don cikar burinki ki ka ce min babu abin da zai faru, ga shi tun ba'a je ko'ina ba komai ya kwaɓe. He disvirgin me Friendy."

"Burina ko burinmu Sanaa? Don ƙaruwarmu da cigabanmu na nemi hakan. Ko kafin nasan taimakonmu zai yi ban ce ki guje shi ba. Kin bani mamaki da ki ka tsaya namiji ya yaudareki ya kusanceki Sanaa, kodayake ke ɗin wawiya ce."
Khadeeja ta faɗa tana ma Sanaa wani mugun kallo.
Sanaa kukanta ne ya tsaya jin Khadeeja tana neman ɗaura mata laifi, wanda kuma duk ita ce ta jawo mata hakan ko da dasa hannunta na yarda da ta yi ya kusanceta, ita ce tace ta kulashi don su more shi. Murmushin taƙaici Sanaa ta yi, tasa hannu ta share hawayenta sannan ta ce.
"Tabbas na tafka wauta da na bari hakan ya shiga tsakaninmu ban yi ƙoƙarin kare kaina ba, amma ki yarda Khadeeja dasa hannunki ko da akwai nawa. Kuma don Allah a matsayin ki na ƙawata wacce na yarda da ita nasan za ki rufa min asiri, don Allah ki rufa min asiri karki bari kowa ya ji me ya faru musamman a ƙasarmu, ƴan uwanki ko nawa. Momma da Abba nasan za su fahimce ni su rufa min asiri."

Khadeeja murmushi ta yi, tana kallon Sanaa ta ce.
"Kina ganin idan na rufa miki asiri nan gaba ba zai fito ba ne. To aure za ki yi, duk wanda ya sameki ba budurwa ba sakinki zai yi ko ya koreki korar kare."

"Ba zan yi aure ba."
Sanaa ta faɗa da sauri zuciyarta tana zafi, maganar da Hammad ya faɗa mata ya dawo mata. Takai hannu share hawayenta da ya zubo ta sake faɗin, "Zan ƙare rayuwata a karatu, kuma nasan Momma da Abba ba zasu matsa min na yi ba, don su ma burinsu na yi karatu mai zurfi."

"Da yafi miki."
Khadeeja ta faɗa, tana danne zuciyarta ta dafa kafaɗar Sanaa ta ce.
"Shi kenan, kar ki damu. Tashi ki yi wanka ki yi sallah."

Sanaa miƙewa ta yi ta taka a hankali ta shiga bathroom, ruwan zafi ta tara ta shiga ciki, sai da ta gasa kanta sannan ta watsa ruwa ta ɗaura alwala, towel ta jawo ta ɗaura ta nufi ƙofa don fita. Hannu takai handle ɗin don buɗewa ta ji magana ƙasa ƙasa yana tashi, dakatawa ta yi tasa kunnuwanta don ji.
Wani mugun bugu zuciyarta ta yi jin abin da ya fito daga bakin na waje. A hankali ta buɗe ƙofar tana fitar kanta waje, ji ta yi an ci gaba da maganar da ake yi don ƙofar bai yi ƙara ba balle ya ankarar da me yi.
Takawa ta yi a nutse yadda babu sauti ta tsaya a bayanta, ta ci gaba da sauraran me take faɗa ciki da farin ciki tana dariya. Sanaa ji ta yi duniyarta ta tsaya, komai ya tsaya cak nata sai zuciyarta da take mugun bugawa da ƙarfi.
Ba ta taɓa tsammanin haka ba daga wajen wacce ta ɗauki yarda da amanar tsayuwarta ta bata, wacce yanzu ta gama faɗa mata za ta rufa mata asiri, wacce ta taimakawa don so da ƙauna da take mata tsakani da Allah.
Sanaa yadda take jin zuciyarta ba ta san lokacin da takai hannu ta fizgota ta juyo da ita tana kallonta. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu ta kwaɗa mata mari ta cafko wuyar rigarta. Cikin tsawa take faɗin.
"Uban me na miki a rayuwa za ki saka min da haka? Na ɗauke ki matsayin ƴar uwa, ƙawa shaƙiƙiya da duk duniya bani da kamarta, na miki gata da arzikin mahaifina da nawa. Me yasa za ki min haka? Me yasa?"

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now