HAMMAD SANAA
Page 8
Wattpad PhartyBB
NWA
#FreeBookSanaa zaune a ɗakin bayan shigarta, a bakin katifa ta zauna ta yi shuru. Ganin lokaci ya ja ta miƙe ta isa wajen akwatinta. Jakarta ƙarami ta ɗauke ta ajiye gefe, kwantar da ƙaramin akwatinta ta yi ta buɗe, kaf ta gama dubawa babu towel a ciki, haka ta kwantar ɗayar ta buɗe, shi ma babu sai kayan sawa da duk dogin riguna marasa nauyi. Kamar ta yi kuka ta zauna daɓas a ƙasa.
'To me zan ɗaura na yi wanka?'
Ta faɗa tana sake bincike. Kaf ta duba babu towel Momma ba tasa mata ba, ta ji haushin hakan. Haka ta cire riga ɗaya marar nauyi da mayafinsa mai ɗan faɗi ta ajiye a saman katifarta. Undies ta ciro ta ajiye sannan ta rufe akwatin ta mayar ta ajiye.
Ƙaramin jakarta ta buɗe ta ciro turarukanta da lotion ta zuba saman gadon, ƙaramin akwatin ta sake buɗewa, sabulun wankarta mai ƙamshi ta ɗauka da soso sabo da Momma tasa mata a cikin gidansa mai kyau. Daga haka ta rufe ta ɗaura jakar saman shi.
Miƙewa ta yi ta ɗauki basket ɗin wankar ta fita waje, anan ta samu Kulsum na wanke wanke. Kusa da ita ta ƙarasa ta tsaya sannan ta ce.
"Ina son yin wanka. Babu bucket?"Kallonta Kulsum ta yi tana miƙewa sannan ta ce.
"Akwai, bari in zuba miki."Murmushi Sanaa ta yi, shi ne na farko bayan zuwarta ta ce.
"Na gode sosai."Haka Kulsum ta shiga bangida ta ɗauko bucket ta fito, ruwa ta cika a ciki ta ɗauka takai banɗakin ta fito, wajen yin aikinta ta koma ta faɗawa Sanaa cewa.
"Na gama.""Na gode miki."
Sanaa ta faɗa tana wucewa.
Cikin bangidan ta shiga, turus ta tsaya duk da jiya ta shiga. A wanke babu datti ko ƙazanta, siminti ne lailaye a ciki, buɗewar saman ya ba shi damar bushewa. Nata bangidan ta tuna, wanda yake ɗauke da komai na buƙatar wanka da ɗan Adam mai ji da gata zai buƙata. Uwa uba gurin bahayar ne bai mata ba, yadda za ta iya tsugunnawa idan ya zo mata take tunani.
Jiki a sanyaye ta shiga ciki sosai tana ture ƙofar langa-langar ta rufe, sosonta da sabulu ta ajiye. Kayan jikinta ta cire ta rataya a ƙofar, haka ta zauna saman kujerar ƙarfen dalma, bucket ɗin ta jawo kusa da ita tare da kamfato ruwan ta fara wanka. Cikin sauri ta yi wankar don iska yana buginta tana jin sanyi. Tana gamawa ta mayar doguwar rigar jikinta tana ɗaukar basket ɗin wankarta ta buɗe ƙofar ta fita da sauri.
A waje kusa da ɗakinta da taga ƙusa ta rataya basket ɗin tana wucewa ɗaki da sauri. Zama ta yi ta cire ɗankwalin kanta ta hau goge jikinta, bayan ta gama ta cire doguwar rigar jikinta ta hau sa undies, daga nan ta saka rigar da ta ciro, tana kammalawa ta zauna tare da shafa lotion nata ta feshe jikinta da turaruka. Tana gamawa ta mayar su jaka ta linke kayan da ta cire ta ɗaura saman jakarta.
Kwanciya ta yi tana ɗaukar wayarta, har lokacin babu ƙiran iyayenta. Sai kuma abin ya fara damunta duk da dama yana damunta ganin ba su nemeta ba. Gurin ƙira ta shiga ta laliɓo lambar Abba, gwada ƙira ta yi da mtn nata taga babu services, haka ta gwada da Airtel taga nan ma ya ƙi shiga, dole ta haƙura tana ajiye wayar a saman cikinta. Idanuwanta ta lumshe jin hawaye ya taru. Ta saƙa wannan ta kunce har ƙarfe sha biyu tana kwance.A waje Kulsum bayan ta gama wanke wanke ta kimtsa gidan, don Ya Fanna ba ta nan. Bayan ta gama ta shiga wanka, da ta fito ta wuce ɗaki tasa kaya ta gyara jikinta. Fitowa ta yi zuwa ɗakin Sanaa bayan ta gama.
Da sallama ta shiga mata, jin sallamarta yasa Sanaa buɗe ido tana miƙewa ta amsa. Ciki Kulsum ta ƙaraso ta nemi waje a ƙasa ta zauna tana faɗin.
"Maah ta fita tun safe, amma ina jin ta kusa dawowa."Jingina kai Sanaa ta yi tana cewa.
"Allah dawo da ita lafiya.""Amin Ya Allah."
Kulsum ta amsa da shi. Daga nan suka yi shuru gaba ɗayan su, kusan mintuna ashirin ganin haka Kulsum ta miƙe ta ce.
"Bari in ɗaura abinci."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...