HAMMAD SANAA
Page 12
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookHammad yana cikin daddaɗan baccinsa ya ji ƙara ya dame shi, da ƙyar ya buɗe idanuwansa wanda suke cike da bacci, anan ya ji ƙarar wayarsa ce take ta ruri a gefen pillow da yake kai. Hannu yakai ya jawo wayar yana duba waye yake ƙiransa haka, sunan Sultan ya gani ya bayyana a fuskar wayar.
Ɗauka ya yi yana kafawa a kunne tare da sallama. Yana ji Sultan ya amsa ta ɓangaren shi tare da gaishe da shi. Zaune ya tashi yana sosa saman idanuwansa da suke cike da zara-zaran gashin ido. Bayan ya jinjina jikinsa da gini, sannan ya amsa gaisuwar yana faɗin.
"Ina Ummina? Kun yi waya da su Bashar?""Ummi tana lafiya, sai dai kullum maganarta ɗaya lokacinka yana tafiya. Idan har za ka iya haƙura ka dawo gida kawai Yaya."
Ya ji Sultan ya faɗa ta ɓangarensa.
Murmushin taƙaici Hammad ya yi yana faɗin.
"Ba zan haƙura ba Sultan, ko lokacina ya wuce sai na aiwatar da abin da ya fito dani."Yana ji Sultan ya sauƙe numfashi sannan ya ce.
"Shikenan Yaya, Allah ya mana jagora.""Amin ya Allah."
Hammad ya faɗa ya zare wayar yana kashewa. Ajiyewa ya yi a gefe, yayinda ya lumshe ido ya buɗe a take. Saura mishi watanni kaɗan, wanda cikinsu zai samu cikar burinsa. Yana jin ko bai aiwatar da niyarsa na cikar burinsa da iyayensa ba, to dole ya cika ɗayan na zuciyarsa da ita tafi rinjayarsa, har ya amince da hukuncin iyayensa.
Girgiza kai ya yi ya miƙe tsaye, tabbas dole yau ko gobe ya fara aiwatar da niyarsa.
Wajen akwatinsa ya yi ya buɗe ya ɗauki brush da MacLean ya fita, tamkar yadda yake haka ya yi ya dawo ɗakin. Fitowarsa waje yaga garinma bai gama wayewa ba, bayan dawowarsa ɗakin ya duba wayarsa yaga ƙarfe tara da mintuna.
Bakin katifa ya zauna yana fara saƙa da warwara. Wayarsa ya jawo ya buɗe yana fara danne danne. Yana zaune ya ji ƙwanƙwasa ƙofa. Ajiye wayar ya yi ya miƙe.
Ƙofar ya nufa ya buɗe, Isah ya gani tsaye ɗauke da food flask. Isah shi ya fara gaishe da Hammad.
"Ina kwana?"Sai lokacin Hammad ya farga ya amsa yana faɗin.
"Lafiya lau. Ya ka ke.""Allahamdulillahi. Ga abincin safe."
Faɗin Isa yana miƙa mishi flask din hannunsa.
Karɓa Hammad ya yi yana godiya ya koma ciki, bayan ya rufe kofar. Kasancewar ya yi brush zama ya yi ya buɗe flask, abinci ne mai kyau. Cikin nutsuwa ya ci kaɗan ya rufe sauran.
Baya ya ja don gyara zama, sai kuma ya miƙe da sauri jin dirin mota, fita waje ya yi ya leƙa, anan yaga Alhaji Hussain yana shirin fita. Cikin sauri ya ƙarasa bakin get ya tura ya buɗe mishi.
Isah driver ne yake jan motar, baya Alhaji Hussain zaune ya kishingiɗe. Ganin Hammad ya buɗe get yasa Isah jan motar suka fita a gidan. Rufe get ɗin Hammad ya yi ya koma ɗaki. Kayan sawa ya cire ya ajiye saman katifa, daga haka ya ɗauki sabulu da sosonsa da yake cikin ƙaramin basket ya fita. Toilet ya shiga ya yi wanka, da ya gama ya fito yasa kaya, mai da turare ya shafa sannan ya kimtsa ɗakin sama sama.
Yana kammalawa ya fita a ɗakin, babban ƙofar falon gidan da zai shigar da mutum ciki ya nufa kai tsaye.
Tsayawa ya yi yana ƙare masa kallo, sannu a hankali ya ɗaga hannu ya buga door bell din, sau uku ya buga sannan ya dakata yana jiran a buɗe, sai dai bai san me zai ce musu ba, domin shi kansa bai san ta ina zai fara ba.
Buɗewar ƙofar yasa shi duban wanda ya buɗe, nan suka yi ido biyu da matar aikin gidan. Da kallo matar tabi Hammad, har lokacin ta kasa tuna ina tasan mamallakin fuskar Hammad.
Kan Hammad ƙasa, da ƙyar ya buɗe baki ya ce.
"Ana sallama a waje.""Waye? Ka ce a shigo babu matsala, bari in sanar da Momma."
Ta faɗa tana barin wajen da sauri zuwa ciki.
Hakan ya ba Hammad damar ɗago kansa ya fara bin babban falon gidan da kallo, daga inda yake yana iya hangowa. Kujeru ne set biyu, sai gefe dinning, daga gefensa kitchen ne, ta gefen hagu kuma stairs ne, yana kallon matar aikin gidan ta haura ta wuce, nan ya tabbatar nan ɗakunan baccinsu yake.
Tsaf ya ƙarewa falon kallo, ganin yaja lokaci za ta iya sauƙowa a kowanne lokaci yasa yabar wajen da sauri. Bakin barandar ɗakinsa ya zauna yana sake bin gidan da kallo, a ransa yana tunanin ta ina zai fara yin abin da ya kawosa, har ya samu damar yin komai cikin sauƙi.
Buɗe ƙofar falon yasa ya kai kallon shi wajen, matar aikin gidan ce ta fito, bayanta mace mai kamala da shigar alfarma. Tun zuwansa bai ganta ba, amma kallo ɗaya ya mata ya gane ita ce matar gidan.
Yana ganin sun nufo wajensa ya miƙe da sauri, kai ya sunkuyar ƙasa ganin irin kallon ƙurilla da suke binsa da shi.
Suna ƙarasowa wajen shi, matar aikin ta ce.
"Ina bakin? Momma za ta fita."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...