Page 26

339 41 25
                                    

HAMMAD SANAA

Page 26
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Sanaa haka ta ci gaba da zama bayan kammala Secondary School ɗinta, har tsawon watanni uku kafin result nasu ya fito. Kamar yadda iyayenta suke buri haka ta samu sakamako mai kyau. Tuni Abba ya bazama nema mata makaranta a ƙasar waje don karantar harkar likitanci, kamar yadda abin ya zama yayi, tura yaro ƙasar waje yin karatu.
Sanaa ta yi farin cikin jin haka sosai, kuma da ma ta sani don Momma da Abba sun sha faɗa mata. Addu'arta biyu, na farko Allah yasa ƙasar su Uncle Hakim ne Australia, na biyu kuma Allah yasa Khadeeja ma ta samu su tafi tare. Hakan yasa tana samun labari ta shirya ta tafi gidan su Khadeeja, don sanin ita me ake ciki.
Bayan ta isa gidan suka shige ɗakin Khadeeja. Zaune suke saman gadon Khadeeja, Sanaa sai korowa Khadeeja bayani take, akan Abbanta yana nema mata makaranta a waje, kuma tana addu'ar Allah yasa ƙasar su Uncle ne, ƙarshe tana kallon Khadeeja a sanyaye ta ce.
"Fatan ke ma Abbaa yana nema miki mu tafi tare."

Girgiza kai Khadeeja ta yi, ta ƙirƙira murmushin dole ta ce.
"Bani da tabbas Friendy, na yi wa Abba maganar amma shuru har yanzu. Amma zan sake mishi, don tabbas ina da burin mu yi karatu tare."

Jikin Sanaa sake sanyi ya yi, tasan matsalar Khadeeja shi ne yawan kuɗaɗen da za a kashe idan ya kasance ƙasar da nisa kuma da tsada, duk da ita ma ba ta san nawa ba ne. Hannayen Khadeeja ta kamo ta damƙe, murmushi ta yi tana kallon Khadeeja ta ce.
"Zan yiwa Abbana magana ya haɗamu mu biyun, idan har Abbaanki zai yarda."

"Ban sani ba, sai dai mu jarraba."
Faɗin Khadeeja tana murmushi, don tasan Abbaa zai amince, shi ma yana ta fafutukar nema mata ko wata ƙasa kusa ne ta yi karatunta, ganin zamanin kowa burinsa ya tura ɗanshi ko ƴarshi karatu ƙasar waje.
Har yamma lis suna tare da juna, tare suka fito suka shiga kitchen, kujera Sanaa ta jawo ta zauna, tana kallo Khadeeja ta ɗaura abincin dare, ko tsinke ba ta tayata ba har ta gama ta kwashe suka fita falon gidan.
Anan suka samu Baban Khadeeja ya dawo, har ƙasa Sanaa ta durƙusa ta gaishesa. Cikin fara'a ya amsa mata don ya santa sosai, ko mahaifinta kaɗai ya sani balle ita da tun tana yarinya suke tare da ƴarsa.
Dukkan su suna zaune a falon har da mamar Khadeeja. Khadeeja ce ta zunguri Sanaa da ƙafarta, hakan yasa Sanaa fahimtar me take nufi.
Kanta ta ɗago tana kallon baban Khadeeja ta ce.
"Abbaa don Allah ina neman alfarma."

Hankalinsa ya mayar kanta, yana kallonta ya ce.
"To Allah yasa zan iya miki."

Kanta ta sunkuyar ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Akan karatunmu da Friendy. Abbaa dama na yi wa Abbana magana akan ya haɗamu mu biyu ni da ita, ya nema mana makaranta tare."

Da mamaki Abbaa ya ce.
"Haba Sanaa! Me ya kaiki? Dole ne sai kun yi karatun tare."

Girgiza kai ta yi da sauri, muryarta ta canza tana neman yin kuka.
"Ka yi haƙuri Abbaa, ban san ranka zai ɓaci ba."

Jin muryarta ta canza yasa ya sassauta murya.
"Bana son ɗaurawa mahaifinki wahala Sanaa, naki ma kaɗai zai kashe kuɗi balle ku biyu. Ni ma ina nema mata gurbi ko a Sudan ne taje can."

Jin abin da ya faɗa da sauri Khadeeja tasa baki cikin maganar, ta ce.
"Abbaa ya gama komai fa. Ni dai ka barni naje bana son Sudan."

Shuru Baba ya yi don gaskiya da Alhaji Hussain ya nemi shawarar shi ba zai yarda ba, amma ƙin amincewa babban mutum haka tamkar watsa mishi ƙasa a ido ne, kafin ya ce wani abu ya ji mamar Khadeeja tana faɗa mishi cewa.
"Abbaan Khadeeja dama ce ta samu, ka barta ta je su yi karatu tare, za su fi jin daɗin yin karatun idan suna tare."

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now