HAMMAD SANAA
Page 47
Na Pharty BB"Za ki sanar da ni abin da ya wuce Sanaa idan an saka mana ranar aure."
Faɗin Turaki yana kallon Sanaa da take kallon shi ita ma. Jin abin da ya faɗa yasa ta sunkuyar kanta ƙasa tana sauƙe numfashi ta ce.
"Ina sha Allah, ai mun gama wannan maganar.""Haka ne, tunatar wa ne."
Ya faɗa yana murmurshinsa mai kyau. Murmurshi Sanaa ita ma ta yi ba ta ce komai ba.
Shiru ne ya kauraye wajen na mintina, ganin haka Turaki ya miƙe ɗauke da Nana ya ce."Zan wuce kar lokaci ya ƙure min a hanya."
Sanaa ita ma miƙewa ta yi tana murmushi, tare suka jera suka fita zuwa ƙofar gida da motarsa take fake. Bayan ya buɗe ya shiga ya miƙa mata Nana, ta karɓeta tana faɗin.
"Na gode, sai mun yi waya."Murfin motar ya rufe, ya kalleta yana murmushi ya ce.
"Shike nan, sai mun yi."Matsawa Sanaa ta yi daga haka ya kunna motarsa yana yin riverse ya bar wajen. Sanaa ma gida ta koma, ba ta tsaya falo ba ta wuce ɗakinta ta kwantar da Nana ta sake sauƙa. Abinci ta ɗebe ta koma ɗaki, zama ta yi ta fara ci anan tunanin Hammad ya faɗo ranta ganin ba ta ganshi ba tun fitarta taro Turaki da mishi rakiya. Kafaɗa ta ɗaga alamar ina ruwanta ganin za ta jefa kanta tunanin shi.
...Momma ba ta dawo gida ba sai yamma lis. Bayan ta huta ta rama sallolinta ta fito falo don ɗebe kewa da zaman jiran dawowar Abba. Burinta ya dawo ta sanar mishi abin da yake ranta wanda take jin tsoron faruwar shi. Faruwar hakan tana ji zai bayyana abin da yake binne da suke boyewa, duk da gefe ɗaya tana jin farin cikin faruwar shi.
Numfashi ta furzar tana jinjina kanta saman kujerar da take zaune, a ranta ta ce.
'Tabbas idan hakan zai faru zan fi kowa farin ciki. Amma kafin faruwar shi wannan lokaci dole ta bi umarninmu.'Momma tana zaune tana wannan tunani har Abba ya dawo. Miƙewa ta yi ta tare shi suka wuce sama, bayan ya watsa ruwa ya canza kaya zuwa jallabiya sannan suka sauƙo kasa.
A dining table suka zauna, Momma ta zuba musu abinci. Suna cikin ci Momma ta ka sa danne ranta akan abin da yake damunta, ta ajiye cokalin hannunta ta kalle shi, cikin natsuwa ta ce.
"Abban Sanaa ina son maka wata magana akan Sanaa da muka yi kwanaki da Uncle Hakim.""Me ya faru?"
Faɗin Abba yana dakatawa da cin abinci."Ɗazu mun yi magana da Uncle Hakim akan maganar auren Sanaa da muka yi da shi, mun yi magana da Momynsa nan da sati biyu zasu zo da Uncle da Daddynsu da sauran jama'a ayi maganar auren su. Sai dai ina tsoro, ina tsoron su zo su ga abin da muke ɓoyewa."
Momma ta karasa maganar tana ɓata fuskarta don jimamin abin da zai faru.
Abba hannun momma ya kamo cikin kwantar da hankali ya ce.
"Me ki ka yanke?""Sana'a ƴarmu ce ba zamu gujeta ba duk abin da ta aikata, ko gudunta da muke saboda wannan ƴarce. Don haka ba za a zo a same mu da ita ba, mu kai ta gidan marayu."
"Kina ganin haka shine daidai?"
Abba ya tambayi momma har lokacin yana riƙe da hannunta.
Kai momma ta ɗaga ta ce.
"Eh, zamu faɗa mata zuwan su sannan da hukuncin da muka yanke. Wannan lokaci dole ta bi umurnin mu.""Shike nan, tashi ki ƙirata."
Abba ya faɗa yana sake hannunta.
Mikewa momma ta yi ta nufi sama, ɗakin Sanaa ta nufa tana isa ta tura ta shiga. Sanaa ta hango kwance saman gado ta ɗaura Nana saman cikinta tana shafa bayanta.
Sanaa jin ƙarar buɗe kofa yasa ta juya taga Momma ce, cikin sauri ta mike tana gyara zamanta cike da mamakin ganinta a ɗakinta.
Momma ba ta zauna ba ko karasawa ciki kamar yadda take yi ba, daga inda take tace.
"Ki zo Abbanki yana ƙiranki."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...