HAMMAD SANAA
Page 39
NWAWashegari
Sanaa haka ta gudanar da yini cur a ɗakin cikin hotel da take ciki, ta ƙi fita ko nan da ƙofa ta rufe kanta. Tun safe da ta farka kuka take yi tuna abin da ya faru. Ciwon kai da ya kamata yasa ta bar kukan ta hau sauƙe ajiyar zuciya.
Ta tsani komai da kowa, ba ta da buri da ya wuce ta ji ta jikin Mommanta da Abbanta, ta yi kuka su lallasheta ko za ta ji sauƙi da raɗaɗin zuciyarta. Sai dai duk da hakan da take ji, ta kasa buɗe wayarta balle ta ƙira su ko ta ga ƙiran su.
Ƙarfe sha ɗaya taji yunwa yana neman halakata dole yasa ta miƙe, bathroom ta shiga ta watsa ruwa ta fito, doguwar riga ta zurma ta ɗauki purse ɗinta da ATM ɗinta yake ciki ta fita. A restaurant ɗin cikin hotel ɗin ta tsaya ta ci abinci, ta yi takeaway ta koma ɗakinta. Haka ta wuni a ɗaki ita ɗaya abin duniya duk yabi ya isheta....
A haka kwanaki suka tafi har tsawon kwanaki shida.
A rana ta bakwai Hammad suka dawo. Allah-Allah yake kafin su dawo, don gaba ɗaya yana can amma hankalinsa yana kan Sanaa.
'Wane hali take ciki? Ta warke ta daina jin zafi?'
Su ne tambayoyin da yake yi wa kan sa. Burin sa ya dawo ya fara nuna mata tsantsar kulawa da ƙauna, ya share mata hawaye ya goge mata taɓon zuciyarta, ya haskaka mata duniyarta.Ranar da suka dawo shigar yamma suka yi. Suna sauƙa bai zauna ba, yana watsa ruwa ya canza kaya ya fito a ɗakin su ya nufi ɗakin su Sanaa.
Tsaye ya yi a ƙofar ɗakin, tare da bismilla ya tura handle ɗin kofar yana shiga ciki. Idanuwansa suka fara yawo a falon ta ina zai hangota suka sauƙa akan na Khadeeja wacce take zaune tana bin shi da kallo, jin motsi yasa ta miƙe daga kwancen da take.
Hammad idanuwansa ya ɗauke daga kallonta, a hankali ya taka ya nemi kujera ya zauna. Kafin Khadeeja ta ce komai ya ce.
"Ina take? Tana lafiya?"Wani kululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Khadeeja, duk abin da ya faru tsakanin su amma zai iya zuwa tambayarta, a tunaninta wannan kaɗai zai raba su rabuwa na har abada. Duk da hakan bai sa ta ji ta karaya ba, ta sassauta murya tana kallon shi ta ce.
"Bayan abin da ya faru tsakaninku ta haɗa kayanta tabar nan. Ban san ina ta yi ba, na ƙirata baya shiga may be ko ta karya sim ɗinta don kar a nemeta."Wata bugu zuciyar Hammad ta yi, bai san lokacin da ya ɗago yana kallon Khadeeja ba. Tana dasa aya a maganganunta cikin sauri ya ce.
"What! Ina take tunanin za taje? Ta san kan ƙasar ne, infact ma ta warke ne?"Ni ma ban sani ba, amma ko'ina take za ta dawo tin da babu inda ta sani. To me za ka damu kanka akanta ne?"
Khadeeja ta faɗa tana kallon Hammad ido cikin ido.
Hammad idanuwansa ya ɗauke ana Khadeeja bayan ya mata kallon daƙiƙa, tamkar ba zai ce komai ba can ya sauke numfashi ya ce.
"Kin san abin da ya faru tsakanin mu da ita?"Murmushi Khadeeja ta yi ta ce.
"Ai ko ban sani ba za ta faɗa min, balle na sani."Hammad ɗago kansa ya yi ya kalleta, yaga tana murmushi. Miƙewa ya yi tsaye, yana kallonta ya ce.
"Haka ne saboda naga ta yarda dake. Ke kuma kin ci amanar ta ko?""Ni kuma! Sharri za ka min?"
Khadeeja ta faɗa da sauri tana miƙewa tsaye tare da dafe kirjinta, idanuwanta kamar zasu faɗo take kallon shi.
Hammad bai damu da halin da take ciki ba ya juya ya fita. Yanayin Khadeeja kaɗai ya tabbatar mishi da sa hannunta komai ya faru, kuma dole ya ci gaba da tuhumar ta.Sai dai ta ya? Me ta yi musu? Tsanarta ta yi da zai sakata aikata haka ta ci amanarta ko akasin sa? To me yasa? Me ta mata a rayuwa? Ban da alherin da yake hangowa ita ta yi mata.
Tuna waɗannan ya ji bai san ta ina zai fara tuhumarta ba, dole sai da Sanaa. Da tana nan da ita za ta taimaka mishi su gano me yasa ta musu haka, amma ita ma bai san ina take ba.
ESTÁS LEYENDO
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...