Page 25

312 38 10
                                    

HAMMAD SANAA

Page 25
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Momma ce zaune saman stool a gaban mirror, tana shirye cikin riga da zani na atamfa holland, ƙamshi take zubawa sosai ta yi kyau. Cikin sauri take ɗaura agogon hannunta ganin lokaci ya kusa ƙurewa, aji take da shi a daidai lokacin don koyarwa ɗalibai.
Jin ƙarar wayarta cikin jaka ta yi tsaki, tana jin haushin waye ya ƙirata cikin wannan lokaci da take sauri, ba ta son katse abin da take. Ƙin ɗauka ta yi ta ci gaba da ɗaura agogon hannunta har wayar ta tsinke. Bayan ta gama shirin ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta yafa, handbag ɗinta da yake saman mirror ta ɗauka, flat shoe ta saka ta juyawa ta fita a ɗakin.
Tana taka matakalar benen wayarta ta sake ringing, cikin sauri ta dakata ta buɗe jakarta ta zaro wayar. Lambar Sanaa ta gani ɓaro-ɓaro a fuskar wayar, ta manta yaushe rabon da ta ji muryarta ko su ƙirata, don ita ba ƙiran su take ba.
Kamar ba za ta ɗaga ba don ba ta san me za ta ce mata ba, may be ma maganar ɗaya ce kamar kullum su yi haƙuri, basu nemeta ba, sun daina sonta, to ta ƙira ta sanar mata ta haihu.
Tsaki ta yi ta ɗauka ta kafa a kunne ganin zai yanke, amsa sallamar da Sanaa ta mata ta yi tana faɗin.
"Lafiya? I'm hurry, i have class now."
...

Sanaa numfashi ta sauƙe jiki a sanyaye jin muryar Mommanta haka, tamkar da wata wacce ba ta so take wayar. Jin ta sanar mata tana sauri yasa ita ma cikin sauri ta ce.
"Momma na haihu zan dawo gida? Na gaji da zaman ƙauyen nan. I think warhaka komai ya gushe?"

Tana ji ta ɓangaren Momma cikin tsawa ta ce.
"What? Ki dawo ina? Ai Sanaa babu abin da zai gushe sai lokacin da muka ɗiba miki ya cika, don haka ki zauna. Za mu nemeki da kanmu kwanan nan ki dawo gida."

"Ba zan iya ba Momma, in sha Allah da alheri nake tafe. Ku barni na dawo."
Sanaa ta faɗa cikin muryar kukan da take neman yi, kiri-kiri sun dai gujeta, sun daina sonta.
Jin abin da Momma ta faɗa yasa ta mayar hankalinta tana saurara, inda Momma ta ce.
"I swear to God karki yarda ki dawo Sanaa, idan ba haka ba zan ba ki mamaki. Bayan mun guji cikin kuma ki haifa ki dawo mana da shi to me aka yi? Ba gwara ki zauna ki haifa ba a gabanmu ba. Don haka ki zauna ki ƙara bamu lokaci, soon zamu nemeki My Dearest daughter."

"Please Momma..."
Sanaa ta faɗa cikin kuka wadda tasan Mommanta ba ta so ko kaɗan. Sai dai kafin ta ƙarasa maganar ta ji Momma ta tareta ta ce.
"Last warning da za ki ƙirani ki min wannan maganar. Idan kuma kin ƙi ji ki dawo ki gani, ana ƙoƙarin miki gata kin tsaya shashancin."

Kit ta ji Momma ta kashe wayar. Zare wayar Sanaa ta yi ta fashe da kuka. Wani gatan za su mata kuma bayan wanda suka mata ya cutar da ita.
Kuka take sosai ganin har yanzu sun ka sa haƙura, sun ƙi yarda cewa ƙaddara ce ta sameta, ta saurareta ma ta ƙi, nasu burin yafi nata, su da suka gujeta.
Ɗago kanta ta yi takai hannu ta share hawayenta.
"Na daina zubar da hawayena akan ku, ku ku ka haifeni amma ba ku riƙe ni kamar yadda Allah ya ba ku amana ba, don haka rayuwata zan fara daban kuma a tare da ku. Wani ɗan shaye-shaye yake haifa kuma ya zauna da shi gida ɗaya su rayu, wani karuwa yake haifa, haka duk suke ɗauka a matsayin jarabawar Ubangiji. Amma ni me na yi? Tawa ƙaddarar na faɗa muku ba da son rai ba ne."
Sanaa ta faɗa haka tana miƙewa, tana ganin ta yanke hukuncin da take jin shi ne dai-dai. Komawa gidan za ta yi ta zauna tare dasu, ko da za su gasata da abin da ta haifa haka za ta jure ta zauna, zuwa lokacin da Turaki zai yi magana da manyansa ya turo gidansu. Ta san da zaran ya zo za su sassauta mata komai, kuma za su so ta yi auren.

Wajen akwatinta ta nufa ta kwantar, kayanta wankakku da na Nanah ta jera a babban akwatin, ƙaramin kuma ta zuba masu datti ciki ta rufe, babu abin da ta bari nasu sai kayan da zasu sa gobe. Ji take ba za ta iya ƙara kwanaki ba ta tafi ba, ko wanki ba za ta tsaya yi ba, gani take zai ɓata mata lokaci don burinta kawai ta ganta gabansu tare da Nanah taga me za su yi. Haushin kanta ma ta ji da ta zaɓi hukuncin yin nesa da su, ji ta yi da ta ƙi tafiya, ta kafe ta zauna tare dasu har ta haihu.
Saman katifarta ta koma ta zauna tana ɗaukar Nanah jin tana ƙananan kuka, gyarata ta yi ta fara ba ta abincinta. Cikin sauri yarinyar ta karɓa tana sha.
Ido Sanaa ta tsura mata, tausayinta ne ya lulluɓeta tuna duk abin da ake akanta ba ta san komai ba, ba ta ma san me duniyar ba balle abubuwan cikinta, amma tun kafin ta zama mutum aka tsaneta. Sonta da ƙaunarta ya ƙara kamata cike da tausayinta.
Hannunta ta ɗaura saman yalwataccen gashin kanta da yake cike ta shafa a hankali, ido cike da hawaye ta ce.
"Ina sonki ƴata, ko duniya za su juya miki baya ba zan taɓa gudunki ba. Ban taɓa tunanin samunki ba Allah ya bani ke, duk da ban shirya hakan ba. Yanzu muka soma yaƙin Nanah, ki cigaba da jure komai watarana za mu yi nasara."

HAMMAD SANAAOnde histórias criam vida. Descubra agora