HAMMAD SANAA
Page 36
NWAHammad ɗago kansa ya yi ya kalli Sanaa da ya ji ta yi shuru, ido suka haɗa ta sunkuyar kanta da sauri kan littafin. Murmushi ne ya suɓuce mishi bai shirya ba, ya lura tana tsoron shi dole tasa take zaune.
Hannunsa yakai ya dungure mata kai, Sanaa ta kalle shi da sauri tana jan baya. Gira ya ɗaga mata ya ce.
"Kina tsorona ko? Ina takura miki?"Kanta ta sunkuyar ƙasa, idan ta ce a'a ta yi ƙarya, gwara ta faɗa mishi gaskiya su rabu lafiya, ya daina bibiyarta ba ta so, tana jin wannan hukuncin da ta yanke shi ne daidai.
Rayuwarta ce ba ta Khadeeja ba ko na wani, don ko su Momma basa zaɓa mata abin da suke so sai da ra'ayinta, tana bin ra'ayin Khadeeja a matsayinta na ƙawarta ƙwaya ɗaya da ta yarda da ita ta bata amana, duk da taga ta fara canza mata. Don haka gwara ta sanar da shi gaskiya ya daina bibiyarta ba ta so, karatu ne tana da nata kuma Allah shi zai taimaka mata ba shi ba. Sai ya gama mata zai tafi za ta sanar da shi akan kar ya ƙara zuwa ko binta duk idan take.
Hammad murmushi ya yi yana ci gaba da kallonta, yana ji ta yi shuru, hakan yasa ya bawa kanshi amsa akanta, amsar da bai shirya yanzu ba ko tunani yanzu ba, amma ganinta ya canza mishi komai, duk da yanzu ba shi da niyar faɗa mata amsar sai nan gaba, sai ya gama yin abin da ya kawo shi ƙasar idan zai tafi. Dole tasan matsayinta a zuciyarsa na wacce ta hana shi sukuni a rayuwarsa, tun ranar da ya fara haɗuwa da ita.
Kansa ya mayar ya ci gaba da rubutu a hankali yana mata bayani, yasan ta saka kunne tana saurara ko ba za ta yi magana ba, dama ta ƙara fahimta yake so don yaga tana da ƙoƙari sosai.
Dukkan su babu wanda ya lura da rashin Khaleed ko Amir balle Khadeeja a falon, yana mata bayani ta baza kunnuwanta tana saurara.Tsawon mintuna ashirin Khadeeja ta shigo falon, hannunta ɗauke da leda. Sanaa da sauri ta kalleta, cike da mamaki ta ce.
"Kin fita ne."Kai Khadeeja ta ɗaga, ta ƙarasa ta buɗe fridge ta saka musu takeaway da ta musu ita da Sanaa bayan fitarta. Sanaa ganin haka ta mayar kanta kan littafanta tana sauraran bayanin da yake mata, wanda tasan shi ne na ƙarshe don ba za ta ƙara bari su haɗu ba.
Khadeeja tana ajiyewa ta ce.
"Ko za ku bukaci abin sha."Daga haka tabar wajen, fita ta yi a falon cike da murna da taƙaicin ganin Hammad ya yi wa Sanaa assignment, haka take so Sanaa ta sake mishi fuska su samu rabon su.
Sun ɗauki mintuna Hammad ya dakata da bayanin da yake mata, kallon Sanaa ya yi da ta ga ya dakata ta ɗago. Murmushi ya mata ya ce.
"Gimbiya kina fahimta?"Wani banbaraƙwai Sanaa ta ji ta kasa ba shi amsa, sai kuma ta miƙe ta nufi fridge don kawo mishi ruwa.. Da kallo Hammad ya bi bayanta dashi kafin ya ɗauke kansa da sauri ganin ƙanƙantar rigar jikinta duk da iya guiwarta ne.
Sanaa fridge ta buɗe, ta ɗauki orange juice guda biyu da taga Khadeeja ta musu takeaway, ta dawo ta ajiye a Center table sannan ta zauna.
Hammad hannu yakai ya ɗauki ɗaya ya buɗe ya fara yasha, kamar tasan yana neman abin sha, sai dai kurɓa biyu ya yi ya ajiye jin ɗanɗanon wani iri, haka Sanaa ma a hankali tasa hannu ta ɗauki ɗaya ta fara sha, ci gaba ta yi da sha don ƙishi take ji.
A haka Hammad ya ci gaba da mata bayani inda ya fara dakatawa yana furzar da numfashi.
Sau uku yana dakatawa yana furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa, na huɗu ka sa jurewa ya yi ya ajiye pen ɗin ya yi baya yana jinginar da kanshi saman kujera ya lumshe idanuwansa da suka fara juyawa. Wani mugun sha'awa ce take taso mishi lokaci ɗaya, bai taɓa jin kwatankwacin hakan ba tun da yake, don yana ƙoƙarin kare kansa daga jin haka a matsayinsa na wanda yasan babu inda zai sauƙe. Gashin jikinsa suka fara miƙewa fiye da wanda idan ya ji ƙamshin Sanaa suke yi, balle yanzu ga yanayin da yake ciki ga ƙamshinta tana kusa da shi yana shigar sa sai abin ya haɗe mishi biyu, jikinsa yana ji ya fara tsuma yana tsananin buƙatar mace da zai sauƙe abin da yake ji ya cika mishi mara.
Da sauri ya buɗe idanuwansa da suka yi jaa jin nishin Sanaa da ƙarfi mai cike da wahala, ganin ta ya yi ta sulale ƙasa tana dafe da cikinta. Idanu ya zuba mata ya ka sa taimaka mata domin yasan yana taɓata ba zai tsaya a iya taimako ba, amma kallon da yake mata ƙara tunzura zuciyarsa take zuwa kanta don shigar jikinta ba wani kakkauran rigar kirki ba ce, dole ya runtse idanuwansa da ƙarfi.
Sanaa wacce take durƙushe tsananin azaba da ciwon mara ya cinyeta tuni ta fara hawaye, ita tun da take period bai taɓa mata ciwo haka ba. Wani ruwa-ruwa take ji a ƙasanta har da motsi-motsi take ji, hakan yasa ta fara matse cinyoyinta, tana jin kanta a wani irin yanayi, gashin jikinta duk sun tashi, jikinta yana rawa.
Ba ta san lokacin da ta cafko ƙafar Hammad ba, cikin kuka ta ce.
"Ka taimaka min, marata ciwo."
CZYTASZ
HAMMAD SANAA
RomansCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...