HAMMAD SANAA
Page 55 (End)
Na Pharty BBBayan komar su gida sannan jama'a suka san da haihuwar, duk tunanin su Hammad yana wajen aiki Sanaa kuma tana ciki ba ta fito ba. Tuni gidan ya kaure da murna ana shiga ana ganin babies da aka musu wanka cikin kaya iri ɗaya, yanayin su da komai irin na Sanaa hatta dogon hancin su da bakin su.
Gimbiya da kanta ta taso ta zo ganin su haka tsohon mai martaba da sarki Sultan tare da mukarraban sa, hatta baba Qadeer da gimbiya Zaituna. Khaleed ka sa zuwa ya yi don yasan ba zasu karɓe shi ba, amma Bushra tun da ta samu labari tana can, tsakanin su har yanzu babu jituwa balle wani abun, ya kasa fadawa kowa haka suke rayuwa duk tsawon lokaci.
Sanaa ita da kanta ta ƙira Momma da Abba ta faɗa musu, ta ƙira Maah ta faɗa mata. Da yamma Momma da Abba suka zo suka ga babies tare da dangin Abba da suka samu labarin auren Sanaa suka yi ta mamaki. Momma da Abba suka rufawa ƴarsu da kansu asiri suka ce auren da tarewarta duk lokaci ɗaya ne, gidan sarauta ne basa son taro, jin haka yasa suka ja bakinsu suka yi shuru suka mata murna. Sanaa ta yi murnar ganin dangin Abbanta, har da yaran su yan mata da kanana duk suka zo.Haka kwanakin ya wuce Sanaa tana samun kulawa daga dangin mijinta, gimbiya musamman tasa a kawo mata bayi biyu babbar mace da bazawara ga Sameera, don suna taimaka mata dasu wankan babies.
Mutanen gidan kullum suna tare da ita har dare, a haka ranar suna ya zagayo yara suka ci sunan gimbiya da Momma, Rabiatu da Aisha. Hammad ya haɗa gagarumin walima a masarauta, aka ci aka sha aka watse lafiya.
Sanaa ta samu alheri ranar, taga mutanen da abin su bai dame su ba domin kowa burin sa ya kyautata mata da yaranta. Hammad ya haɗa musu kaya akwatuna biyu, haka ɓangaren gimbiya ma da Momma kowa ya yi rawar gani, musamman da suka ji sunan nasu ne. Momy da Ilham basu samu zuwa ba.
...Bayan watanni uku.
Abubuwa da dama sun faru, Sanaa ta gama wankan jego cikin koshin lafiya. A ranar da ta kammala Hammad ya sallami bayin, don shi sam baya son bawa ko baiwa a ɓangaren shi, idan ba mai yi wa Sanaa shara da wanke wanke ba wanda ya zama dole ne.
Da daren ya shigo ya samu Sanaa ta kwanta ta kwantar da Hassana da Hussaina, gefen su Nana sun yi bacci ta lulluɓe su. Zama ya yi gefen da take yana binsu da kallo kafin ya tsayar kallon sa kan Sanaa da take kallon shi.
Murmushi ya mata ya ce.
"Wannan duk nawa ne?""A'a, na aro ne."
Ta faɗa tana matsawa ya kwanta, ta gyara ta kwantar kanta saman kirjinsa ta ƙara da faɗin.
"Ya maganarmu? Lokacin fa ya yi.""Mu yi bacci."
Faɗin Hammad ya kai hannuna ya kashi bedside lamp, ya fara karanta addu'a.
Shuru Sanaa ta yi tana jinsa, tun da bikin uncle ya kusa take tunatar mishi ya ƙi maganar har aure saura kwana goma amma shuru. Haka bacci ya ɗauketa tana tunanin me za ta yi ya barta taje.Da safiyar ƙarfe tara ya wuce aiki, ita ma Sameera ta zo ta taimaka mata da gyaran gida kamar kullum ita ta ji da wankan yara da nata.
Tana kammalawa ta kwashe su suka nufi ɓangaren gimbiya da taimakon baiwa Sameera. A can ta samu Bushra zaune, ta yi mamakin ganinta kamar kullum amma haka ta kawar komai ta zauna bayan ta gaishe da gimbiya.
Ƙarfe uku ta miƙe ta ɗauki Hassana ta kalli Bushra ta ce.
"Taimaka min da Hussaina zuwa ɓangarena.""Nanar fa?"
Ta faɗa tana miƙewa ta tashi ta ɗauki Hussaina."Mu je sai ki dawo ɗaukarta."
Sanaa ta faɗa tana yin gaba, Bushra tabi bayanta har zuwa ɓangaren Sanaa.
Zama ta yi a saman kujera gefen Sanaa tana ajiye Hussaina. Sanaa ta fara shayar da Hassana ta kalli Bushra da take kokarin tashi dauko Nana ta dakatar da ita.
"Zauna Bushra don Allah."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...