Page 44

518 49 68
                                    

HAMMAD SANAA
Page 44
Pharty BB

Hammad yana fita a gida babu inda ya nufa sai airport, cikin minti ashirin ya gama komai ya shiga cikin jirgi, minti biyar da shiga jirgi ya sanar ya ɗaga zuwa ƙasar San Francisco Birnin California. Gabanin asuba suka isa, yana fitowa taxi ya tara ya nufi hotel.
Bayan shigar shi hotel ɗin ɗaki ya nema suka ba shi ya wuce cikin ɗakin ya ajiye karamar akwatinsa, bathroom ya wuce ya watsa ruwa sannan ya ɗauro alwala, fitowa ya yi ya tada sallah ya hau rama sallolin da ake bin shi. Bayan ya idar ya miƙe ya haye gado ya kwanta don bacci da yake ji.
Bai jima ba bacci ya ɗauke shi, bai farka ba sai sha ɗaya. Ya miƙe ya wuce bathroom ya wanke bakinsa ya yi wanka ya fito, akwatinsa ya ɗauka ya buɗe ya ɗauki kaya ƙanana yasa, ya fesa turare ya shafa lotion. Bayan ya gama ya rufe akwatin, ya ɗauki wayarsa da atm ɗinsa yasa a aljihunsa sannan ya fita ɗakin.
A reception ya tsaya ya yi breakfast, da ya gama ya miƙe ya biya ya fita a wajen da hotel ɗin gaba ɗaya. Taxi ya tara ya faɗa mishi sunan makarantar su sannan ya shiga. Sun ɗan yi tafiya suka iso, ya biya shi ya sauka ya fita.

Da bismilla ya saka ƙafarsa cikin makaranta yana addu'ar Allah ya haɗa shi da ita, idan kuma bai sameta zai bi hukuncin da zuciyarsa ta yanke mishi.
Hammad idanuwansa ya dinga yawo cikin makarantar ko zai ga Sanaa amma babu ko mai kamarta, ɓangaren classes nasu ya nufa nan ma shuru har cikin class din ya shiga, ya fito ya nufi cafeteria nan ma ba ta nan. Ganin haka ya nufi part ɗinsu domin aiwartar da abin ya yanke.
Elevator yabi ya shigar da shi zuwa floor ɗinsu, bayan ya tsaya ya fito.
Kai tsaye ɗakin su Sanaa ya nufa, yasa hannu ya murɗa handle din ya ji a buɗe, hakan yasa ya tura shiga.
Da Khadeeja ya fara cin karo ta fito a ɗaki cikin shiri, daga alama fita za ta yi zuwa class. Dumfararta ya yi babu tunanin komai.
Khadeeja a mutuƙar tsorace ta fara ja baya, ta tsorata da ganin sa bayan tasan yabar ƙasar shi da Khaleed har da Amir.
Hammad ganin Khadeeja tana jan baya cikin azama ya ƙara taku biyu ya damƙota. Ihu za ta fasa yasa hannunsa ya toshe mata baki tare da janta zuwa cikin bedroom, saman gado ya wurgata ya juya ya kulle ƙofar da mukulli, ya zare ya jefa a aljihunsa.
Juyowa ya yi yaga ta miƙe tana danna wayarta cikin sauri daga alama ƙira za ta yi, hannu yasa ya fizge wayar ya kashe, ya saka a aljihunsa yana mata wani mugun kallo.
Khadeeja duk tsiyarta ta tsorata da ganin yanayin shi, jikinta rawa ya fara yayinda zuciyarta take bugawa tare da tambayar kanta me zai mata. Cikin rawar murya ta samu bakin furta.
"Me haka? Me za ka min? Ka buɗe min ƙofa na fita ko na maka ihu."

Hammad zama ya yi a saman gadon Sanaa, wani mugun kallo har lokacin yake aikawa Khadeeja. Cikin tsawa ya ce.
"Zauna!"

"Na maka me?"
Khadeeja ta faɗa cike da tsoro, fatanta ɗaya kar dai ya gano gaskiya ya ce zai mata hukunci ta hanyar amfani da ita.
Wani mugun harara Hammad ya daka mata, cikin ƙyama ya ce.
"Me ki ke tsammani? Zan miki abin da ki ka sani na mata. God forbid na ratsa wacce zan yi amfani da ita sai ke ƙazama. Go down!"

Tsawar da ya mata yasa ta durƙushe ƙasa ba ta sani ba, jikinta ya ci gaba da yin rawa.
Hammad zaman sa ya gyara, ya ɗaga yatsunsa biyu yana kallo ya ce.
"Tambaya biyu zan miki, ina neman amsar dukkan su. Rashin ba da amsar ɗaya daga ciki zai sa na miki duk abin da ya zo raina. Ina take? Sannan da sa hannunki komai ya faru tsakaninmu."

Shuru Khadeeja ta yi tana girgiza kanta, ba za ta iya faɗa mishi ba domin cikin sirri suka gudanar komai, sannan ta musu alƙawari ba za ta faɗawa kowa ba bayan Sanaa.
Hammad ganin haka ya matsa kusa da ita, za taja baya yasa hannu ya fizgo gashinta da yake cikin gyale ta yi rolling. Murɗa gashin ya yi cikin tsananin fushi ya ce.
"Ki bani amsa."

Khadeeja hawayen azaba ta fara tana girgiza kanta ta kasa magana. Hammad a zafafe yasa ɗayan hannunsa ya buge bakinta da yasa ta fasa ihun azaba ta ce.
"Zan faɗa maka."

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now