Page 18

194 27 6
                                    

Assalamu alaikum mata masu sana'a.
Masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin sauƙi, to ƙofa buɗe take. Mai buƙata ya tuntuɓi lambar nan 07037487278
...

HAMMAD SANAA
Page 18
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Turaki kansa ya ɗaga yana kallon resher bishiyar da yake kaɗawa, ya cika sosai don damina da ya shigo. Tamkar ba zai furta komai ba, duk ƙoƙarin shi ya danne amma ya kasa, bai san ta ina zai fara ba, domin shi ba mazauni ba ne balle yasan gidan su. Ganin ba zai iya jurewa ba ya sauke kanshi ƙasa yana ɗaura idanuwansa kan na Sani.

"Sani ko kasan gidansu yarinyar nan?"
Turaki ya tambaye shi.
Sani da ya ji tambayar ya gyara zama ya ce.
"Wacce a ciki?"

Don yasan idan ba baƙuwarsu ba to Kulsum, dama kwana biyun ya lura da yanayin Turaki sam babu walwala, ya tambaye shi yana gudun fushinsa.
Numfashi Turaki ya sauke ya ce.
"Ɗaya farar mai zuwa ɗebo ruwa, mai zane a fuska."
A tunaninsa samun gidan su Kulsum shi zai sa ya samu Sanaa cikin sauƙi, don ta sanar mishi ƴar uwarta ce.
Sani da ya fahimci Turaki kwatancen Kulsum yake ya ce.
"Na sani sosai, ƴar Malam Umaru ce. Tana zuwa tsangayarmu karatu."

"Allahamdulillahi. Za ka min jagora?"
Turaki ya ce da sauri jin abin da yake gani da wahala ya zo mishi cikin sauƙi.
Kai Sani ya ɗaga ya ce.
"Ko yanzu ka shirya."

Miƙewa Turaki ya yi tsaye yana faɗin.
"Tashi muje, ai babu maganar ɓata lokaci."

Murmushi Sani ya yi ya miƙe shi ma, dardumar da suka tashi a kai ya linke, suka saka takalman su suka bar gurin. Gida suka nufa, Sani ya ajiye dardumar suka daura alwala ganin magriba ta yi. Masallaci suka nufa suka bi jam'i, bayan an idar da sallar suka fito suka nufi gidan su Kulsum.
Sani shi yake musu jagora, yayinda Turaki zuciyarsa ta kasa nutsuwa, ya kasa tabbatar da me yake ji akan Sanaa, son sanin wacece ita da ƙaddarar da ta kawota ƙauyen shi yafi komai rinjayar zuciyarsa, sai kwana biyu da bai ganta ba yaji ta samu gurbi a zuciyarsa. Sai dai shi kansa bai tabbatar menene ba balle ya faɗa mata.
Ba su yi wata tafiya mai nisa ba suka iso ƙofar gidan su Kulsum. Cak suka tsaya an rasa wa zai fara sallama. Ganin haka Sani ya matsa kusa da ƙofar sosai, cikin ɗaga murya ya doka sallama yadda za su ji.

Maah tana kwashe abincin jellof na sphagetti da ta dafa, Kulsum tana sallah a ɗaki, yayinda Sanaa ta idar ta fito waje. Jin sallamar yasa ta amsa tana nufar ƙofa ta cewa Maah.
"Bari in duba."

Waje ta nufa tana amsa sallamar, maƙalewa sauran sallamar ya yi ganin Turaki da Sani wanda wutar lantarki wajen ya ba ta damar ganinsu. Cike da mamaki ta ƙarasa wajen su, fuska ta tsuke tana cewa.
"Lafiya?"

Murmushi Turaki ya yi da ganinta, addu'arsa ta karɓu da ya fara arba da ita. Kusa da ita ya matsa ya ce.
"Lafiyar ce ta kawo haka baƙuwarmu. Ina ki ka shiga kwana biyu? Are you fine?"

Ƙara ɓata fuska ta yi tana jan baya.
"I said to you to stay away from me. What do you want?"

"I want to be with you."
Turaki ya samu kansa da faɗin haka murya can ciki. Ba zai yi ƙarya ba tabbas yana son kasancewa da ita, a kanta ya fara jin abin da yake ji tun farin ganinta, wanda bai gama sanin menene ba.
Shuru Sanaa ta yi ta ɗauke kanta ranta yana ci gaba da ɓaci, murya a ciki ta ce.
"I'm not your type."
Tana faɗin haka ta juya ta shige ciki da sauri.

Da kallon mamaki Turaki ya bita, maganarta ya sa shi cikin tunani da neman fassara su, ga kuma canjin yanayi da ya ji daga muryarta. Nan ya sake tabbatarwa cewa akwai abin da yake tattare da ita.
Maganar Sani ya dawo da shi hankalinsa ya kalleshi da sauri.

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now