Page 29

277 28 8
                                    

HAMMAD SANAA

Page 29
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Ranar Litinin ƙarfe sha ɗaya na safiya. Sanaa ce zauna saman ɗaya daga kujerun falon gidansu, fuskarta ta yi ja sosai don kuka da ta yi da safe, gaba ɗaya ji take kamar a ce ta fasa tafiyar, ba ta son yin nesa da iyayenta don abin da ba ta taɓa ba kenan, tafiya wani guri ta barsu tun tasowarta, shi yasa ko hutu gidan dangi ba ta zuwa, idan za ta je gaishe dasu to da Mommanta take zuwa.
Kuka ta yi sosai a ɗakinta da safiyar tun da ta ga lokaci ya kusa, Momma ce da ta shigo mata magana ta ganta haka ta hau lallashinta, haka Abba ma ya shigo ya lallasheta, sai ya ji jikinsa ya yi sanyi his only daughter za ta yi nesa dashi, amma hakan shi ne gatanta. Bayan ta yi shuru suka fita suka barta ta shirya.
Sai ƙarfe goma ta fito ta yi breakfast da ƙyar ta koma ɗakinta, haka ta lallaɓa ta shiga wanka, ta fito ta saka riga abaya dogo, babu abin da ta shafa sai lotion, ta taje gashinta ta kama da ribbon, ta ɗauki mayafin rigar ta yafa a kanta, takalmi sawu ciki tasa ta ɗauki wayarta ta jefa a jaka ta sauƙo ƙasa.
A falo ta zauna tana jiran zuwan Khadeeja don su wuce airport. Momma da Abba ƙin sauƙowa ƙasa suka yi kusa da ita, duk gudun su sake sa ta wani kukan, suka barta zaune ita ɗaya a falon.
Ƙarfe goma da rabi Khadeeja ta yi sallama ta shigo, ita ma ranta a haɗe daga alama tafiyar ce ba ta so. Tare da Abbanta suka zo don shi ya kawota da kanshi. Sanaa ce ta amsa murya a sanyaye, ta gaishe da Abban Khadeeja tana cewa.
"Bismilla Abba, bari in ƙira Abba da Momma."

Saman kujeran suka zauna, Sanaa ta wuce upstairs ta ƙira Momma da Abba, tare suka sauƙo zuwa falon. Abba da Momma suka zauna saman kujera, Sanaa ta zauna kusa da Khadeeja suka yi jigum.
Bayan su Abba sun gaisa suka miƙe don tafiya, haka Sanaa da Khadeeja suka bi bayan su riƙe da jakakkunan su ƙanana na goyo, ciki passport ɗinsu da ATM nasu ne. Tun daren jiya Momma ta yi wa Sanaa transfer kuɗin da Abba ya tura mata, tasan zai isheta har ta dawo.
A harabar ajiye motoci, Sanaa da Mommanta da Abbanta mota ɗaya suka shiga, Khadeeja da Abbanta motarsa suka shiga. Daga haka mai gadi ya buɗe musu get suka fita.
Airport suka nufa kai tsaye, bayan sun isa suka sassauƙo suka nufi ciki. Momma a waje suka dakata, Sanaa tana ganin haka ta ƙarasa kusa da Momma ta faɗa jikinta tana kuka.
Rumgumeta Momma ta yi tana shafa kanta.
"Is ok my daughter, ga waya za muna yi. Fatan dai ki dage ki yi karatu kin ji?"

Kai Sanaa ta ɗaga tana cewa.
"In sha Allah Momma, zan yi kewarki sosai."

"Ni ma haka."
Momma ta faɗa tana ɗago Sanaa a jikinta.
Abba ya matso ya kama hannunta suka nufi ciki. Khadeeja da ta yi sallama da Abbanta tabi bayan su. Abba shi ya shiga ciki tare da Sanaa da Khadeeja, anan ya haɗa su da wanda gwamnati ta ɗauka don yiwa ɗalibai jagora zuwa ƙasar. Daga nan Abba ya yi wa su Sanaa sallama ya fita zuwa wajen Momma. Sanaa tana kallo Abbanta ya fita ya barta, hawayen idanuwanta suka zubo, hannunta takai ta share a hankali ganin kowa babu hawaye a fuskarsa.
Screening aka hau yi musu, bayan an gama suka wuce cikin jirgi, duk ɗalibai ne yawanci a economy class ɗin. Sit ɗin Sanaa da Khadeeja a tare, Sanaa kusa da window take, idanuwanta a jikin window ta yi shuru. Khadeeja tuni ta ciro wayarta ta fara ɗauke-ɗauken hotuna cike da murna yau ga ta a jirgi zuwa America.
Tsawon mintuna talatin aka sanar jirgi zai tashi kowa ya ɗaura belt, bai fi minti biyu ba suka ji jirgi ya fara tashi. Da sauri Khadeeja ta damƙo hannun Sanaa don ba ta taɓa hawa jirgi ba, Sanaa kuwa ta saba hakan yasa ba ta ji ko ɗar ba.
Bayan jirgi ya tashi Khadeeja ta sake hannun Sanaa, ajiyar zuciya ta sauƙe ta ce.
"Wai na tsorata."

Murmushi kawai Sanaa ta yi don Khadeeja ta ba ta dariya. A haka suka ci gaba da tafiya na tsawon lokaci, tun suna sa ran isowa har bacci ya ɗauke su don dare ya shiga sosai. Tafiyar 18hrs 57mins suka yi a hanya kafin su isa ƙasar San Francisco California, a San Francisco international airport jirgin ya sauka, sai lokacin su Sanaa suka farka cike da gajiya, lokacin ƙarfe shida na safiya. Sauƙowa suka yi aka fito musu da akwatin su, kowa yaja nashi zuwa babbar motar da ta zo ɗaukar su daga makaranta aka turo.
Bayan sun saka akwatinan su suka shiga motar, daga haka aka ja motar suka bar airport ɗin. Birni iya birni suka gani a ƙasar, tun daga Airport ɗinsu abin kallo ne, balle da suka shiga cikin garin kaɗan idanuwansu su faɗo ƙasa tsabar kallon manyan manyan gidaje da yafi na Abuja.
Har cikin makarantar aka kaisu, nan ma kanshi abin kallo ne yadda ya haɗu, ga department na koyan karatun harkar likitanci daban-daban. A bakin babban part ɗin wajen aka tsayar da motar, sauƙowa suka yi suka bi bayan wanda yake musu jagora har office ɗin manya malamai wanda suke kula da ɗalibai na makarantar. Guri aka basu suka zauna, anan ya gabatar da ɗalibai wajensu. Godiya suka mishi, suka haɗa su da wanda zai kaisu hostel yabasu ɗaki, sannan suka sanarwa ɗalibai gobe zasu fara fitowa karatu, don kowa ya riga yasan me zai karanta da kuma courses ɗin da zai ɗauka don an tura musu tun da suka yi registration.
Daga haka suka miƙe suka bi bayan wanda aka haɗa su dashi, motar suka koma har da shi. Tafiyar da bai fi minti biyar ba driver ya yi ya tsaya a babban gini upstairs da yake ɗauke da ɗakuna masu kyau tamkar hotel. Gaba ɗaya suka sauƙo, aka fito musu da akwatin su suka ja suka bi bayan wanda makaranta ta haɗa su dashi. Stairs suke bi kasancewar elevator zai basu wahala kuma zai musu kaɗan.
A first floor yabawa ɗalibai shida ɗakuna uku kowanne ɗaki ɗaya mutum biyu. Second Floor suka wuce nanma yabawa ɗalibai shida ɗakuna uku, haka a third floor ya haɗa dalibai shida ɗaki uku. Sanaa da Khadeeja su biyu suka rage, saura goma sha takwas duk sun samu ɗakuna sun raba kansu, hakan yasa ya wuce dasu Sanaa Fourth floor. Ɗaki ɗaya yabasu suka ja akwatinan su suka wuce ciki, shi kuma ya koma.
Cikin ɗakin falo ƙarami ne mai ɗauke da kujeru three siter da one siter guda biyu, sai desk na rubutu a gefe guda biyu da lamp, sai ƙaramin fridge, a share tas, gefe ƙofa ɗaya da alama bedroom ne. Nan suka nufa suka buɗe, ai kuwa bedroom ne da gado guda biyu ƙanana da katifa da pillow, an ɗaura bedsheet da duvet guda ɗaya a kowanne gado, ga wardrobe mai ƙofa biyu, ga Ac, sai ƙofar bathroom, a gyare babu datti ko kaɗan ɗakin.
Akwatinsu suka ja suka ƙarasa ciki, a kusa da wardrobe suka ajiye akwatinsu. Sanaa da sauri ta wuce bathroom, a wanke a share tas yake. Fitsari ta yi ta ɗaura alwala ta fito, haka Khadeeja ma ta wuce ta ɗaura alwala ta fito, ta samu Sanaa tana rama sallolinta, ita ma hijabi ta ciro a akwatinta ta hau yi.
Bayan Sanaa ta idar da sallar ta miƙe ta cire hijabinta, saman ɗaya daga cikin gadon ta haye ta kwanta don akwai bedsheet akai, kuma a gyare tsaf babu ƙazanta ko datti, daga makarantar kaɗai ka gani za ka san babu harkar ƙazanta don gyara da kula da yake dashi.
Haka Khadeeja da ta idar ta haye gadon ita ma sai bacci. Sun jima suna bacci har ƙarfe uku, yunwa ce ta tayar da Sanaa don rabonsu da abinci tun a jirgi da aka raba musu. Sanaa tashin Khadeeja ta yi da take ta bacci.
Tashi Khadeeja ta yi tana murza ido.
"Menene kuma?"

"Yunwa nake ji. Ke ba kya ji?"
Sanaa ta faɗa tana tashi ta sauƙa a saman gadonta.
Khadeeja miƙewa ta yi ta sauka a gadonta, wajen Sanaa ta ƙarasa inda ta nufi wajen wardrobe ta buɗe.
Sanaa akwantinta ta kwantar ta fara ɗaukar kayanta tana jerawa a cikin wardrobe ta cewa Khadeeja.
"Mu gyara kayanmu sai mu fita nemo abinci."

"To hakan ya yi."
Khadeeja ta faɗa tana kwantar akwatinta, ta ɗauki kayanta ta fara jerawa a gefe ɗaya. Suna yi ta cewa Sanaa.
"Friendy kin ga kyan makarantar da ƙasar ma."

"Sosai ma Friendy, dubi ɗakin nan tamkar a gida, komai akwai ga tsafta."
Sanaa ta faɗa tana rufe akwatinta babba ta ɗaga ta ɗaura sama wardrobe ɗin kasancewar ba shi da tsayi. Ƙaramin ta buɗe ta cire undies ɗinta na ciki ta zuba a wardrobe, haka ta jera turarukanta da lotion, takalmanta ta jera a ƙasa.
Haka Khadeeja ta jera kayanta da cikin akwati ɗaya ne sai ƙaramin jaka, bayan ta fama ita ma ta ɗaura akwatin saman wardrobe.
Jakarsu suka ɗauka suka yafa mayafansu suka fita a ɗakin.
Sanaa kallon filin wajen ta yi ta ga ɗakuna guda shida kowanne ɗaya yana facing ɗaya, haka ɗakinsu yana facing wani ɗaki, ga elevator ga stairs, ɗaiɗaikun ɗalibai suna yawo da yawanci turawa ne sai baƙin fata da ta gani ƙwaya ɗaya.
Kallon Khadeeja ta yi da take kalle-kalle ita ma.
"Mu shiga elevator Friendy."

"Kin iya amfani da shi?"
Khadeeja ta tambayi Sanaa.
Kai Sanaa ta ɗaga ta ce.
"Haba ke kuwa, mu je."

Elevator suka nufa suka shiga ya rufe ƙofa, Sanaa ce ta yi amfani da shi ya saukar da su ƙasa ya buɗe ƙofar. Fitowa suka yi suka nufi hanyar waje ta inda suka shigo. A bakin ƙofar suka tsaya suna bin harabar makarantar da kallo, ɗalibai sai yawo suke, kowa yana harkar gabansa.
Khadeeja ce ta fara tafiya ta ce.
"Friendy mu yi gaba ko zamu samu cafeteria ko restaurant."

Cikin sauri Sanaa tabi bayanta suka jera, tafiya kawai suka fara inda ƙafar su taja su suke takawa, a haka suka hango katon waje upstairs, a sama an rubuta Snack, Drinks and More. Kallon juna suka yi suna yin murmushi, da sauri suka ƙarasa wajen, ƙofar glass din ya buɗe suka shiga. Wajen cin abinci ne mai kyau mai ɗauke da tables da kujeru uku a kowanne table, ga ɗalibai zaune suna ta cin abinci, ciki harda wanda suka zo tare.
Cikin sauri suka nufi empty table suka ja kujera suka zauna, Sanaa ta ɗaga hannunta ta ƙira waiter da ya nufo wajensu already. Bayan ya zo cikin girmamawa ta harshen turanci ya tambaye su.
"What do you want?"

"Two plates of chips, then orange drinks and two bottles of water."
Sanaa ta faɗa mishi tana kallon Khadeeja alamar ya yi mata, kai ta ɗaga alamar ya yi.
Barin gurin waiter ya yi yaje ya haɗa ya kawo musu, ya ajiye a table din gabansu ya bar wajen.
Cikin sauri suka ɗauki fork don ci, Sanaa tana shirin kai bakinta ta ce.
"Allah yasa dai ya yi daɗin ci."

Khadeeja da takai na farko tana taunawa taji Sanaa ta tambayeta, kai ta girgiza ta ce.
"Ba laifi."

Da bismilla Sanaa takai bakinta, a hankali ta hau taunawa, jin da daɗi kaɗan yasa ta cigaba da ci, to idan ba ta ci ba ma me za ta ci. Haka suka ci sosai don yunwa, kaɗan Sanaa ta rage ta ture tana ɗaukar goran ruwa ta buɗe tasha. Khadeeja tas ta cinye ta ɗauki ruwa tasha.
Ganin haka Sanaa ta miƙe tsaye ta ce.
"Mu je ko?"

Miƙewa Khadeeja ta yi tabi bayan Sanaa zuwa wajen biya. Sanaa ta ciro ATM ɗinta master card ta basu, mai karɓar kuɗi ya karɓa ganin Visa ne zai iya cire kuɗi a ciki. Snacks da Sanaa ta gani a jera a glass ta nuna mishi tana so kala uku da drinks biyu da bottle water biyar, ya ɗauko dukka ya mata packaging ya miƙa mata. Ta karɓa tana godiya, ya cire kuɗinsa ya miƙa mata ATM ɗinta ta karɓa tukun tabar wajen, Khadeeja tabi bayanta har ta isota suka jera. Sanaa ƙaramin cape da ta gani a waje an rubuta T-Mobile ta nufa, tana cewa Khadeeja.
"Bari mu ga ko suna sayar da sim card."

Bayan sun isa wajen Sanaa ta tambayeshi cikin turanci sim card take nema, nan ya sanar mata akwai. Ta ce ya ba ta guda biyu, ya ɗauko ya musu register ya ba ta, ta karɓa ta miƙa mishi ATM ɗinta, ya karɓa ya cire kuɗinsa ya mayar mata. Daga haka suka bar gurin, suna tafe ta miƙawa Khadeeja ɗaya ta ce.
"Ga naki."

"Na gode Friendy."
Khadeeja ta ce bayan ta karɓa.
Part ɗinsu suka koma, elevator suka sake shiga ya rufe, Sanaa ta danna numbern floor ɗin da zai kaisu. Khadeeja dai da ido take bin Sanaa ganin sam ba ta nuna ƙauyenci ko tsoro. Yana tsayawa ya buɗe suka fara ƙoƙarin fitowa.
Cikin sauri ya shigo elevator kaɗan ya buge Sanaa da take ƙoƙarin fita, ta tsorata ta yi baya kaɗan ta ba shi hanya, ta matsa tana barin wajen da sauri.

#vote
#comment
#share
#follow

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now