HAMMAD SANAA
Page 20
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookWashegarin Turaki bai je gidan su Sanaa ba, ba ya son hassada mata wata damuwar akan wacce take ciki, don yanzu kana ganinta kaga wacce take cikin damuwa. Ya barta nan da kwanaki, wanda yake sa ran zuwa lokacin za ta iya sanar mishi da damuwarta.
Hutawa ya yi a gida ya kasa ko fita tun safe, sai yamma lis ya lallaɓa suka fita da Sani zuwa bishiyarsa. Can ma dai shuru ya yi sai sama-sama yake amsa hirar Sani. Magriba tana yi suka bar gurin suka nufi masallaci, bayan an idar sallar suka koma gida....
Sanaa tun safe take zuba kunnuwanta don jin sallamar Turaki, amma shuru har dare. Sai ta ji duk ta muzanta, gaba ɗaya ta ji ta ƙara shiga damuwa, shikenan shi ma ya gujeta kamar kowa. Da kanta take nuna mishi ba ta son alaƙar su, amma rashin zuwan shi yau yasa taji babu daɗi. Dalilin haka ta wuni a ɗaki, ta ka sa fita wajen su Maah da Kulsum.
Kulsum ita ma tana ta baza kunnuwanta, amma jin shuru har dare yasa ta jin daɗi, tasan ya hango cikin Sanaa wanda zai sa yaja baya da ita, tasan zai tambayi Sanaa tana da aure, kuma cikin waye jikinta. Idan har ba ta sanar mishi ba ya gwada tambayarta, a lokacin tana jin za ta faɗa mishi gaskiya akan Sanaa da wacece ita, domin ta samu shiga wajen shi.
Maah ganin har bayan magriba Sanaa ba ta fito ba yasa ta miƙe bayan ta gama aikinta, ɗakin Sanaa ta shiga da sallama. Kwance ta samu Sanaa a ƙasa inda ta yi sallar isha'i, ciki ta ƙarasa tana bin Sanaa da kallo tana faɗin.
"Ba ki da lafiya ne? Ko kina jin wani abu ne?"Sanaa zaune ta miƙe tana amsawa murya a sanyaye ta ce.
"A'a, hutawa nake.""To barka, na ɗauka ko kin fara jin ciwo ne."
Maah ta faɗa tana hamdala.
Girgiza kai Sanaa ta yi kanta a ƙasa, tasan saura lokaci kaɗan ya rage mata da bai kai wata ɗaya ba. Ganin haka Maah ta nemi waje ta zauna."Lokaci kaɗan ya rage miki, amma naga ba ki fara shiri ba. Ko kin zo da kayan jarirai?"
Maah ta faɗa tana kallon Sanaa da kanta yake ƙasa tun fara maganar. Dole yasa ta mata maganar, don ganin ta yi shuru ba ta da niyar shirin sayar kayan haihuwa, ita kuma ba ta da kuɗi balle ta gwada siya mata, sai abin da Baah ya ba ta, kuma ba ta ji Baah ya ce iyayenta sun turo kuɗin siyar kayan haihuwar ba.
Tana gani Sanaa ta miƙe da ƙyar, jakarta ta buɗe tare da ɗaukar purse ɗinta ta buɗe ta cire kuɗin ciki gaba ɗaya. Wajen Maah ta ƙarasa ta zauna kusa da ita a ƙasa. Kuɗaɗen hannunta ta miƙa mata ba ta ko kirga ba, kafin ta ce.
"Ga wannan idan za su isa, idan kuma ya yi kaɗan sai mu san yadda za a ciro a bank ɗina."Karɓa Maah ta yi tana mamakin yawansu, kirgawa ta yi taga dubu tamanin da shida ne, dubu hamsin ta ɗauka ta miƙawa Sanaa sauran ta ce.
"Karɓi wannan ki riƙe, don siyan abin yanka da sauran wasu abubuwa nan gaba. Wannan ya isa ina tsammani."Karɓa Sanaa ta yi, jikinta duk ya mutu tana jin wani iri a zuciyarta. Miƙewa ta yi ta mayar sauran kuɗin purse. Daga haka Maah ta miƙe ta fita waje, ta turo Kulsum ta kawo mata abinci. Tana ajiyewa ta fita. Sanaa kaɗan ta ci ta rufe sauran ta miƙe ta fitar ta wanke hannunta ta dawo ɗakin.
Haka har lokacin bacci ya yi ta haye katifarta ta kwanta. Da tunani kala kala ta yi bacci. Bayan ta yi bacci Kulsum ta shigo ta ɗaura musu net ta kashe wutar ɗakin ta shiga ta kwanta.Washegari da safe bayan cin abinci Maah ta musu sallama ta tafi Babban Gida siyayya.
Sanaa tamkar jiya haka ta zuba kunnuwanta don jin sallamar Turaki, sai dai har dare babu shi babu alamarshi, nan ta ji zuciyarta ta ƙara cika da ƙunci da damuwa, shikenan shi ma ya ka sa tsayawa ya fahimceta har ya yanke hukunci. Dalilin haka yasa jikinta ƙara sanyi, haka ta wuni har daren ƙarfe takwas.
Da daren Maah ta dawo ɗauke da kaya, baho babba na mai jego da ƙarami na wankan jariri, sai basket da ciki kayan sanyi kala ɗaya, towel biyu da over-roll biyar, sai pampers mai arba'in guda ɗaya, da sabulun salo na wankan jariri.
Ɗakin Sanaa takai ta ajiye tana ƙiran Sanaa ta zo gani. Kasawa ta yi, dole yasa Maah fitowa ta bari.
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...