Page 5

313 33 3
                                    

HAMMAD SANAA

Page 5
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Ƙauyen Gumsa ƙauye ne da yake ƙarƙashin garin Geidam a Jahar Yobe. Babu hanyar kwalta a ƙauyen, don barin kwaltar ake daga garin Babban Gida a gangara jeji a shiga cikin ƙauyen. Fulani da Kanurai ne mazauna ƙauyen, wanda gidajen ciki bai fi ɗari uku ba. Ƙauye ne da makarantar boko bai damu mutanen ciki ba, sai tsangaya-tsangaya, makarantar primary ƙwaya ɗaya ce a garin. Duk da hakan, ƙauyen akwai service ba sosai ba, da wutar nepan da ba gidan kowa ba shi ma.
Duk ranar kasuwar Babban Gida local government suke zuwa siyayya, domin Geidam da suke ƙarƙashinsa sai an tsallake ruwa ta ƙwaleƙwale kafin mutum ya shiga.

Ƙarfe takwas na dare suka shigo ƙauyen bayan doguwar tafiyar da suka sha tun safe. Da kallo take bin ƙauyen cike da mamakin wani irin waje ta zaɓa kanta rayuwa a ciki, ta ina za ta fara rayuwa a cikin waɗannan mutane ne da take hango tsantsar ƙauyenci a tare da su, duk da garin da duhu, akwai ɗaiɗaiku hasken fitilu na lantarkin da yake jikin gidajen wane da wane, wannan ya bata damar ganin masu shawagi a waje.
Tun da suka bar Babban Gida suka nufi jejin take mamakin ina za su shiga a wannan duhuwar. Sai dai addu'a da neman tsari bai bar zuciyarta, don tasan ita ta nemi takai kanta ko'ina a duniyar nan domin tsira.
Gani ta yi drivern ya yi fakin a ƙofar wani gida, kafin ta tambaye shi taga ya ciro wayarsa Nokia. Da kallon mamaki take binsa ganin ƙira zai yi a wajen da take tsammani babu service. Abin mamaki ji ta yi yana waya da ƙyar don rashin wadataccen service.
Tana ji yana amsawa da sanar da sun iso sannan ya kashe. Gani ta yi yana ƙoƙarin sauƙa.

"Ina za ka je? Ko mun iso?"
Ta tambaya da sauri. Juyowa ya yi taga ya fasa fitar, cike da ladabi ya ce.
"Mun iso. Ga can Mai gidan, bari in mishi magana sai in zo."

To ta ce kafin ya fita tana furta,"Ya Allah!" Tare da share hawayen da suka zubo mata. Ta fara hasaso irin rayuwar da za ta gudanar tun yanzu.
Idanuwanta ta buɗe tana kallon drivern da mutumin da suke tsaye, kusan mintuna biyar taga ya nufo motar, zama ta gyara da kyau. Murfin motar ya buɗe sannan ya ce.
"Hajiya ki fito."

Babu musu ta buɗe murfin motar tana fita tare da bismilla ta taka ƙafarta, iska taji mai daɗi ya buso mata ta kama jikinta tana hamdala. Maganar driver taji daga bayanta.
"Hajiya muje."

Juyawa ta yi tabi bayansa zuwa wajen mutumin da yake jiran su a tsaye, gaishesa ta yi murya ƙasa ƙasa, amsawa ya yi yana tambayarta hanya ta amsa da allahamdulillahi. Daga haka ya nufi cikin gida yana cewa.
"Ku biyo ni."

Bin bayansa suka yi har zuwa cikin gidan nashi. Mace da yarinya suka samu zaune saman tabarma a filin gidan da yake wadace da hasken lantarki, duk da gidan ƙasa ne gidan.
Ganin su ta miƙe tana musu sannu da zuwa. Bayan sun amsa Mai gidan ya ce.
"Kawo tabarma."

Cikin sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko ta fito tana shimfiɗawa. Sanaa ya nuna yana cewa.
"Zauna ki huta."

Babu musu ta cire takalman ƙafafunta flat shoe tana hawa ta zauna, don ta gaji sosai tafiyar awanni goma sha. Bayan zamanta mai gidan yake faɗawa matarsa cewa.
"Ki ba ta ruwa da abinci, nasan ma ba ta yi salloli ba."

Kai Sanaa ta ɗaga a hankali, ganin haka matar da sauri ta miƙe ta ɗauki buta ta cika da ruwa ta kawo mata. Miƙewa Sanaa ta yi ta ɗauka tana cewa.
"Zan kama ruwa."

"Ga bangida."
Ta faɗa tana nuna mata, babu musu ta nufa ganin da haske a ciki, duk da a buɗe yake saman.
Bayan wucewarta mai gidan yasa matarsa kawowa Sanaa ruwa da abinci da sallaya ta shimfiɗa mata saman taburman. Da ta gama ya fita tare da drivern don ba shi masauƙi shi ma.
Sanaa da ta fito ta yi alwala ta hau saman sallayar ta kalli gabar ta fara sallah don kanta bai ɓace ba. Bayan ta idar da sallar magriba ta yi isha, tana addu'o'i taji muryar matar gidan da harshenta na kanuri yafi yawa ta ce.
"Ki ci abinci."

To ta ce tana gyara zama ta buɗe kwanon, da biski miyar yakuwa ta yi karo, ba don yunwar da take ji ba kuma tasan miyar yakuwa da za ta rantse ba ta san abincin ba, don biskin ma ba ta san menene ba.
Da bismilla tasa hannu ta fara ci, tsamin miyar yasa taji daɗinsa ta ci gaba da ci, babu laifi ta ci sosai, ta ɗauki ruwan cikin kofin silba mai sanyi tasha tana hamdala.
Bayan ta gama matar ta sa yarinyarta tashi ta tana cewa.
"Ɗauke kwanon."

Babu musu ta miƙe ta ɗauke, tabar mata ruwan. Sanaa ƙaramar jakarta da driver ya shigo da shi ta jawo, buɗewa ta yi ta ciro magungunta tasha ta mayar. Wayarta ta jawo taga babu missed call na kowa nata kuma babu service na MTN gaba ɗaya ya ɗauke sai Airtel kaɗan, haka ta mayar wayar ta ajiye jiki a sanyaye. Abba da Momma sun yi fushi da ita, da har za su wuni basu nemata ba.

Mai gidan bai jima ba ya dawo, guri ya samu ya tsaya yana faɗawa matarsa ya ce.
"Ya Fanna kin gama gyara ɗakin ne?"

"Eh tun safe."
Ta ba shi amsa da shi. Jin haka ya ce.
"To ki nuna mata ta shigar kayanta, tana buƙatar hutu ai."
Kallo Sanaa ya yi da kanta yake ƙasa tana jin su, ya ci gaba da cewa,"tashi ki shiga ciki ki huta kinji."

Babu musu ta miƙe, akwatinta taja tana ɗaukar ƙaramin tabi bayan matar shi zuwa ɗakin da taga ta shiga. Ɗakin filaste yake da siminti an shimfiɗa leda, gefe katifa ce ƙarama kuma sabuwa mai tudu, saman shi bedsheet da bargo da filo ne duk sabi a gidan su, da alama ba a taɓa amfani da su ba har da net sabo a cikin gidansa, labule ne kaɗai babu a ɗakin. Babu laifi ɗakin, amma ga wanda ya saba rayuwa a irin ɗakin Sanaa, zai ga nan tamkar kurkutu aka kawosa, haka ga Sanaa ma da ta yi tozali da ɗakin.
Amma ya ta iya? Ita ta zaɓa, dole ta ƙarasa ciki tana ajiye akwatinta a gefe. Fitar matar bayan ta nuna mata yasa ta karkaɗe katifar tana zama tare da buga tagumi tana bin ɗakin da kallo. Tunanni yadda za ta iya fara rayuwa a wannan gida da ƙauyen take.

...

Bayan fitar matar Ya Fanna ta samu mijinta zaune, gefe ta zauna. Ganin haka ya mayar da hankalinsa kanta yana cewa.
"Ya Fanna ita ce yarinyar da Isa zai kawo daga Habuja, wacce muka yi waya da Babanta jiya ya aiko kuɗi a siya mata kayan kwanciya, har ya bada kuɗaɗen da zan saya kayan abinci don ita. Don Allah ki riƙeta amana, kinga dai yadda muka fara samun kuɗi a wajen babanta ta dalilinta." Ya faɗa yana zaro wayarsa a aljihunsa ya ci gaba,"bari in ƙira Babanta na sanar mishi ta iso lafiya."

Da ƙyar ya shiga don rashin service. Bayan Alhaji Hussain ya ɗauka mai gidan ya gaishe da shi yana sanar mishi Sanaa sun iso lafiya. Ta ɓangaren Alhaji Hussain numfashi ya sauƙe yana cewa.
"Na gode sosai Malam Umaru, ku kula min da ita don Allah. Komai ku ke buƙata ku min waya, zan turo ta hanyar dana turo jiya."

"In Sha Allah Alhaji karka damu."
Faɗin Malam Umaru yana tabbatar wa Alhaji Hussain zai riƙe Sanaa da kyau. Daga nan suka yi sallama ya kashe, kallon matarsa ya yi yana faɗin.
"Kin ji ko?"

Kai Ya Fanna ta ɗaga cikin farin ciki, haka ya ci gaba da cewa.
"Za ta zauna ne damu kafin zuwa lokacin da ya faɗa. Mu kula da ita tsakani da Allah babu cutarwa, in sha Allah zamu samu lada a wajen Allah, kuma zamu samu lada a wajen mahafinta na kuɗi."

"Da yardar Allah, Allah ya bamu iko."
Ya Fanna ta faɗa cike da jin za ta yi. Duk da rashin ilimin ƙauyen amma sun yi imani da kiyaye dokokin Allah da suka sani. Hakan yasa suke jin su ɗin za su iya kula da Sanaa ba kamar yadda iyayenta suka kasa ba. Ƙaddara ce ta sauƙa mata ita ma, da bata wuce kan kowa.

...

Abuja

Tun da yaga magriba ta yi ya fara tunanin ta ina zai fara gadin gidan da yake da girma haka, bai taɓa yin wannan sana'ar ba sai da ƙaddara ta sa shi aikata haka.

#KeepCommeting
#KeepVoting

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now