Page 3

425 36 3
                                    

HAMMAD SANAA

Page 3
Wattpad PhartyBB
Nagarta Writers Association
#FreeBook

Idanuwanta ta buɗe jin kamar motar ya tsaya ga ƙara da hayaniya yana tashi kaɗan kaɗan. Ganin su ta yi cikin gidan Mai da yake ɗauke da mutane masu sayar da abubuwa.
Kallon drivern ta yi ganin ya faka a gefe.
"Lafiya?" Ta faɗa tana gyara zama.
Drivern juyawa ya yi ya kalleta yana cire seat belt, cikin ladabi ya ce.
"Bari mu yi sallah Hajiya, la'asar ta kusa kuma ko azahar bamu yi ba."

Wayarta ta ɗauka ta duba taga uku da mintuna. Kai ta girgiza ta ce.
"To shikenan."

Daga haka ya fita ya nufi masallaci, ita ma fita ta yi tana bin wajen da kallo, ba ta yin tafiya balle tace nan ɗin inda ta sani ne ko tasan wajen. Masallacin da ta gani na mata ne ta nufa, buta ta ɗauka cikin butocin da suke tare taji da ruwa, tsugunnawa ta yi tai alwala bayan ta idar ta shiga ciki inda ake sallar ta yi azahar ta haɗa da la'asar da zai same su a hanya ganin lokacin ya kusa. Bayan ta idar ta fito ta shiga cikin motar ta zauna jiran shi, mintuna uku ya fito daga shagon wajen ɗauke da ledoji a hannunsa.
Motar ya shiga ya kunna yaja suna barin wajen, sun ɗauki hanya yasa hannu ɗaya ya ɗauki ledar ya miƙa mata.
"Hajiya na saya miki meatpie da hollandia ko za ki ci."

"Na ƙoshi."
Ta faɗa tana girgiza kai, yunwar ma ba ta ji don damuwar da take ciki.
Bai fasa miƙa mata ba ya sake cewa.
"Ki daure Hajiya don Allah."

Hannu tasa ta karɓa, buɗewa ta yi ta ɗauka ta fara ci a hankali tana haɗawa da hollandia, sai taji daɗinsa ta ci gaba da ci. Ganin haka shi ma ya buɗe nashi ledar yana ɗauka ya fara ci a hankali. A haka suka ɗauki hanya.
Bayan Sanaa ta gama ci ta rage hollandia ta ajiye sauran tana hamdala, kanta ta kwantar tana lumshe idanuwanta.

***

Da gudu ta wuce ɗakinta cikin murna, tana shiga saman gadonta ta haye tana ɗaukar wayarta, lambarsa ta laliɓo ta doka mishi ƙira. Yana ɗauka cikin murna ta ce.
"Uncle ina wuni? Ya aiki?"

Daga ɓangarensa ya amsa cike da farin cikin jin muryarta. Ya ji haushin rashin zuwan graduation nata da bai yi ba haka iyayensa ma.
Sanaa ciki da ɗoki ta fara koro mishi bayani.
"Uncle na faɗawa Abba ya amince, ranar Sunday don Allah ku ƙoƙarta ku zo, harda mu Momy da Ilham."

"Really Fav?"
Ta ji ya faɗa da murna ta ɓangarensa. Kamar yana ganinta ta ɗaga masa kai tana cewa.
"Da gaske wallahi."

Tana ji ya sake faɗin.
"In sha Allah za ki ganmu kafin ranar. Yau zan yi shiga da fice sai na sama mana ticket, ko ni da Ilham ce za mu zo."

"Allah ya nuna mana Uncle. Sai anjima zan fara list na abubuwa."

Da amin ya amsa sannan ta kashe wayar, miƙewa ta yi ta fita ta koma wajen iyayenta, samu ta yi Abba ya fita sai Momma, mai aiki na tattare kayan gift ɗin da suka buɗe suka gani suka bari a wajen, kusa da Momma ta zauna tana sanar mata sun yi waya da Uncle ya mata alƙawarin zuwa shi da Ilham.
Kallonta Momma ta yi tana cewa.
"Kin san dai yanayin aikinsa ko."

"To Momma ni bazan yi ha idan ba zai zo ba."
Faɗin Sanaa tana tura baki. Baki Momma ta taɓe ta ce.
"Allah yasa ki ganshi to."

"Ya min alƙawari kuma sai ya cika."
Ta ce tana miƙewa tabar wajen ta wuce ɗakinta. Jakarta na makaranta ta ɗauka ta ciro notebook da biro ta koma gaban desk da take karatu ta zauna. Lissafin abubuwan da take bukata ta yi hatta kayan da zata sa, bayan ta gama ta rufe ta mayar tana ɗaukar iPad nata.
A ɗaki ta wuni ita ɗaya kamar koyaushe har dare. Da daren ƙarfe tara ta miƙe ta shiga wanka ta fito tasa kayan bacci riga da wando, hijabinta na sallah ta ɗauka tasa tana ɗaukar list ɗin da ta yi ɗazu ta fita. Falon ta sauka inda taji muryar iyayenta, nan ta hango su saman dinning, wajen ta ƙarasa tana jan kujera ta zauna.
Da kallo duk suka bita da shi, miƙawa Abbanta papern ta yi bayan ya karɓa ta ce.
"Abba na lissafa komai."

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now