Page 11

224 25 3
                                    

HAMMAD SANAA

Page 11
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

"Babu wacce ta taɓa zuwa wajen nan sai ke. Kuma na yi mamaki da Turaki ya ka sa aiwatar da komai a kanki."
Kulsum ta faɗa yayinda suke tafiya, har lokacin ita ma mamakin ƙarfin halin Sanaa take, gefe ɗaya kuma Turaki da ya kasa yin komai akanta.
Sanaa murmushi ta yi tana gyara mayafinta da ya sauƙo ta ce.
"Ai idan kun nuna kuna tsoronsa, shi zai sa ya muku abin da yaga dama."

"Babu batun tsoro. Shakkarsa ake duk ƴan matan ƙauyen nan, har maza ma."
Kulsum ta ce mata. Baki Sanaa ta taɓe ba ta ce komai ba.
Haka suka ƙarasa wajen deɓar ruwan, Kulsum ta saka bucket nata layi, ita kuma Sanaa ta matsa gefe ta tsaya.
Layi bai jima ba ya iso kanta, ta matsa ta tuƙa ruwa ya zubo, bayan ya cika ta ɗauki bucket ɗinta suka bar wajen. A hanya ko kallon inda su Turaki suke Sanaa ba ta yi ba, haka suka wuce. Bayan shigarsu gida Kulsum ta juye ruwan a drum, tana ƙoƙarin fita Sanaa tabi bayanta.
Ganin haka Kulsum da sauri ta dakata da tafiyar tana kallon Sanaa, sannan ta ce.
"Don Allah ki koma ki huta."

Dariya Sanaa ta yi har fararen hakwaranta suka bayyana jerarru.
"Ni ba wajen Turaki zan je ba, rakiya zan miki matsoraciya."

Ajiyar zuciya Kulsum ta sauƙe duk da ba ta gama yarda da ita ba, haka suka kama hanya. Lokacin da suka wuce wajensu Turaki ba ta kallesu ba nan ma, haka suka ƙarasa wajen deɓar ruwan. Babu layi, hakan ya ba Kulsum damar ɗeba ruwa suka dawo gida.
Bayan shigarsu gida, Sanaa saman shimfiɗaɗɗan tabarmar ta zauna don ta gaji, hakan ya yi wa Kulsum daɗi, bayan ta juye ruwan ta fita ƙaro wani.
Zaune shuru suke babu wani hira tsakanin Maah da Sanaa. Har Kulsum ta sake yin sawu uku, tsaf ta kusan cika drum din sannan ta bari ganin magriba ta yi.
Alwala suka yi dukjansu, Sanaa ta wuce ɗakinta, hijab ta saka ta yi sallah, da ta idar ta yi addu'o'i da ta sani tare da neman sassauci a wajen Allah. Bayan ta shafa ta miƙe ta fita, kusa da Kulsum ta zauna da ita ma ta yi nata sallar, duk da ba wani hirar suke ba zama tare dasu yana ɗauke mata kewa da zama shuru. Wayarta babu wani network balle ta yi chat, iyayenta ta ƙira sun ƙi ɗauka balle su kwantar mata da hankali, hakan yasa komai ya fita a ranta, balle chat da tun da duniyarta ta canza ta rufe kowanne a account nata a yanar gizo. Nemawa kanta nutsuwar ruhi da kwanciyar hankali take, ba ta bin labaren duniya ba.
Yadda ta zuba musu ido tana kallo Kulsum ta miƙe ta karɓa Maah aikin raba abinci, murmushi ne ya suɓuce mata a fuska, cikin lokaci ƙanƙani kuma murmushin ya ɗauke a fuskarta. Nata rayuwar ta fara tunawa yadda ba ta yin ko wani aiki.

...

Da sauri ta shiga kitchen jin motsi. Ta duba ɗakin Momma ba ta nan, Abba kuma ya fita balle ta ce tana ciki, hakan yasa ta sauko ƙasa ko tana falo. Ganin ba ta nan ta nufi kitchen jin motsi. Momma ta hango tsaye a bakin sink, cikin sauri ta ƙarasa wajenta tana faɗin.
"Momma ina mai aikin? Ki ke wanke wanke."

"Tana zazzaɓi."
Momma ta ce tana ɗauraye plate ɗin hannunta ta ajiye ta matsa gefe.
"Zo ki ƙarasa."

Fararen idanuwanta ta ware, sai kuma ta turɓune fuska.
"Ni kuma Momma? Kin san ban iya ba fa."

Harararta Momma ta yi tana cewa.
"Oya zo ki yi, ina da abin yi. Na leƙa kina bacci yasa na barki, da ke za ki yi."

Bubbuga ƙafa ta yi a ƙasa cike da taɓara.
"Momma don Allah ki barni. Ni wallahi na tsani wanke wanke, balle ma ba iyawa na yi ba kin sani."
Sanaa ta ƙarasa maganar tana kifta ido za ta yi kuka.
Ƙofa Momma ta nuna tana ɓata rai ta ce.
"Fita min a guri. You're 18 amma kina abu kamar yarinya."

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now