Page 17

234 32 6
                                    

Assalamu alaikum
Ina masu business da suke nema a tallata musu hajarsu, to masu buƙata a tallata musu cikin sauƙi ƙofa buɗe take. Ga duk mai buƙata, zai iya tuntuɓar lambar nan 07037487278
...

HAMMAD SANAA

Page 17
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebook

Hammad idanuwansa ya lumshe ya buɗe yana zubawa fuskar wayarsa ido, gama wayarsa da Ummi da Sultan kenan. Kullum tuni suke mishi da lokacinsa ya kusa ƙarewa, musamman yau da a lissafin shi saura watanni huɗu.
Komawa ya yi baya ya kwantar da kanshi saman pillow, a hankali ya lumshe idanuwansa.
...

Masarautar Allah Ranai, ya samo asali ne daga tushen kaka da kakanni, fulani ne da suke ma masarautar laƙabi da Allah yaja zamani. Bayan rashin Sarki Hammadu Harɗo aka ɗaura ɗanshi na farko mai suna Muhammad Al-Khaleefa.
Sarki Hammadu Harɗo yana da yara maza uku da mata biyu wanda duk yaran mace ɗaya ce Hasiya, matarsa na biyu Mariya har ya rasu ba ta haihu ba, ganin da sauran girmanta ta yi wani aure bayan gama takabarta. Tana aure ta haihu da shekaru biyu, sai kuma ya zamto aka fara magana cewa Uwargida ita ce ta mata asiri.
Uwargida Hasiya ba ta taɓa gigin magana ba, domin sam bai dameta don tasan babu abin da ta mata, ikon Allah ya hanata haihuwa.
Saurata ya koma hannun yaronta na farko Muhammad Al-Khaleefa, babban mutum mai yara uku maza biyu mace ɗaya. Haka sauran ƴan uwanshi ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya duk sun yi aure, wasu a kusa da gida wasu nesa.
Mutane suna jin daɗin sarautar Muhammad Al-Khaleefa, yana mulki daidai da yadda ake buƙata.
Matarsa Gimbiya Nanah tare da yaransu uku, sai mahaifiyarsa da suke rayuwa cikin masarautar tare. Duk sun girma sun yi wayo. Na fari shi ne Qadeer Muhammad Al-Khaleefa, na biyu Hameed Muhammad Al-Khaleefa da macen Rahmatullah Muhammad Al-Khaleefa. A lokacin karatun boko ya fara shigowa, hakan yasa ya nemawa yaransa gurbi.
Rayuwa tana tafiya, abubuwa suna canzawa har Qadeer ya kammala karatun sakandare, anan yaji sha'awar zuwa ƙasar Turkish ƙara karatun boko. Sarki Muhammad Al-Khaleefa bai so ba ganin shi ne babban yaronshi namiji, Hameed ba wani girma ya yi ba. Ganin yaron ya dage kuma yana so yasa aka nema mishi gurbin karatu. Cikin sa'a yin haka da watanni uku ya tafi.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafi har aka kwashe shekaru biyar, a lokacin Hameed ya shiga jami'a don shi ƙin tafiya ya yi ganin shi ɗaya ya rage wajen mahaifinsa, sai ƙannensa da yaransu da suke zuwa mishi lokaci zuwa lokaci. A wannan lokaci tsohuwa matar Hammadu Harɗo wato Hasiya ta rasu, mahaifiyarsu. Sun ji mutuwarta don ita ɗaya ta rage musu, an tara jama'a wajen jana'izarta, haka suka miƙata gidanta na gaskiya.
Bayan rasuwarta aka yi auren Rahmatullah inda mijinta yake ƙasar Sudan da aiki, haka aka yi biki aka kaita gidanta. Duk abubuwan da suka faru Qadeer Al-Khaleefa bai taɓa zuwa ba, babu shi babu labarin shi. Nan abin ya fara damun iyayensa ganin har an ɗauki shekaru shida bai zo, babu labarin shi. Amma babu yadda suka iya haka suka zuba sarautar Allah ido.
Hameed ya gama makaranta inda ya karanci sociology, ya samu aikin yi cikin sa'a don sanayyar mahaifinsa. A lokacin aka kawo mishi maganar aure, tabbas yana buƙatar hakan don ya kai. Tuni ya nuna ƴar uwarsa yake so ƴar ƙanin babansa na farko. Dangi sun yi murnar jin haka, musamman iyaye maza biyun. Cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida biki wata uku.
Cikin hukuncin Allah lokaci ya yi aka ɗaura auren Hameed Al-Khaleefa da matarsa Rabi'atul Adawiyya. Cikin gidan aka ajiyeta a ɓangaren Hameed da aka gyara musu. Yana da girma ga dakunan isasshe, ga masu aiki bayi a zube.
Shekaru uku da auren su Sarki Muhammad Al-Khaleefa ya kwanta jinya, a lokacin Rabi'atul Adawiyya tana da cikin wata tara. Jinyar sati ɗaya rai ya yi halinsa inda mutuwar Sarki Muhammad Al-Khaleefa ya girgiza masarauta da mutane sosai, musamman Gimbiya Nanah da zaucewa kaɗai ne ba ta yi ba. Haka Hameed ya kasa kuka tsabar tashin hankali, amma ya suka iya haka suka miƙa shi gidansa na gaskiya.
Washegari aka fara magana akan sabon sarki da za a ɗaura. Hameed yakai riƙe muƙamin amma shi ne ƙarami, Qadeer ya kamata a ba wa, Qadeer kuma har lokacin babu labarin shi, ga kuma ƙannen Muhammad Al-Khaleefa da suka ce sun haƙura a ɗaura Hameed saboda sarauta ta koma wajensu, duk da wasu sun yarda wasu kuma suna ganin rashin dacewar haka.
Da ƙyar Hameed ya haƙura akan ba yadda ya iya. Tun ranar ya dawo Sarki Hameed Al-Khaleefa, ya ajiye aiki a gefe yana tafiyar da sarauta cikin aminci da yarda, tamkar yadda mahafinsa yake yi.
Rasuwar Sarki Muhammad Al-Khaleefa da sati uku Gimbiya Rabi'atul Adawiyya ta haiho ɗanta namiji, dangi sun yi murna musamman iyayen Rabi'atul Adawiyya. Satin suna ya raɗawa yaro suna tsohon sarki Hammad Hameed Al-Khaleefa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har tsawon shekara ɗaya, a ranar suka samu gaggarumin labari don dawowar Qadeer tare da balarabiyar mace ƴar ƙasar Turkiyya. Bayan zama da murnar dawowarsa ya sanar musu rasuwar mahaifinsa ya sa shi dawowa, kuma ya dawo kenan tare da matarsa Zaituna da ɗan su ɗan wata biyar.
Ɓangare aka ware musu suka fara rayuwar su ciki, rashin yin maganar a ba shi sarauta shi ne yasa mutane jin hankalin su ya kwanta. A tsammaninsu zai ce shi ne babba a sauke Sarki Hameed a ɗaura shi, shi ya cancanta.
Gimbiya Rabi'atul Adawiyya da Zaituna sun haɗa kansu babu kishin balbali. A lokacin Rahmatullah ta zo ganin gida ita ma da yaranta biyu mace dana miji. Satinta biyu ta koma.
Shekaru sun ja Gimbiya Rabi'atul Adawiyya ta sake haihuwar namiji, Sarki Hameed yasa sunan mahaifinsa Muhammad Al-Khaleefa suna ƙiransa Sultan, bayan shi kuma shuru har tsawon shekaru goma sannan ta haifi tagwayenta Bashar da Bushara. Zaituna bayan ɗanta Khaleed ta haifi Haris, ta sake haihuwar mace Jaana sannan namiji Ayaan.
Yara mazan Hammad, Khaleed, Sultan da Haris sun haɗa kansu babu bambanci, sun riƙe juna da amana, sun ɗauki yarda sun ba juna. Zaratan maza masu kyau da kowanne da halinsa. Haka Jana da Bushra, Ayan da Bashar.
Hammad ba shi da surutu da son hayaniya, wanda mutane suke mishi kallon mai girman kai da miskilanci. Haka ga Khaleed shi ma ba shi da faɗa, sai dai idan kun zauna za ku yi hira. Sultan yana da saurin fushi amma akwai tausayi, sai Haris da ya zamto mai surutun cikin su.
Hammad, Khaleed da Haris abu ɗaya suka karanta ban da Sultan da ya ƙi hakan.
Haka rayuwar masarautar ta ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da ƙaddarar su ta tarwatsa su. Inda aka rasa wanene magajin kujerar sarki tsakanin Hammad da Khaleed.

...

Ido Hammad ya buɗe tare da kai hannu ya shafa kansa, wannan ruɗanin kaɗai yana sa shi tunani, balle aje ga batun abin da ya fito da shi. A zuciyarsa ya fara faɗin.
'Kuma dole ya karɓi sarauta, dole ya zamto musu Sarki. Ko da za a ce ƙarfin halinsu ya yi yawa, na ƙwace kujerar mulki daga inda ya kamata, dole ya karɓa ko da na awanni ne ya mulkesu.'

***

Duk da damina ya shigo ita kam zafi take ji kwana biyun. Bayan farkawarta ta gama abin da za tayi wanka ta yi, kowa na wanka da ruwan ɗumi don sanyi da aka yi jiya dalilin anyi yayyafi gari ya yi sanyi, amma ita da ruwa na drum ta yi. Ɗaki ta shige ta fito, bayan ta fesa turare ta fara neman kayan sawa.
Akwatinta ta bincika kaf, duk rigar da ta ɗauka sai taga zai kamata. Da ƙyar ta samu wani abayarta marar nauyi sannan ya mata yawa ta zurma. Juyi ta yi ta sake yi tana kallon kanta, bai kamata ba kuma bai bi jikinta ba rigar, amma mutum mai sa ido tsaf zai ganota, musamman iyayenmu manya mata. Amma ya ta iya, shi kaɗai ta samu daidai da zai taimaka mata ta samu su je su dawo.
Sauran kayan ta saka a akwati ta mayar ta ajiye, jakarta ta buɗe ta ɗauki purse ɗinta ta zari dubu biyar. Rufewa ta yi ta mayar, mayafin rigar ta ɗauka ta yafa ta kewaye jikinta da shi sannan ta fita.
Samu ta yi Kulsum ta shirya tana jiranta. Maah da take zaune ta kallesu, fuskarta da murmushi ta ce.
"Kar ku jima."

"To Maah."
Sanaa ta ce tana yin gaba. Haka Kulsum ta amsa ita ma suka fita.

Kasuwa suka nufi, domin yau ne kasuwar ƙauyen, mutanen karkarar gefe da gefen ƙauyen suna shigowa cin kasuwa. Tafiya suke suna hira har suka iso, anan Sanaa ta fara cin karo da mutane bambanta, kowa da abin da yake siyarwa. Wasu gyaɗa, wasu nono kasancewar damina ya shigo, haka kayan lambu ma sosai a gurin.
Sanaa babu abin da ya shiga ranta kamar gyaɗa da nono, hakan yasa ta kalli Kulsum ta ce.
"Ina son nono da gyaɗa ɗanya."

"To mu je ki siya."
Kulsum ta faɗa tana yin gaba, Sanaa tabi bayanta. Dubu biyu ta miƙawa Kulsum bayan isarsu wajen, karɓa Kulsum ta yi ta siya mata kowanne na duba ɗadɗaya, bayan an saka a leda ta miƙawa Sanaa ta karɓa. Daga nan suka siya kayan miya irinsu tumatur, albasa, attaruhu, da lawashi sannan suka dawo gida.
Bayan sun huta Sanaa ta miƙe ta ɗauko babban roba a kitchen ta juye nonon takai ɗakin Maah ta ajiye. Zama ta yi ta buɗe gyaɗar ta baje ta hau ci tamkar babu gobe, don ta ji ya mata daɗi. Kulsum dai dariya take mata ta ce.
"Ba za ki bari a dafa ba."

Girgiza kai ta yi baki cike da gyaɗa.
"Na fi son haka. Ina zan iya jira ya dahu."

Dariya dukka suka mata, haka ta ci sosai da ƙyar ta bari, shi ma sai da Maah ta ce.
"Wannan gyaɗar zai dameki fa."

Dalilin haka ta hakura ta bari suka ci gaba da hira. Da daren Kulsum ta dama mata nono cikin roba, tas ta shanye, Kulsum dai tana ganin ikon Allah wannan ci haka, sai dai ta mata dariya, don ba ta son mata magana ta ji ba daɗi, don tasan babu mai mata maganar da zai ɓata mata ranta ko tayar mata da hankali. Dole yasa taja bakinta ta yi shuru.

...

#vote
#comment
#follow
#share

HAMMAD SANAAWhere stories live. Discover now