HAMMAD SANAA
Page 50
Na Pharty BBSanaa ɗauke idanuwanta ta yi cikin na Hammad ta ja dodon numfashi ta sauƙe, haka Hammad ma ya sauke numfashi yana gyara kwanciyar Nana a jikinsa.
Ya yi gyaran murya ya ci gaba da faɗin.
''Bayan na nemi mu yi magana ki ka ƙi washegari nabar gidanku na dawo gida, hankalina bai kwanta ba har sai ranar da muka zo gidanku wajen Alhaji tare da su mai martaba, anan muka tarar iyayen Turaki, bayan gaisuwa da zama aka yi maganar fahimtar juna, inda Turaki ya hakura ya bar min ke don saboda babyna kuma da abin da ya faru tsakaninmu don rufin asirinmu, wanda bai sani ba don shi zatonsa aure kika yi kika fito da ciki. A take muka biya sadaki aka ɗaura mana aure, ni na hana Turaki ya faɗa miki duk da nasan su Alhaji zasu faɗa miki, sai aka ci sa'abasu faɗa miki ba.
Saura min abu ɗaya na cika burina don Allah za ki taimaka min? Na hukunta su Khaleed da Amir da hannuna, khadeeja kuma duniya kaɗai za ta koya mata hankali.''Sanaa miƙewa ta yi bayan gama sauraron maganar shi ta ce.
''Ni dai don Nana zan zauna tare da kai. Kuma don naga yadda za ka hukunta mugayen nan."''Ba kya sona? Ai ni ina sonki, tun ranar da na fara jin kamshinki, ko ba ki ji na miki alkawarin zame miki gata ba a wancan daren?''
Hammad ya faɗa yana miƙewa shi ma.
Sanaa daki ta wuce ta rabu da shi, Hammad bayanta yabi zuwa ciki ya sameta zaune tana waya. Sanaa bayan shigarta ta ɗauki wayarta ta kira Baah ta sanar musu an ɗaura aurenta da mahaifin Nana ba da Turaki ba ne, kuma har ta tare.
Hammad kwanciya ya yi ya kwantar Nana a gefe ganin ta yi bacci. Yana jin Sanaa tana waya har bacci ya ɗauke shi. Ita ma da ta gama ta juya ta kalle su, taga kamar su ɗaya. Kwanciya ta yi tana tunanin me ya kamata ta yi, aure an riga an ďaura a inda tasan ba za a taba mata gori ba, kuma ta ga iyayensa suna sonta. Da wannan tunani bacci ya ɗauketa.
Haka suka sha bacci har azahar kukan Nana ya farkar dasu. Sanaa ta jawota gefenta ta fara bata nono, Hammad ya miƙe ya shiga bathroom ya ɗaura alwala ya fito ya fita ya nufi masallaci.
Sanaa da ta shayarta ta miƙe ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito ta fara sallah. Bayan ta idar ta ɗauki Nana suka fita falo, anan ta samu an kawo musu abinci an jera a center table.
Zama ta yi don ba yunwa take ji ba, haka Hammad ya dawo ya same su, zama shi ma ya yi ya karbi Nana. Sanaa da kallo ta bi shi ganin baya gajiya da ďaukarta.
Ganin ba shi da niyar neman abinci ta ce.
''Abinci fa?''''Sai anjima gimbiyar Hammad. ''
Ya faɗa yana murmushi, murna a zuciyarsa ganin ta damu da shi, dama yasan rigima ce.
Haka suka zauna har yamma, bayan la'asar suka ci abinci, Sanaa ta tattare ta fitar suka haɗu da baiwa ta karɓa da sauri ita ta koma falo.
Hammad da ya fita sallar magariba bai dawo ba sai ƙarfe goma. Ya samu Ilham ta zo ta ɗauke Nana, Sanaa ta haye gado ta kwanta ta yi shirin bacci. Kayan hannunsa ya ajiye ya shiga bathroom ya yi wanka, ya fito yasa jallabiya da boxes. Gadon ya haye ya jawo abin hannunsa ya buɗe, kaza ce da fresh milk, ya ajiye a gefe ya kalli Sanaa yaga ta rufe idanuwanta kamar mai bacci.
Hannu yasa ya ɗagata yana faɗin.
''Tashi ki ci kazar amarci. Nasan idonki biyu.''''Ni na koshi.''
Sanaa ta faɗa tana kokarin kwanciya. Hammad ya hanata ya riketa gam, yasa hannunsa ɗaya ya ɗauki tsoka ɗaya ya kai bakinta ya tura. Dole ta fara ci, haka ya yi ta bata ta ci da dama sannan ya bata fresh milk tasha ta koshi nan ya barta.
Sanaa bathroom ta shiga ta wanke bakinta, ta fito ta hau gado ta lullube jikinta. Hammad da ya ci ya koshi ya mike ya fitar komai ya dawo ya shiga bathroom, ya wanke bakinsa ya kashe wutar dakin ya nufi gado ya kwanta gefen Sanaa.
Hannusa yasa ahankali ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam ganin ta fara mutsu mutsu kwacewa, ganin ta ƙi tsayawa Hammad ya fara rabata da kayan jikinta cikin salo.
Sanaa jin haka ta ƙara tsorata ta ce.
"Ni fa bana son wannan abin''
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...