HAMMAD SANAA
Page 21
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookSanaa ce kwance a ɗaki saman katifarta take bacci, bayan yin sallar asuba ta koma jin yadda bayanta yake riƙewa, ba ta jima ba bacci ya ɗauketa mai daɗi.
Idanuwanta ta buɗe da sauri jin wani juyi da cikinta ya yi, zaune ta miƙe tana kai hannunta ta dafe cikin, ji ta yi ya ci gaba da juyi yana sauƙa mararta. Dafe bayanta ta yi tana miƙewa tsaye da ƙyar jin ciwon sai gaba yake yi. So take ta fita ta sanar da Maah ta ka sa, nan ta zube a ƙasa tana sakin salati ganin ruwa yana bin ƙafarta.
Duk ƙoƙarin Sanaa ta fita waje ta ka sa sai ciwo, kuka ta sa tana kwalla ƙara da ƙarfi tana ƙiran.
"Maah! Maah!! Cikina da marata."Ba ta gama faɗin abin da za ta ce ba Maah ta ɗago labulen ta shigo, ganin Sanaa a wannan halin yasa ta ƙarasa ciki, da sauri ta ɗagota.
"Naƙudar ce? Har faya ta fashe.""Ban sani ba."
Sanaa ta faɗa cikin kuka hawaye shar shar suna zuba. Haka dama ake ji, azaba tamkar ana yankata, ba ta taɓa jin ciwo irin wannan ba.
Maah dai ganin naƙuda ce gadan gadan ya zo ma Sanaa yasa ta saketa ta fita. Ɗakinta ta shiga da sauri ta kwaso tsofin zannuwanta guda biyu da leda fari, sai reza guda ɗaya ta fito ta koma ɗakin Sanaa.
Har lokacin Sanaa kuka take tana juyi dafe da cikinta da burinshi kawai ya fito duniya. Sanaa azaba ya yi azaba ba ta son lokacin da ta fara faɗin.
"Ku ƙira min Mommana, don Allah ku haɗani da Momma da Abbana. Wallahi mutuwa zan yi na sani, ciwo nake ji a marata da cikina."Maah dai sai shirin inda Sanaa za ta haihu take, tasan duk wahalar naƙuda ce irin wacce take zuwa gadan gadan tun da ga har faya ta fashe, irinta tafi wahala akan wadda yake yi ya bari.
Ledar ta fara shimfiɗa sannan ta shimfiɗa zani guda ɗaya, sauran ta ajiye a gefe tare da rezar. Wajen Sanaa ta yi tana kamata ta ce.
"Ki ƙoƙarta ki hau kan nan."Girgiza kai Sanaa ta yi.
"Ki ƙira min Mommana, ku kaini asibiti.""Ki ƙoƙarta dai."
Faɗin Maah tana miƙar da ita da ƙyar, ka sa miƙewa Sanaa ta yi a tsunkuye taja ƙafafunta tana hawa saman shimfiɗar.
Ganin haka Maah ta gyara mata tana ɗaga rigarta sama ta ce.
"Bari in duba.""Ina? Me za ki duba?"
Sanaa ta faɗa da sauri tana kallonta duk da ciwon da take ji.
Maah ba ta kulata ba ta ware ƙafafunta, salati ta yi ta ce.
"Kai ya kawo, ki yi nishi."Sanaa salati ta yi tana runtse idanunta, haihuwa ƙanin mutuwa. Cike da azaba ta yi nishi da ƙarfi, wani nishin ta sake sakewa tana ji jariri yana fitowa cike da azaba.
Maah da ta samu ta riƙo kan jairirin rabin jikinsa ya fito ta sake faɗin.
"Ki ƙoƙarta, saura kaɗan."Wani nishi Sanaa ta yi da dukkan sauran ƙarfinta, tana ji jariri ya faɗo tare da sakin kuka, baya ta yi ta kwanta tana sakin wani kukan da ta rasa na menene, don yana faɗowa ta nemi sauran ciwon ta rasa sai kaɗan kaɗan da ciwon jiki.
Maah rezar ta ɗauka ta yanke cibiya, ta ɗauki zani ta goge jikin jariri sannan ta ɗauki wani ta nannaɗe a ciki ta ajiye saman katifa.
Maah daga nan ta hau gyara Sanaa, daɗinta ɗaya ba ta ƙaru ba, kuma idan haka ne haihuwar bai ba ta wahala ba, don da naƙudar da haihuwar cikin lokaci da bai wuce awa ɗaya ba ta yi .
Tsaf ta gyara Sanaa ta ɗagota ta jinginar da ita jikin gini, ta nannaɗe kayan haihuwar ta fitar waje, dawowa ta yi ta sake goge wajen da ta haihu ta fita waje. Wuta ta hura ta ɗauki babban tukunya ta zuba ruwa don yin wankan Sanaa da na jariri.
Ɗaki ta koma ta samu har lokacin Sanaa zaune, wannan lokaci idanuwanta a rufe suke tana fitar da numfashi.
Kusa da ita ta zauna tana faɗin.
"Sannu, Allah ya ba ki lafiyar shayarwa ya kuma raya."
YOU ARE READING
HAMMAD SANAA
RomanceCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...