Assalamu alaikum
Masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin sauƙi, to ƙofa buɗe take. Ga duk mai buƙata, zai iya tuntuɓar lambar nan 07037487278...
HAMMAD SANAA
Page 15
Wattpad PhartyBB
NWA
#freebookCikin sauri Kulsum tabi bayan Sanaa suka jera, haka suka kama hanya babu wacce ta yi wa wata magana. A hanyarsu ta tafiya Sanaa ko ta kalli wajen Turaki yayinda za su wuce, tasan warhaka yana nan. Aikuwa idonsa akan su, domin Kulsum tana juyawa taga ya zubawa hanyar ido, cikin sauri ta ɗauke kanta, sai dai ta ji daɗin ganin Sanaa ba taje wajen ba.
Haka har suka ƙarasa wajen deɓar ruwan, babu wacce ta yi magana. Haka Kulsum ta ɗeba ruwa suka juya, a komawa haka suka wuce su Turaki da ya zuba musu ido.
Wata zuciya tana kwaɗaita mishi bin Sanaa yaga gidansu, wata tana hanasa, haka har suka ɓace mishi. A ranshi yake ji lallai yarinyar akwai abin da yake tattare da ita, sannan sam ba ta yi kama da ƴan matan ƙauyen ba, daga shigarta da yanayinta, tabbas daga wani gurin ƙaddararta ya faɗo da ita nan....
Kulsum ta ji farin cikin rashin ganin Turaki bai biyo Sanaa ba, a haka suka ƙarasa gida. Bayan ta juye ta sake fita ɗebo wani, Sanaa ganin ba wani hira suke ba ta ƙi binta ta zauna.
Haka Kulsum ta gama deɓar ruwan ta gama. Zama ta yi tana hutawa gefe ganin da sauran magriba. Maah tana ta aikin haɗa abincin dare, yayinda Sanaa na gefe tana aikin kallonta cewarta tana son koya.
Haka har aka ƙira magriba suka miƙe suka gabatar. Har daren tamkar na jiya ya zamo musu, babu magana tsananin su, duk da dama ba wani hira suke ba, amma Sanaa canzawar Kulsum ya dameta, sai dai jini da jiki yasa taja bakinta ta yi shuru.
Haka suka shiga ɗaki suka kwanta, kowacce ta juya ƴar uwarta bayan.***
Abuja, ƙarfe goman daren ranar.
Hammad zaune yake saman farin kujera, kansa ɗage idonsa yana kallon sama, taurarin sararin samaniya ya zubawa ido, tamkar malamin da yake karantar wani abu.
Komai ya dagule mishi, bai tsammani haka zai sha wahala ba, a tunaninsa tun da ya samu gidan Alhaji Hussain komai zai zamto mishi da sauƙi, sai dai ga shi cikin gidan yau tsawon sati uku, amma ya rasa ta ina zai fara. Babu yara ko mutane a gidan da zasu sa mishi ido, ko ganinsu ya hanashi yin komai, amma komai ya ƙi gaba.
Numfashi ya sauƙe a hankali ya furta.
"Allah ka shige min gaba, ka bani mafita, ka cika min burina."Idanuwansa ya lumshe ya buɗe yana sauƙe kansa ƙasa, gidan yabi da kallo. Saura mishi lokaci kaɗan da aka ɗauka mishi, kuma ya amince da shi domin cikar nashi burin bayan na iyayensa.
Haka Hammad ya gama darensa zaune yana saƙe-saƙe, karfe biyu ya shige ɗaki ya kwanta, tuni bacci ya ɗaukesa. Ƙiran sallar fari ya farka, fita ya yi ya ɗaura alwala ya dawo ɗakin ya fara nafila, ana fara gabatar da sallah ya miƙe ya fita masallaci.
Bayan an idar da sallah ya dawo, ɗakinsa ya shige ya kwanta rama baccinsa.Alhaji Hussain ƙarfe bakwai ya fito a ɗakinsa cikin shirin fita, meeting na gaggawa ne ya same shi wanda aka haɗa musu su da suke neman ƙuri'a, bai tashi Momma ba ya fice ko breakfast bai tsaya yi ba.
Motarsa da take fake ya nufa ya buɗe yana shiga, kunnawa ya yi tare da yin riverse ya kalli get. Cikin ƙarfi ya danna hon ganin mai gadinsan ba ya nan.A firgice Hammad ya farka yana miƙewa zaune, jin ƙarar hon ya miƙe tsaye da ƙyar yana fita waje. Ganin Alhaji Hussain ne da kan shi yasa cikin sauri ya nufi get ya tura ya buɗe.
Alhaji Hussain na ganin haka ya ja motarsa ya fice da sauri. Da mamaki Hammad yabi motarsa da kallo ganin uban gudu da yake yi.
أنت تقرأ
HAMMAD SANAA
عاطفيةCin amanar yarda, yayinda ƙaddararsu tasa su yin nesa da juna. Ko ya ya haɗuwarsu zai kasance? Wace irin ƙaddara ce ta rabasu da suka zaɓi yin nisa da juna? It's all about romance, destiny, hatred, limitless and intensely love. #FreeBook #Vote #Foll...