EPISODE 2

608 30 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
        *😢DAREN AURENA💔*

*Daga Alk'alamin 'yar mutanan zazzagawa✍🏾*
*Nanah M Sha'aban*
      
        _Labari mai tab'a zuciya_

Shafi na 2

"Assalamu alaikum" Mai shigowar ta fad'a tare da tura kofar d'akin ta shiga, Murmushi Aunty Murja ta sakar mata tare da amsa Mata sallamar "Wa'alaikissalam Amatullahi"
"Ina wuni Aunty Murja" Amatullahi ta tsugunna har k'asa cikin ladabi tana gaisar da Aunty Murjan
"Lafiya kalau ya kike"
"Lafiya alhamdulillah"

Sai kuma ta komar da dubanta kan Khadijatullah wacce tayi luf a jikin Aunty Murja.
"K'awata ba dai har yanzu kuka kike yi ba, haba Khadijatullah dubi yadda fuskarki ta koma idanuwanki duk sunyi ciki_ciki saboda kuka ya kamata kisan cewa wannan k'addara ce Allah ubangiji ya d'ora Mana, Kuma dukkan musulmi ya kamata ya rumgumi duk iriyar k'addarar da tazo Masa Mai kyau ce ko akasin haka".

Shuru kawai Khadijatullah tayi tana sauraronta tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta na cigaba da zubar da hawaye, tabbas tasan su Aunty Murja ba zasu tab'a fahimtar irin tashin hankali, bala'i da masifar da take ciki ba, taya za'ayi a daketa Kuma a hanata kuka, bayan sun san irin cutar da Jabir yayi mata tana jin labarai a gidan t.v, kuma tana jin labarai iri_iri wad'anda maza suka yiwa matayensu na cin mutunci, Amman ita Bata tab'a jin labarin irin abin da Jabir yayi Mata a DAREN AURENSU ba, ta yaya za'ayi ta manta da wannan daren, wanda take kiransa da bak'in dare domin ita DAREN AURENTA ya kasance Daren bak'in cikinta, Wanda har yanzu take cikin bak'in ciki.

Amatullahi ta saka hannunta a kan fuskar Khadijatullah tana goge Mata hawayenta,nan ita da Aunty Murja suka sakata a gaba suna yi Mata hira domin su samu ta hak'ura, ita dai kawai jinsu take Amman a wannan karon tayi kok'arin had'iye kukanta domin ta fahimci kukanta Yana jefa masoyannata guda biyu cikin tashin hankali, Aunty Murja ce ta tashi ta d'auko musu abincin da ta girka a wani d'an k'aramin kwanon silba, ta dawo gurin da take ta zauna tare da bud'e kwanon shimkafa da Mai da yaji ce, "Kash! na manta ban d'auko cokula ba" Amatullahi tayi murmushi "To Aunty Murja bari in d'auko miki" mik'ewa tayi ta nufi inda kwandon kwanukansu yake wanda babu wani kayan kirki a cikinsa, ta d'auko cokula guda biyu wad'anda kana ganinsu zaka san sunyi mugun dad'ewa domin har sun fara lank'washewa, zama tayi tare da mik'awa Aunty Murjan cokulan "Gashi Aunty Murja" cokali guda d'aya ta k'arb'a sannan ta ce "to matso sosai muci abincin" Da sauri Amatullahi ta girgiza kai domin abincin dake kwanon bama zai ishesu ita da Khadijatullah ba, saboda bashi da wani yawa "Kaii Aunty Murja Alhamdulillah wallahi sai da naci abinci sosai kafin in zo" sai kuma ta mik'awa Khadijatullah cokalin tana fad'ar "gashi nan kici abincin" girgiza kai ta shiga yi alamar bata cin abincin, cikin d'aurewar fuska Aunty Murja take magana "wato abin da kike son ki tsira kenan rashin cin abinci, ai shikenan tunda haka kika zab'ar wa kanki" sai kuma ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Khadijatullah ta karb'i cokalin hannun Amatullahi "Aunty Murja Dan Allah ki dena kuka zan ci" ta fad'a tare da saka cokalin a cikin abincin, shuru Aunty Murja tayi ita ma ta shiga cin abincin loma biyar Khadijatullah tayi ta ajiye cokalin, ta zame ta kwanta a kan yaloluwar katifar da take kan gadon ta rufe Ido domin Bata so Aunty Murja ta k'ara takura Mata taci abinci, Aunty Murja ma Bata ce Mata komai ba, Amatullahi kuwa mik'ewa tayi tare da cewa "to Aunty Murja zan tafi".
"Amatullahi yau tafiya da wuri haka" murmushi tayi ta ce "wallahi Aunty Murja zamu je Unguwa ne da Mama shine nace Bari inzo na ganku kafin mu tafi" Aunty Murja ta ce "Allah sarki Amatullahi to mun gode sosai" "Haba Aunty Murja bakomai ai" zagayawa tayi dai_dai saitin kan Khadijatullah ta shafa fuskar ta ta tana cewa "To k'awata sai na sake dawowa gobe idan yau min dawo da wuri zan k'ara dawowa na ganku" Kai kawai ta d'aga mata, Amatullahi ta k'ara yiwa Aunty Murja sai anjima sannan ta fita daga gidan da saurinta, Aunty Murja ta tashi ta shiga gyara d'akin daga nan ta dawo kan gadon ta kishim gid'a  tana sauraron radio da ta kunna a wata matatciyar radio duk rayi raga_raga.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Shirye yake cikin wasu k'ananun kaya, kyau iya kyau ya gama yi, turarurrukan dake kan madubin d'akinsa wanda kamar shagon kanti saboda yawansu, ya shiga fasawa a duk jikinsa saboda duk yawan turaren nan sai da ya bisu d'aya bayan d'aya yana fesasu a jikinsa, wani d'an k'aramin kum ya d'auka k'irar dubai shi kanshi kum d'in abin tsayawa ka kalla ne, ya shiga taje kannasa da kum d'in a hankali tamkar wanda a kace dole sai ya taje kannasa, sai da ya d'auki kusan awa d'aya yana shiryawa, sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin, ko kulle d'akin bai yi ba haka ya nufi b'angaren Mami Yana taku d'aya_d'aya kamar wanda yake tsoron tafiyar, a haka har ya isa part d'in Mami to sallama bai yi ba haka ya tura kai cikin falon nata a zaune ya tarar da ita tana kallon wani film a zee word, da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rumgumeta tare da yi Mata kiss a kumatunta, Murmushi Mami tayi tare da shafa kansa "Wow my son you look so Masha Allah" Murmushi yayi tare da cewa "Thanks you Mum I really love you so much" Mami ta ce "Me too My son I love you so much" Mik'ewa tsaye yayi tare da cewa "Mami zan tafi club sai na dawo a chan zan kwana naga magriba tayi ana ta nema na akwai Abu Mai muhimmanci da zanyi me" yayi maganar cikin Yana yin shagwab'a "To sai ka dawo, Allah ya kaika lafiya, Amman goben ka dawo da wuri saboda Aliyu zai dawo daga dubai Kuma da wuri sai sauka" cikin yanayin farin ciki Jabir ya ce "Kaii d'an uwana Aliyu Ashe dai zan k'ara ganinsa kaii kamar ma kar inje club d'in saboda naga d'an uwana nayi ten year fa ban saka shi a idona ba".
Murmushi Mami tayi "Ai sai gobe zai dawo kaga bai kamata kak'i zuwa club d'in ba saboda kace akwai abinda zakai Mai muhimmanci ai sai gobe zai dawo ai har ka dawo ma" cikin yanayin jin dad'i ya ce "please Mami karku je d'aukoshi har sai na dawo" wani k'ayatatcen murmushi tayi ta ce "karka damu zamu jiraka" wani irin tsalle yayi sannan ya nufi kofar fita daga falon Yana fad'ar "Yawwah Mami nagode sosai" da murmushi ta bishi sannan ta cigaba da kallonta hankalinta kwance, shi kuwa Jabir Yana fita kai tsaye wajen da aka tanada d'an ajiye motoci ya nufa, ya shiga sabuwar motar da Abbansu ya Aiko Masa da ita, Mai gadi ya bud'e Masa gate ya fita da gudu daga gidan bai zame ko ina ba sai club, ai kuwa Yana isa club d'in tun kafin ya fito daga mota aka saka Masa ihu, Yana fitowa daga cikin motar zee namo tazo da gudunta ta rumgumeshi tana yi Masa kiss ta ko ina a jikinsa, d'aukarta yayi cak dan Daman Shima a matse yake yazo club d'in ya huta da zee domin Yana jin dad'in yarinyar sosai hotel d'in club d'in ya nufa da ita, ana fa guri ya k'ara hau tsinewa da ihu, shi kuwa Jabir bai bii ta kansu ba domin burinsa kawai ya samu ya biya buk'atarsa da Zee d'in, d'akin da aka basa ya shiga, ya ajiye zee d'in a kan gado, ya cire mata kayan jikinta daman ba wani kayan k'irki bane a jikin nata rigar bacci ce wacce ko gwiwarta Bata Kai ba, Bata da hannu d'an haka ya zama duka rabin k'irjinta duk a waje suke, Anan ya shiga tsotsarta ta ko ina tamkar ya samu wata alewa, Zee abin nema ya samu dan haka ta sakar Masa dukkanin jikinta Yana tsotsarsa, Anan dai sukai ta shek'e ayarsu (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace Allah ya shiryeku Amin) sai wajen isha'i sannan ya sauka daga kan Zee d'in Amman ita Zee d'in sam Bata so haka ba, saboda bata gama dawowa dai_dai ba, toilet ya shiga da niyyar yin wanka, Zee ya mik'e ta shiga cikin toilet d'in, ta tarar da Jabir har ya fara yin wankan bayansa ta hau ta fara shafashi a hankali "Baby kasan fa baka gama dani ba, dan ni ban koshi ba".
Jabir dai shuru yayi domin ya rasa masifa irin ta Zee kullum idan yayi sex da ita duk irin dad'ewar da zai yi a kanta sai tayi Masa korafin Bata koshi ba, janyota yayi ta dawo gabansa Yana kallonta tana kallonsa tana wurga Masa wani shu'umin murmushi.

Jabir ya ce......................

Anan zan tsaye sai naji comments d'inku domin in har da gaske kuke littafin nan Yana muku dad'i Ina son naga comments da yawa ni Kuma zanyi muku typing Mai yawa kamar read more 3 ko 4 insha Allahu😘

Love youu all🌸

Gaisuwa ta musamman ga mommah Hajara B Sarki😘💔😇

Daga Alk'alamin 'yar mutanan zazzagawa💖🌸💃

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now