*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😰💔*
_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban💔*_Labari mai tab'a zuciya❣️_
*Alk'alami yafi takobi🚴🏽♀️*
Shafi na 24
"Hajiya Mama na shiga uku dan Allah ki taimaka min" Tayi maganar tana k'ara sautin kukanta, Hajiya Mama ta ce "meya faru takwarata","Hajiya ta raba ni da Yaya Salis, Hajiya ta ce sai ya sake ni ba za ta yarda ya kuma zama da ni a matsayin matarsa ba" Kuka take yi sosai har sai da kan ta ya fara sara Mata, Hajiya Mama cike da tashin hankali ta ce "wacece wannan da d'anyen hukunci","Maminsa ce"Nihal ta bata amsa tana cigaba da kuka.
Shuru Hajiya Mama tayi "tabbas abin da ka yi sai anyi wa naka, Jabir ya wulak'anta marainiya gashi ita ma k'anwarsa anyi mata" Tayi maganar cikin zuciyarta, Shi ma Alhaji Mansur Abin da yake fad'a a tasa zuciyar kenan, Hajiya Mama ta d'ago ta dai-dai lokacin Amatullahi ta kai fuskarta kan Nihal d'in a firgice take nuna Nihal tana cewa "ke ce daman" Da sauri Nihal ta juya tana kallon Amatullahi tabbas duk da tana cikin matsanancin tashin hankali Amman ba za ta, tab'a mantawa da wannan fuskar ba ita ma cike da mamaki ta ce "ke ce anan?".
Sai kuma ta tashi ta nufi gurin da su Amatullah da Khadijatullah suke zaune ita ma ta zauna tana fuskantarsu hawaye na zuba daga cikin idanuwanta "ke ce Amaryar Abbanmu ko Kuma ke ce Khadijatullah" Khadijatullah ta kalli Nihal gabanta na fad'uwa "Wacece wannan? A Ina ta san sunana" Tambayar da take yi a zuciyarta kenan ba ta san ta fito fili ba, sai jin Nihal tai tana nuna ta tana cewa "ke ce Khadijatullah?"Kai ta gyad'a Mata alamar "Eh".
Hannunta ta kama sosai ta k'ara fashewa da kuka "Ki yi hak'uri duk da cewa ni ban da laifi, amman nasan alhakinki ne yake ta bibiyata, na san Yaya Jabir bai kyauta miki....................." A zaburai Khadijatullahi ta mik'e dai-dai lokacin Aunty Murja ta fito ta ji duk abin da Nihal ta ce wato hakan na nufin mahaifin Jabir shi ne mijinta, kanta ne yayi matuk'ar sarawa ta shiga maimaita innalillahi wa'inna ilaihi raju'un a fili.
Alhaji Mansur da Hajiya Maama sun yi matuk'ar jirjiga da jin wannan al'amarin "wato daman Khadija ita ce wacce wannan tsohon d'an iskan ya lalata rayuwarta" Hajiya Mama ta fad'a tana cigaba da jinjina lamarin, Khadijatullahi kuwa fita tayi da gudu Aunty Murja ta bi bayanta domin tsayar da ita, Nihal ma bin bayan su tayi ita kuma Amatullahi zama tayi tana cigaba da jin farin ciki domin kuma ta dad'e tana neman hanyar da zata addabawa Jabir sai gashi yau ta samu cikin sauk'i "ai kuwa sai na tabbatar na gasa maka aya a hannunka Jabir" Amatullahi ta fad'a a cikin zuciyarta.
A zaure Aunty Murja ta rik'e Khadijatullahi ta rungume nan suka shiga kuka, Nihal ma zuwa tayi ta rungume su tana ita ma kukan take tana jin sonsu yana ratsa dukkannin zuciyarta, Shahida da Yaya Aliyu ne suka shigo gidan suka tarar da su sun rungume juna suna kuka, da sauri Shahida ta k'arasa kusa da su tana tambayar "meya faru? Ko mutuwa aka yi?" Nihal ce ta fad'a musu duk abin da yake faruwa, nan fa ita ma Shahida ta fashe da kuka har da kururuwa ta rumgumesu suna kukan tare.
Aliyu ne ya shiga rarrashinsu da kalamai masu dad'i har ya samu kayi shuru haka suka koma cikin gidan Shahida da Nihal suna rik'e da hannun Khadijatullahi, zama suka yi jungum-jungum kamar gidan makoki, Amatullahi ce ta shiga jan su da hira domin kuwa ita kad'ai ta san abin da take shiryawa a kan Jabir domin kuwa sai ta tabbatar ta wulak'antasa sai ta saka shi a cikin bala'i da masifa sai ta hanashi kwanciyar hankali.
(ni kuwa na ce Jabir ka shiga uku gurin Amatullahi iyayen fitina, ba'a tab'a ma yi take barantana an tab'o bestynta😂😂🥳)
Haka kowa ya sake suka fara tab'a hira sama-sama, suka shiga gyara gidan da yin girke-girke duk da cewa Alhaji Mansur ya saka ayi musu order abincin bikin amman Hajiya Mama ta ce su ma ba za su zauna ba dole su k'ayin wasu abincin, shi kuwa Aliyu idanuwansa suna kan Khadijatullahi duk inda tayi sai ya bi ta da kallo tausayin yarinyar yake matuk'ar ji sosai sai kuma a yau ya k'ara tabbatarwa da cewa Jabir tabbas baya cikin jinsin mutane, sai dai aljanu domin kuwa ko wasu aljanun ma ba zasu iya aikata abin da yayi wa baiwar Allah salihar mace irin Khadijatullahi ba.
